Rikicin Filato: Mutum 1,891 sun mutu a kananan hukumomi 5

Kwamitin mutum biyar da Gwamnan jihar Filato Simon Bako Lalong ya kaddamar zai yi aikin akan mayar da ‘yan gudun hijira dubu 50, 212 da suka bar gidajensu a unguwanni 118 da masaukan Fulani 98 a kananan hukumomi biyar na jihar. A cewar rahoton shugaban kwamitin Iya bayis Mashall Bala Danbaba (mai ritaya) ya ce, […]

Rikicin Filato: Mutum 1,891 sun mutu a kananan hukumomi 5

Kwamitin mutum biyar da Gwamnan jihar Filato Simon Bako Lalong ya kaddamar zai yi aikin akan mayar da ‘yan gudun hijira dubu 50, 212 da suka bar gidajensu a unguwanni 118 da masaukan Fulani 98 a kananan hukumomi biyar na jihar.

A cewar rahoton shugaban kwamitin Iya bayis Mashall Bala Danbaba (mai ritaya) ya ce, su nada adadin mutum 59,008 da rikicin jihar ya shafa a kananan hukumomi biyar yayin da mutum dubu 1,891 suka rasa rayukansu.

Kananan hukumomin biyar sun hada da: Jos ta Arewa, Riyom, Barkin Ladi, Bassa da kuma Bokkos.