Rikicin dan majalisa da Direban Gwamnan Zamfara ya dauki sabon salo

A sakamakon rigimar da ta faru tsakanin Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar Dokokin Jihar Zamfara, Alhaji Salisu Musa da Direban Gwamna Alhaji Idris Garba ta sake daukar sabon salo inda aka ce dan majalisar ya kwace motar da ya ba wadda ake rigimar a kanta, wato Saratu Garba. Wanda hakan ya jawo tonon asiri a […]

Rikicin dan majalisa da Direban Gwamnan Zamfara ya dauki sabon salo
Rikicin dan majalisa da Direban Gwamnan Zamfara ya dauki sabon salo

A sakamakon rigimar da ta faru tsakanin Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar Dokokin Jihar Zamfara, Alhaji Salisu Musa da Direban Gwamna Alhaji Idris Garba ta sake daukar sabon salo inda aka ce dan majalisar ya kwace motar da ya ba wadda ake rigimar a kanta, wato Saratu Garba.

Wanda hakan ya jawo tonon asiri a tsakanin masoyan biyu, inda daga bisani aka shiga yada hirarrakin soyayya da suka rika yi a tsakaninsu ta waya, har wasu daga ciki suka fado kunnen ’yan jarida.
A cikin wadanan hirarraki dai akwai wadanda suka dauki mintoci masu yawa, kuma cikin abin da suka tattauna akwai maganar motar da ake cewa Salisu Musa ya saya mata bayan ya ce babu abin da ke tsakaninsu sai huldar kasuwanci.
A cikin hirar an jiyo ta tana gaya masa cewa, “Na san cewa ban sanya kudina na sayi mota ba, kai ka sa yi mota abin da nake so in fada maka shi ne ba zan zauna da kai in tashi a tutar babu ba. Na fi so mu tafi kotu da kai kamar yadda ka ce za ka kai ni, ba zai taba yiwuwa in ba da mota kuma in ba da kudi ba, kana ta gaya wa mutane cewa ka saya mini mota.”
Da yake ba ta amsa, ya ce “Ina so ki sani yaya zan je in gaya wa mutane cewa na saya miki mota, a wannan kasa irin tamu, wadda ’yan uwana sukan zo su tambaye ni in biya masu bukatunsu amma sai in ce masu su jira akwai wani abu a gabana.”
Ya ce “Haba-haba a kasa irin tamu yaya mutane za su kalle ni, idan na ce na saya miki mota. Na yi kokarin mu hadu mu zauna mu samu lokaci mu fahimci juna amma duk lokacin da na kira ki sai ki ce kina aiki ko za ki kira ni, shi ya sa nake shigo wa Gusau ni kadai in kai har La’asar amma kin ki yarda mu zauna.”
Da manema labarai suka kira shi ta waya don jin ta bakinsa ciki har da wakilinmu sai ya ce ai wannan hirar ba ta yanzu ba ce sun yi ta ne tun Talatin30 ga Janairu bana. Ma’ana tun ba su samu wannan sabanin ba.
Wakilinmu ya yi kokarin jin ta bakin Saratu Garba kan wannan al’amari amma abin ya ci tura domin duk wayoyinta a kashe suke, kuma ya ziyarci inda take saida abinci ba ta nan.
Sai dai wata mijiya a Majalisar Dokokin Jihar Zamfara ta bayyana cewa an kafa kwamitin da zai bi bahasin wannan al’amari, don gano inda matsalar take don daukar matakin da ya dace.