Rikicin ECOWAS na iya illata Nijeriya — Masana
Ficewar Nijar ya fi janyo damuwa musamman ga ’yan Nijeriya wadanda suke da al’adu da harshe da addini kusan daya.
Alamu na nuna cewa Nijeriya na iya tafka asara idan aka kwatanta da sauran kasashe 12 na Kungiyar Tattalin Arziki ta Kasashen Afirka ta Yamma (ECOWAS) ta fannin tsaro da tattalin arziki sakamakon ficewar kasashen Mali da Burkina Faso da Nijar daga kungiyar, kamar yadda wasu masana da wasu daga cikin al’ummomin da ke a kan iyakar kasar suka shaida wa Aminiya.
Sai dai wasu masana sun musanta cewa ficewar kasashen uku zai yi illa ga harkokin kasuwanci da tattalin arziki da zuba jari wanda hakan ka iya illata dokar kasuwanci ta Afirka (AfCFTA).
- Hukumar Alhazan Najeriya ta ƙayyade kuɗin Hajjin bana
- Yau take ranar zaɓen cike gurbi da raba gardama a jihohi 26 na Nijeriya
An samar da Dokar AfCFTA ce a matsayin wata hanya ta kasuwancin bai-daya a Afirka domin bunkasa ayyukan kasuwanci a nahiyar.
Idan ba a manta ba, sojojin da suka yi juyin mulki a kasashen uku, a ranar Lahadin makon jiya sun fitar da sanarwar ficewa daga Kungiyar ECOWAS.
Wannan ya biyo bayan takunkumin da kungiyar ta sa wa kasashen uku ne bayan hambarar da shugabannin dimokuradiya a kasashensu.
An dakatar da kasar Mali daga Kungiyar ECOWAS a shekarar 2021 bayan juyin mulki biyu da suka yi. Burkina Faso kuwa a shekarar 2022 ce aka dakatar da ita, sannan sai Nijar a shekarar 2023.
Duk da cewa dokar Kungiyar ECOWAS ta nuna dan kungiyar zai iya ficewa ce kawai bayan wa’adin shekara guda, amma wadanda suka tattauna da wakilanmu sun nuna al’amura ba sa daidaita masu ba tun a bara kuma suna ganin hukuncin da kasashen uku suka yanke zai kara ta’azzara lamarin ne maimakon saukaka musu.
Ba kamar abin da ya faro da Mali da Burkina Faso ba, dakatar da Nijar ya fi janyo damuwa musamman ga ’yan Nijeriya da kuma ’yan Nijar din wadanda suke da al’adu da harshe da addini kusan daya.
Al’ummomin kasashen Nijar da Nijeriya na auratayya da gudanar da kasuwanci tare, sannan kuma suna fuskantar kusan matsaloli irin daya a matakan kananan hukumomi da jihohi da kasa-da-kasa.
Iyakar Nijeriya da Nijar na da fadin kilomita 999, kuma ta shafi jihohin Sakkwato da Kebbi da Jigawa da Yobe da Borno.
Babu wata rata mai yawa da ya raba kasashen a jihohin bakwai wanda hakan ya sa kasashen ke cudanya da juna cikin sauki.
Baya ga wasu ’yan takardun da ake cikewa, al’ummomin kasashen biyu ba sa bukatar biza wajen tsallakawa kasashen domin gudanar da kasuwancinsu ko mu’amalarsu ta yau da kullum.
Amma da aka sanya wa Nijar takunkumi a shekarar 2023 tare da sanya musu ido sun ji a jikinsu domin kowa hakan ya sa an rufe dukkan iyakokin kasashen biyu.
Matakain dai ya janyo karancin kayan abinci da bukatun yau da kullum a yankunan kan iyakan. Kasar ta Nijar ta dogara ce matuka daga kayan abinci da na gine-gine daga Nijeriya.
Ita kuwa Nijeriya tana dogara ce daga dabbobin da ake shigowa da su daga Nijar da suka hada da rakuma da tumaki da awaki da kuma dabino da sauransu.
