Rikicin cikin-gida na neman kassara PDP
Ga dukkan alamu rikicin cikin-gida yana neman kassara Jam’iyyar PDP bayan da ta sha kaye a zaben Shugaban kasa da na gwamnoni da ’yan majalisa da suka gabata. Bayan faduwar jam’iyyar a zabe an rika samu zarge-zarge da korafe-korafen cewa wasu daga cikin ’ya’yan jam’iyyar sun taimaka wajen yi mata zangon kasa a zaben, inda […]
Ga dukkan alamu rikicin cikin-gida yana neman kassara Jam’iyyar PDP bayan da ta sha kaye a zaben Shugaban kasa da na gwamnoni da ’yan majalisa da suka gabata.
Bayan faduwar jam’iyyar a zabe an rika samu zarge-zarge da korafe-korafen cewa wasu daga cikin ’ya’yan jam’iyyar sun taimaka wajen yi mata zangon kasa a zaben, inda har lamarin ya kai ga zargin shugabannin jam’iyyar na kasa cewa su ma sun taimaka wajen faduwarta a zaben.
Masu zargin sun kuma ce shugabannin jam’iyyar sun yi rub da ciki kan kudin kamfe da ya kamata su raba wa jihohi.
Shugabannin jam’iyyar wadanda suka rika kokarin kauce wa furta kalaman da za su nuna akwai matsala a cikin jam’iyyar ala tilas suka fito suka kare kansu inda suka dora alhakin faduwar jam’iyyar a zabe kan yadda wasu mukarraban Shugaban kasa Jonathan suka rika zagi da bata dan takarar Jam’iyyar APC kuma zababben Shugaban kasa Janar Muhammadu Buhari da kuma yadda aka ki tsoma shugabannin PDP a cikin harkar yakin neman zabe.
Masu zargin shugabannin Jam’iyyar PDP da danne kudin kamfe sun rika yada wata takarda a kafafen sadarwar zamani cewa an shigar da wasu kudade a wani asusun bankin Zenith Banki mai lamba 6016 inda aka biya Shugaban Jam’iyyar na kasa Ahmadu Mu’azu Naira miliyan 100 ta hannun kamfani Julius Berger, sai mataimakinsa Uche Secondus, ya karbi Naira miliyan 40. Sai Sakataren Jam’iyyar Adewale Oladipo Naira miliyan 30, sauran wadanda suka samu Naira miliyan 30 kowannensu sun hada da Ma’aji, Buhari Bala da Sakataren Kudi Bolaji Akpan da Sakataren Labarai Olisa Metuh da Odita, Adeyanju Fatai da Sakataren Tsare-Tsare Abubakar Mustapha da Shugabar Mata, Kema Chikwe da Mashawarci kan Shari’a, bictor Yusuf Kwon, da Shugaban Matasa, Hassan Maibasira da kuma Mataimakin Sakatare, Onwe Solomon.
Don haka sai suka nemi a rusa shugabannin jam’iyyar saboda zarginsu da gazawar da ta jawo faduwar jam’iyyar.
Sai dai a martanin da Kakakin Jam’iyyar Olisa Metuh ya mayar kan faduwar jam’iyyar a zabe ya ce yadda wasu mukarraban Shugaban kasa suka rika yin kamfe din kiyayya ga Janar Buhari ya taimaka wajen faduwar jam’iyyar. Ya ce da masu gudanar da kamfe din sun tsaya kan tattauna batutuwa da jam’iyyar ba ta fadi a zaben ba.
Game da kudin kamfe kuwa Metuh ya ce sun samu Naira biliyan tara wajen sayar da takardun tsayawa takara kuma daga cikin sun ba kwamitin kamfe din Shugaba Jonathan Naira miliyan 500, sai ’yan takarar gwamnoni an ba kowace jiha Naira miliyan 100, baya ga masu takarar majalisun jihohi.
Mista Metuh ya ce ba a ba Babban Kwamitin wani kudi na kamfe ba, balle ya yi almubazzaranci da shi. Ya ce wakilan kwamitin sunkarbi Naira miliyan 30 wanda ya kunshi alawus dinsu na kayan gida da sauransu da ba a biya su a tsawon shekara biyu da suka gabata ba. Kuma ya ce da hannun Shugaban kasa Jonathan da sauran wakilan Kwamitin Dattawan Jam’iyyar wajen yanke shawarar ba kwamitin wannan kudi.
