Rikicin Gabas ta Tsakiya: Farashin mai ya tashi a kasuwar duniya

Farashin ɗanyen mai a kasuwar duniya ya tashi sakamakon fargabar ɓarkewar mummunan yaƙi a yankin Gabas ta Tsakiya

Rikicin Gabas ta Tsakiya: Farashin mai ya tashi a kasuwar duniya

Danyen Mai

Farashin ɗanyen mai a kasuwar duniya ya tashi sakamakon fargabar ɓarkewar mummunan yaƙi a yankin Gabas ta Tsakiya.

A halin da ake ciki farashin ɗanyen mai nau’in Brent ya ƙaru zuwa Dala 77, kimanin Naira 130,000.

Farashin ɗanyen mai ya tashi ne bayan Shugaba Joe Biden na ƙasar Amurka ya ce suna tattaunawa kan yiwuwar taimaka wa Isra’ila domin kai wa ƙasar Iran hari.

Sakamakon haka ake fargabar ɓarkewar mummunan yaƙi a Gabas ta Tsakiya a sakamakon cacar baka da kuma harin da ƙasar Iran ta kai wa Isra’ila, wadda ita ma take kai hare-hare a zirin Gaza da kuma kan kungiyar Hisbullah a ƙasar Lebanon.

Amma masu hasashe din bayyana cewa farashin zai sauka saboda Amurka banda isasshen mai  sannan Libya ta shawo kan matsalar da ta haka fitar da mai daga ƙasar na tsawon wata guda.

A watan a Dismaba kuma ake sa ran Ƙungiyar kasashe masu arzikin mai, OPEC+, wadd a Saudiyya ke jagoranta kuma za ta ƙara yawan ɗanyen man da take haƙowa.

Iran ta yi wa Isra’ila ruwan makamai masu linzami harin tare da nuna mata yatsa ne bayan Isra’ilar ta kashe Hassan Nasrallah, shugaban Hisbullah ta ƙasar Lebanon da wasu manyan jagororin ƙungiyar wadda Iran ke goyon baya.

Hain da ta bayyana a matsayin ɗaukar fansa kan kashe-kashen da Isra’ila ke wa jagororin ƙungiyoyin gwagwarmayar Larabawa da ke da goyon bayan Iran a Zirin Gaza da Lebanon da Yaman ya haifar da zullumi ga masu zuba jari.

Iran ta ce ba ta son yaƙi, amma duk da haka idan Isra’ila ta ce mata kula, za ta ce cas!

Ta bayyana cewa za ta tsananta yawan hare-harenta kan Isra’ila, muddin Gwamnatin Benjamin Netanyahu ta mayar mata da martani.

Barazanar Iran ɗin na zuwa ne duk da kiraye-kirayen da ke yi na sassauta bude wuta a rikicin, wanda ya ci rayuka sam da 1,000 a Lebanon.

A ranar Alhamis Isra’ila ta sanar cewa ta kai hari hedikwatar leƙen asirin Hisbullah a birnin Beirut, fadar ƙasar Lebanon, a yayin da sojoji da jiragenta suke ba-ta-kashi da mayaƙan ƙungiyar.

Mutum 10 sun mutu a wajen rabon tallafin abinci a Abuja

Tirela murƙushe ’yan sanda 3 har lahira

An ƙwace kwantainoni 54 mallakin Emefiele

Fulawa da dabbobin Fadar Shugaban Ƙasa za su ci N125m a 2025