Rikicin Filato: Ƙungiyar Izala ta raba kayan agaji a Mangu
A makonnin da suka gabata ne wani mummunan rikicin kabilanci ya barke a Karamar Hukumar Mangu
Kungiyar Jama’atu Nasril Islam JNI ta yi rabon kayan agaji ga wadanda rikici ya rutsa da su a Karamar Hukumar Mangu ta Jihar Filato.
Ana iya tuna cewa, a makonnin da suka gabata ne dai wani mummunan rikicin kabilanci ya barke a karamar hukumar, inda mutane da dama suka ras rayukansu doriya a kan gidaje da aka kone da kuma ras matsugunni da daruruwan jama’a suka yi.
- Yadda fitattun sinimomin Kano suka zama kufai
- HOTUNA: Yadda ake karbar gaisuwar rasuwar tsohon gwamnan yobe, Bukar Abba
Sakamakon haka ne Kungiyar JNI reshen Jihar Filato ta yi rabon kayan agajin domin rage radadin wadanda ibtila’in ya rutsa da su.
Wakilinmu ya ruwaito cewa, Darektan ’yan agaji na JNI reshen jihar, Alhaji Danjuma Khalid ne ya jagoranci rabon kayan agajin a Babban Masallacin Mangu.
Alhaji Khalid ya bayyana damuwa dangane da halin da ya tsinci sansanin ’yan gudun hijirar, yana mai kira ga mahukunta da sauran masu ruwa da tsaki da kawo dauki.
Da suke karbar kayan agajin a madadin kwamitin da JNI ta wakilta domin karbar tallafi, Jafar Musa Daskegar da Aisha Muhammad, sun godiya da cewa wannan yunkuri zai agaza matuka wajen rage radadin wadanda rikicin ya shafa.
Aminiya ta ruwaito cewa, daga cikin kayayyakin tallafin da Kungiyar ta JNI ta bayar akwai buhun shinkafa 140 mai nauyin kilo biyar, buhun gishiri shida, kwalin taliya 20, tufafi, gidajen sauro, audugar mata da yara da sauransu.