Rikicin da ya faru a Kasuwar Magani
A ranar Litinin din makon jiya ne rikici ya barke a Kasuwar Magani da ke karamar Hukumar Kajuru a Jihar Kaduna. Rahotanni ce mutum 10 ne suka rasu a yayin rikicin yayin da aka kona shaguna kimanin dubu 1. Haka kuma an yi asarar ababen hawa da wasu gine-gine. Rahoto ya nuna rikicin ya auku […]
A ranar Litinin din makon jiya ne rikici ya barke a Kasuwar Magani da ke karamar Hukumar Kajuru a Jihar Kaduna. Rahotanni ce mutum 10 ne suka rasu a yayin rikicin yayin da aka kona shaguna kimanin dubu 1. Haka kuma an yi asarar ababen hawa da wasu gine-gine. Rahoto ya nuna rikicin ya auku ne a tsakanin kabilar Kadara da ta Hausawa. An ce a ranar Litinin da safe ce wata budurwa wacce take bin addinin Kirista ta yi yunkurin shiga addinin Musulunci kamar yadda saurayinta ya nemi ta yi hakan, al’amarin da bai yi wa matasa ’yan kabilar Kadara masu bin addinin Kirista dadi ba. Hakan ya janyo ce-ce-ku-ce a tsakanin matasan Kirista da na Musulmi inda kafin ka ce kwabo aka fara kone-kone.
Wata majiya ta ce mako daya kafin rikicin, hankali ya fara tashi a bisa wadansu rahotanni da aka rika bazawa a shafin sada zumunta kan wadansu al’amurran addini da suka shafi yankin da hakan ya sa matasan da ke bin addinan biyu suka rika mayar wa da juna martani da hakan ya tayar da hankulan mazauna garin.
Rahoton ya nuna, bayan an fara rikicin, sai matasa daga kowane bangare suka koma gida suka sake yin zuga daga nan ne suka shiga kona wa juna dukiyoyi da gidaje da hakan ta sa rikicin ya munana. Hakan ya sa aka kona manyan otel-otel biyu da ake ji da su a garin. Daga nan ne wani ayarin rundunar samar da tsaro ta sojoji daga Jihar Kaduna a karkashin jagorancin Kwamandan Runduna ta daya da ke Kaduna ya kai ziyara Kasuwar Magani don gane wa idonsa irin abin da ya faru.
Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasiru Ahmed El-Rufa’i ya yi Allah-wadai da rikicin, inda ya umarci Hukumar Bayar Da Agajin Gaggawa ta Jihar (SEMA) ta gaggauta samar da kayayyakin jinkai ga wadanda bala’in ya shafa. “Muna jajanta wa iyalan wadanda suka rasu a rikicin kuma muna yi wa wadanda suka samu raunuka addu’ar Allah Ya ba su lafiya,” inji El-Rufa’i.
Wannan rikici ya sa an tuno da irin rikice-rikicen da suka rika faruwa a jihar a shekarun baya. Da kyar da gumin goshi gwamnatin jihar ta samu shawo kan irin rikice-rikicen a baya, don haka muna fata a wannan karo ma gwamnatin ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen ganin irin wannan rikici bai sake aukuwa a nan gaba ba.
An taba yin rikici a Kasuwar Magani a 1980. Wanda ya faru a kwanan nan, ya faru ne saboda soyayyar da wadansu matasa biyu mace da namiji suka nuna wa juna. Mu sani waNi karin magana kan ce zo mu zauna, zo mu saba, don haka tilas al’ummomin da ke zaune da juna su rika kai zuciya nesa. Ba daidai ba ne da an samu wata husuma sai wadansu su mayar da abin tamkar na addini, kuma hakan bai dace ba. Da zarar an samu matsala to a yi kokarin yin sulhu don a zauna lafiya. Yadda ake amfani da addini da zarar an samu wani sabani musamman a wajen da Musulmi ko Kirista suka fi rinjaye, hakan sam bai dace ba. Najeriya dai kasa ce da ke dauke da addinai da kuma kabilu daban-daban, don haka akwai bukatar mu zauna lafiya.
Sarakuna da limaman addinai suna da rawar takawa wajen samar da zaman lafiya a yankunansu. Me ya sa rikici yake kazancewa ne alhali sarakuna da limaman addinai suna zaune a yankin?
Ya dace shuganannin al’umma su rika sanya ido a kan al’ummarsu, musamman matasa. Da suna yin haka, da an samu raguwar tashe-tashen hankula. Sannan hukumomi su rika yin taka tsan-tsan a kan kalaman da suke yi idan aka yi ko kafin a yi rikici. Matasa dai suna yin koyi ne da irin kalaman da shugabanninsu suke yi, don haka akwai bukatar yin taka tsan-tsan.
Gaskiya jami’an tsaro sun yi jinkiri a lokacin da suka kai dauki Kasuwar Magani. A ina jami’an tsaron suka makale a lokacin da matasa suke ta kone-kone? Duk da bai zai yiwu a ajiye jami’an tsaro a kowane lungu da sako ba, amma akwai bukatar a rika samar da su a kurkusa inda da zarar wani rikici ya tashi, za su kai dauki cikin gaggawa. Ya dace jami’an tsaro su rika sanar da lambobin da za a rika tuntubarsu don a rika sanar da su da zarar wani rikici ya tashi.
Mun yaba da matakin da Gwamnatin Jihar Kaduna ta dauka wajen samar da kayayyakin jinkai ga wadanda rikicin ya shafa sai dai akwai bukatar gwamnatin ta hada kai da jami’an tsaro wajen gudanar da kwakkwaran bincike don zakulo wadanda suka haddasa rikicin domin a hukunta su.