Juyin mulkin soja da aka yi a Nijar da kuma matakan da Kungiyar ECOWAS ta dauka wanda Nijeriya ke shugabanta ya shafi hadin gwiwa wajen yaki da ta’adanci da kasashen biyu ke yi a kan iyakokinsu a Arewaci da Kudancin kasashen kamar yadda jami’an tsaron da ke aiki a kan iyakar Tafkin Chadi suka tabbatar.
A watan Nuwamba 2023 Aminiya ta ruwaito irin gibin da aka samu sakamakon wannan takaddama a tsakanin kasashen biyu wanda hakan ya janyo karuwar hare-haren a Tafkin Chadi.
Wasu wurare a kan iyakokin kasashen biyu musamman ta yankin Gaidam a Yobe da Malam Fatori da Damasak a Jihar Borno suna fuskantar karuwar hare-haren ’yan ta’adda.
A cewar majiyoyinmu a Gaidam, kasar Nijar ta janye sojojinta daga iyakar kasar ta Gaidam wanda ya janyo karuwar hare-haren.
’Yan gudun hijirarmu na cikin kaka-ni-ka-yi — Gwamnatin Borno
Shugaban Kungiyar Dattawan Jihar Borno Dokta Bulama Mali Gubio ya ce idan aka yi la’akari da kawancen da ke tsakanin kasashen biyu, janyewar Nijar daga ECOWAS zai yi illa ga harkokin kasuwanci a Nijeriya da kuma ’yan gudun hijirar Nijeriya da ke Nijar.
“Muna magana ce a kan kasuwancin da ke gudanar a kan iyakokin kasashen biyu ba ’yan fasa kwauri ba.
“Yanzu mutanenmu dole sai sun nemi biza kafin tsallakawa cikin Nijar. Yanzu babu maganar shiga yadda aka ga dama da kayayyakin abinci,” in ji shi.
Ya yi kira ga ’yan Nijeriya da ke a kan iyakokin Nijar da su goyi bayan matakin da Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu zai dauka da kuma kungiyar ta ECOWAS wajen yin amfani da tattaunawa domin magance matsalar.
“Ko babu komai ’yan Arewa su yi abin da za su iya yi domin tabbatar da an kare kasancewarsu da aka kulla shekaru masu yawan gaske.
“Sarakunanmu da malamanmu da da tsofaffin shugabannin kasashen da kuma ’yan kasuwarmu duk sun yi kokarinsu wajen tabbatar da an samu zaman lafiya, amma sojojin sun ki ta hanyar ci gaba da rike mulki duk kuwa da talakawan ba sa so,” in ji shi.
Haka kuma wata majiyarmu a cikin jami’an tsaro a kan iyakar Abadam wanda gari ne da ke kan iyakar kasashen biyu inda dubban ’yan Nijeriya ke gudun hijira a Diffa, Nijar ta ce an fara samun masu komawa gida da yawa.
“’Yan gudun hijira ’yan Nijeriya da ke dawowa daga Diffa da wasu yankuna na Nijar akwai damuwa.
“Yawancin lokuta muna tura su ne zuwa sansanin ’yan gudun hijira da ke Monguno.
“Yanzu haka sansanin a cike yake makil wasu ba su da wurin kwanciya sannan babu isasshen abinci ga wadanda ke sansanin,” in ji majiyar.
Abdullahi Ibrahim wanda lauya ne kuma mai kare haƙƙin mutane a Maiduguri ya ce a yayin da Nijar ta dogara da Nijeriya a fannin tattalin arziki ita ma Nijeriya ta dogara da Nijar ta fannin yaki da ’yan ta’adda musamman Boko Haram.
“Mutane a Malam Fatori suna shiga Maine Soroa a Nijar domin neman magani. Suna kuma sayen kayan bukatun yau da kullum kamar ruwan sha da kayan abinci saboda ya fi sauki da su zo Maiduguri ko Mongono,” in ji shi.
Wani jami’in tsaro da ke aiki a Arewa maso Gabas wanda ba ya so a ambaci sunansa ya ce, “Muna bukatar goyon bayan Nijar domin kawar da ’yan ta’adda musamman a Abdam da Kukawa da Marte da Tunbus a yankin Tafkin Chadi,” in ji shi.
