Rikicin Gado: Sarkin Zazzau ya gargadi hakimai kan cin zalin talakawa
Majalisar Masarautar Zazzau ta sake tabbatar da aniyarta na amfani da tsarin sasanci da sulhu wajen magance rikice-rikicen al’umma da kare talakawa daga cin zarafin masu iko, in ji sanarwar.
Sarkin Zazzau na 19, Alhaji Ahmed Nuhu Bamalli
Majalisar Masarautar Zazzau ta warware rikicin rabon gado da ya shafi al’ummar Matarawa da ke Gundumar Kudan tare da gargadin shugabannin gargajiya a faɗin masarautar kan duk wani nau’i na cin zarafi da zalunci ga marasa ƙarfi.
Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in yaɗa labarai da hulɗa da jama’a na Masarautar Zazzau, Abdullahi Aliyu Kwarbai, ya fitar bayan kammala zaman majalisar ƙarƙashin jagorancin Mai Martaba Sarkin Zazzau, Malam Ahmed Nuhu Bamalli.
A cewar Abdullahi Aliyu Kwarbai, ƙorafin ya kai karo na uku a gaban majalisar ƙarƙashin tsarin sasanci da sulhu na masarautar, inda aka yi zargin cewa wasu magada na gaskiya ba a ba su haƙƙinsu ba, yayin da wasu da ba su cancanci cin gadon ba suka amfana daga rabon dukiyar marigayin.
Ya bayyana cewa bayan cikakken bincike da nazari, majalisar ta bayar da umarnin dakatar da dagacin ƙauyen da lamarin ya shafa tare da umartar a kwato dukkan kuɗaɗen da aka raba ba bisa ƙa’ida ba ga waɗanda ba su cancanci gadon ba.
- Tinubu zai naɗa ɗan shekara 40 a matsayin Shugaban JAMB
- An kashe matashi, an jikkata wasu 12 bayan zaɓen fid-da-gwanin APC a Sabon Gari
Abdullahi Aliyu Kwarbai ya ƙara da cewa an mika kuɗaɗen da aka kwato ga Mai Martaba Sarkin Zazzau, wanda daga bisani ya damƙa su ga Hakiman Kudan da Hunkuyi tare da umartar su da su koma Matarawa domin sa ido kan sake rabon gadon cikin adalci da daidaito bisa tsarin shari’ar Musulunci kamar yadda Alƙur’ani Mai Girma ya tanada.
Sanarwar ta kuma bayyana cewa Sarkin Zazzau ya yi amfani da wannan dama wajen gargaɗin hakimai da dagatai a faɗin masarautar da su sanya ido sosai kan yadda dagatai da magatakardunsu ke mu’amala da jama’a.
“Masarautar Zazzau ba za ta ƙara lamuntar duk wani nau’i na yaudara ko cin zarafin marasa ƙarfi ba,” in ji Sarkin Zazzau kamar yadda Abdullahi Aliyu Kwarbai ya bayyana a cikin sanarwar.
Ya kuma jaddada muhimmancin adalci, gaskiya da riƙon amana a tsakanin shugabannin gargajiya a matakin ƙasa.
Majalisar Masarautar Zazzau ta sake tabbatar da aniyarta na amfani da tsarin sasanci da sulhu wajen magance rikice-rikicen al’umma da kare talakawa daga cin zarafin masu iko, in ji sanarwar.