Shugaban Jam’iyyar ta kasa Ahmadu Mu’azu ma ya fito ya wanke kansa kan yadda yake shugabancin jam’iyyar duk da rashin nasarar da ta yi a zabe. Ahmadu Mu’azu ya ce ya yi bakin kokarinsa don kubutar da Shugaba Jonathan daga faduwa a zaben, inda ya ce masu zarginsa da gaza tabuka wa Jonathan komai da “marasa fadin gaskiya.”
Mu’azu ya fadi a shafinsa na Tweeter cewa tun 1999 yake cikin PDP “saboda akida da yarda da manufofinta. Na yi iyakar kokarina a lokacin kamfe din Shugaban kasa da jam’iyyata. Mun je kowace jiha don kamfe. Kuma duk da zagi da cin fuska da abokai da ’yan uwa suke mana mun goya wa jagoranmu Shugaba Jonathan baya iya garskiyarmu,” inji shi.
An rika samun rahotanni lokacin kamfe cewa Mu’azu na barazanar yin murabus idan ba a daina kamfe din bata Buhari ba. Kuma Mu’azu ya ce masu zarginsu da kasa ba wa Jonathan kuri’un da suka dace daga Arewa sun manta jama’a ne ke zabe. “Idan da ina da iko kowa a jihata ‘Bauchi’ zai zabi Shugaba Jonathan ne, amma jama’a ke zabe ba nib a,” inji shi.
Game da zargin sun ci amanar Jonathan a lokacin zabe, Mu’azu ya ce, “wasu ma sun ci mutunci da zaginmu cewa mun ci amanar Shugaba Jonathan. Ta yaya mutum zai ci amanar kansa?”
Ya ce za sun emo maslaha kan halin da jam’iyyar ta samu kanta a ciki, kuma za ta farfado daga shan kayen da ta yi don tunkarar gaba.
Gwamnan Jihar Ekiti Ayo Fayose da shugabannin jam’iyyar suki zargi da kamfe din batunci ga Buhari wanda hakan ya kara masa karbuwa na daga cikin masu zargin shugabannin jam’iyyar musamman shugabanta na kasa Ahmadu Mu’azu da hada baki da ’yan adawa wajen kada Shugaba Jonathan a zaben da ya gabata.
Ya fadi a wata sanarwa ta hannun kakakinsa cewa, “Ina magana ne musamman a kan shugaban jam’iyya ta kasa, ya sayar da jam’iyya ga ’yan adawa. Ina da kwkkwarar shaida kan wannan haramtacciyar kawance da abokan adawa kafin zabe, idan suka sakemagana zan fallasa su. Don haka ba na nadamar kiran shugabannin kwamitin gudanarwar su sauka, musamman shugabanta na kasa.”
Ganin yadda wannan hayaniya take daukar sabon salo ne ya sa Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Dabid Mark, a shekaranjiya Laraba ya yi gargadin bangarorin biyu kan su mayar da wukarsu kube don kubutar da jam’iyyar daga rugujewa gaba daya.
Kakakinsa Paul Mumeh ya fadi a wata sanarwa cewa Mark na magana ne lokacin da Mataimakinsa Sanata Ike Ekweremadu wanda ke jagorancin kwamitin auna abin da ya biyo bayan zabe ya ziyarce shi a Abuja.
Sanarwar ta ce Sanata Mark ya damu kan ci gaba da bata suna a tsakanin bangarorin jam’iyyar inda yake tsoron fadawa matsayin da “PDP ke kokarin makyarkyatar mutuwa.”
Ya ce matukar ba a hanzarta yin jinyar rauni tare da samo maganin da ya dace ba, jam’iyyar ta doshi hanyar bisnewa. “Jam’iyyar a yanzu a some take, wajibi ne mu yi duk abin da za mu iya wajen farfado da ita, maimakon tsayawa muna cece-kuce marasa amfani da dora wa juna laifi,” inji Sanata Mark.