Ya ce, “ISWAP ana ganinsu a yankin Gashegar da Arkubma da Shilay inda suke tsayawa domin kai hare-harensu da kuma karbar haraji a wajen al’ummomin yankin.
“Ko a kwanakin nan ISWAP sun fito da motoci biyu da babura shida inda suka kwana a kauyen Late da safe suka dan yi zagaye a cikin garin a kusa da Kareto da Laye.
“Yawancin ’yan kungiyar ISWAP sun fito ne daga yankin Gaidam. Wannan yankin na karkashin Karamar Hukumar Mobbar ce,” in ji shi.
Matakin zai kara jefa mu cikin wahala — Mazauna Yankunan Katsina
Da suke bayani a kan lamarin da ke faruwa a kan iyakokin kasashen biyu, Shugaban Kungiyar Al’ummar Jibiya, Alhaji Hide Dahiru ya ce al’amuran kasuwanci suna cikin wani yanayi a yankin, inda ya ce ficewar kasahen uku za ta kara ta’azara lamarin a yankin.
“Akwai dokokin kan iyakokin kasashen da cike da shigi da fice domin gudanar da kasuwanci.
“Yanzu da wadannan kasashen suka fice daga ECOWAS hakan ya nuna ke nan wadannan dokoki ba za su yi amfani ba sababbi za a fito da su.
“Kamar yadda ka sani akwai kayayyaki irin su hatsi da dabino da ake samu daga Nijar da ba a biya musu haraji.
“Idan wannan mataki ya jima ya zama ke nan wadannan kayayyaki za a sanya su cikin wadanda ake safararsu ke nan,” in ji shi.
Wani masanin tsaro Muhammad Nasir Abdullahi ya ce akwai hadin gwiwa a tsakanin Nijar da Nijeriya wajen yaki da ta’adanci a kan iyakokin kasashen biyu, inda ya ce idan aka tsinke shi lamarin zai lalace.
Dangane da zamantakewa kuwa ya ce akwai mu’amala sosai a tsakanin mazauna iyakar kasashen biyu daga auratayya wanda kuma tsaurara matakan zai iya shafar wannan mu’amala ta iyalai.
Hadin kan kasashen na cikin barazana — Farfesa
A cewar Farfesa Tanko Baba masanin siyasa a Jam’iar Usman Dan Fodiyo da ke Sakkwato, matakin zai fi illa wa Nijeriya.
“Nijeriya ce a kan gaba wajen batun ECOWAS. Nijeriya ce ta fi yawan jama’a a cikin kasashen 15.
Kasuwancin Arewacin Nijeriya har cikin Nijar da Mali da Burkina Faso, ke nan kasuwancin da ke tsakanin wadannan kasashe uku zai lalace.
“Ina son ka sani cewa tattalin arzikin Nijeriya a fannin kasuwancin dabbobi kusan kaso 69 zuwa 79 na dabbobin da ke shigowa Nijeriya daga Nijar ne.
“Wasu ma ba daga Nijar kadai suke ba wasu daga Senegal ne a kullum. A yanzu ke nan za a samu nakasu a fannin.
“Bayan matsalar tsaro da muke fama da ita a yankin Arewa. A tarihi Nijeriya ba ta da makwabciya da ke biyayya gare ta kamar Nijar.
“Yanzu ke nan Nijeriya na iya fuskantar barazanar matsalar tsaro a yankin.
“Yanzu Nijar ta fice kuma ’yan ta’addar nan da barayin shanu duk suna da asali da irin wadannan kasashe irin su Mali da Burkina Faso da Nijar,” in ji shi.
Dokta Bashir wanda shi ma masanin tattalin arziki ne a Jami’ar Usman Dan Fodiyo ya ce kasuwanci a tsakanin Nijar da Mali na da girma.
“Idan ka je kan iyakar kasashen nan ka ga irin kasuwancin da ke faruwa a can za ka fahimci cewa mutane da yawa sun dogara da wadannan kasashe wajen kasuwancinsu, ficewar kasashe uku ba karamar matsala ba ce,” in ji shi.
Ya ce kuɗaɗen da ke shigowa a dalilin kasuwanci a tsakanin Nijar da Nijeriya ya kai Dalar Amurka biliyan daya a bara.