Rikicin Boko Haram ya tilasta mutum dubu 40 gudun hijira a Nijar
Hukumar Kula da ’Yan Gudun Hijira ta Majalisar dinkin Duniya (UNHCR) ta ce sama da mutum dubu 40 ne suka guje wa rikicin Boko Haram inda suka tsallaka zuwa Jamhuriyyar Nijar da ke makwabtaka daga kasar nan.Jami’in Hukumar UNHCR a Jamhuriyar Nijar wanda ya bayyana wa gidan rediyon BBC Landan haka, ya ce za su […]
Hukumar Kula da ’Yan Gudun Hijira ta Majalisar dinkin Duniya (UNHCR) ta ce sama da mutum dubu 40 ne suka guje wa rikicin Boko Haram inda suka tsallaka zuwa Jamhuriyyar Nijar da ke makwabtaka daga kasar nan.
Jami’in Hukumar UNHCR a Jamhuriyar Nijar wanda ya bayyana wa gidan rediyon BBC Landan haka, ya ce za su tallafa wa dubban ’yan gudun hijirar musamman wadanda ke zaune a yankin Diffa.
A yanzu haka jami’an hukumar da na gwamnatin Nijar suna ziyarar gani da ido a Jihar Diffa don tattance irin tallafin da za a ba ’yan gudun hijirar.
Mutanen da suka tsallaka sun hada da ’yan Najeriya da ’yan Nijar da kuma ’yan Chadi, kuma yanzu haka wadanda suke cikin mawuyacin hali sun yada zango ne a garuruwan Geskerou da Diffa da Toumour da Nguelkolo da kuma Chetimari.
Sakamakon yanayi marar dadi da ’yan gudun hijirar ke ciki, kungiyar Agaji ta Red Cross a Jamhuriyar Nijar, ta ce daga watan Mayun 2012 zuwa yanzu ta ba da tallafi ga dubban mutanen da suka guje wa rikicin.
Kakakin kungiyar Oumarou Daddy Rabiou ya shaida wa BBC cewa, “Yawancinsu mata ne da kananan yara, kuma akwai ’yan Nijar da Najeriya da kuma ’yan Chadi a cikin ’yan gudun hijirar.”
Rikicin Boko Haram a yankin Arewa maso Gabas da ya fi shafar jihohin Borno da Yobe ya janyo rasuwar daruruwan mutane tare da barnata dukiya ta miliyoyin Naira.
Shugaba Goodluck Jonathan ya kafa dokar ta-baci a jihohin Borno da Yobe da Adamawa a kokarin kawo karshen zubar da jinin da ake yi kimanin wata tara da suka gabata.
Sai dai rahotanni sun nuna cewa duk da irin matakan da gwamnati ta ce tana dauka don kawo zaman lafiya, har yanzu ’yan Boko Haram na kai hare-hare a yankunan jihohin uku.