Rikicin Gaza: Muhimman abubuwan da ya kamata ku sani
Muhimman abubuwa masu alaka da harin da kungiyar Hamas da ta kashe daruruwan yahudawa a Isra’ila
A ranar Asabar mayakan kungiyar Falasdinawa ta Hamas suka kaddamar da wani kazamin hari da ya girgiza Isra’ila a yankin Zirin Gaza.
Mayakan da suka kai harin da kusan ba a taba ganin irinsa a yankin ba, sun shafe tsawon awanni, inda suka kashe mutane akalla 600 tare da yin garkuwa da wasu a Kudancin Isra’ila.
- Hezbollah ta shiga yaki da Isra’ila don goyon bayan Falasdinawa
- Takardun Tinubu: Babu ruwan Kwankwaso da karar da Atiku ya shigar —NNPP
Bayan harin wanda Hamas ta harba rokoki sama da 2,000 ne Isra’ila ta mayar da martani ta sama a yankin Gaza, inda ta rusa gine-gine da dama, ciki har da wani bene mai gidaje sama da 100 a cikinsa.
Ga wasu muhimman abubuwa da ya kamata ku sani kan harin da kuma yankin kamar haka:
Wace ce kungiyar Hamas?
Hamas kungiyar mayakan sa-kan Islama ce da ke gudanar da Zirin Gaza da ke kasar Falasdinu, inda kungiyar ta sha alwasin rusa Isra’ila.
Hamas ita mafi girman kungiyoyin Falasdinawa da ke yaki da mamayar da Isra’ila ta yi wa Falasdinawa kuma tun shekarar 2007 da ta karbi iko da yankin take yakar Isra’ila.
Kungiyar ta kai wa Isra’ila hare-hare ko ta ba wasu kungiyoyi damar yin hakan da dubban rokoki a lokuta daban-daban.
Isra’la ta sha kai wa Hamas hari ta sama da kasa, kuma tun a 2007 ita da Masar suka datse Zirin Gaza saboda abin da ta kira kare kanta.
Manyan kasashe irinsu Amurka da Birtaniya Tarayyar Turai da ma Isra’ila sun ayyana Hamas ko reshenta na soji a matsayin kungiyar ta’addinci.
Ina Zirin Gaza yake?
Zirin Gaza wani yanki ne da ke tsakanin kasashen Masar da Isra’ila, ya kuma yi iyaka da Tekun Mediterranean. Tsawon yankin kilomita 41 ne, fadinsa kuma kilomita 10.
Yawan al’ummar Zirin Gaza miliyan 2.3 ne, don haka shi ne karamin yanki mafi yawan al’umma a duniya.
Takwas cikin kowane mutum 10 a yankin sun dogara ne da tallafin kungiyoyin jin kai da Majalisar Dinkin Duniya, kuma kimanin mutum miliyan daya ne a yankin suka dogara da kuniyoyin jin kan domin samun abinci a kullum.
Isra’ila ce ke iko da sararin samaniyan Zirin Gaza da iyakokinta inda take kayyade kayayyaki da mutanen da ke shige da fice. A daya bangaren kuma, Masar ke kula da shige da fice mtane a tsakaninta da yankin na Gaza.
Me ya hada Isra’ila da Hamas fada?
Du da cewa an jima ana wa juna kallon hadarin kaji tsakanin Isra’ila da Hamas, amma harin kungiyar na ranar Asabar ya zo bagattan.
A yayin harin, kungiyar ta harba daruruwan rokoki, mayakanta suka tsallaka zuwa yankunan Yahudawan masu share-wuri-zauna suka kashe wasu, suka kuma yi garkuwa da wasu da har yanzu ba a kai ga tantance adadinsu ba.
Ba a jima ba Isra’ila da kaddamar da hari ta sama da cewa hadafinta shi ne cibiyoyin mayakan Hamas da ke Gaza.
Shin Hamas ta taba kai irin harin?
Editan kasashen waje na BBC, Jeremy Bowens ya ce harin shi ne mafi girma da Hamas ta taba kai wa Isra’ila daga Zirin Gaza.
Ya kara da cewa shi ne hari mafi muni da Hamas ta kai wa Isra’ila a tsawon lokaci, inda mayakan kungiyar suka tsallako zuwa cikin yankin da Isra’ila ke iko da shi ta bangarori daban-daban.
Hamas ta kai harin ne washegarin da aka cika shekara 50 da babban harin ba-zatan kasashen Larabawa da kasashen Masar da Syria suka kai wa Isra’ila a shekarar 1973.
Watakila muhimmancin ranar ta sa jagororin Hamas suka kaddamar da harin domin sake dawo da tarihi.
Matakan tsaron Isra’ila sun gaza ne?
Harin Hamas na ranar Asabar ya nuna gazawar tsaron Isra’ila, kasa mafi matakai da kayan tsaro a Gabas ta Tsakiya.
Duk da hadin gwiwar hukumomin tsaro na Shin Bet da hukumar leken asiri na cikin gida da kuma Mossad, da ke mata leken asiri ta waje, da rundunonin soji da kayan aikinsu, amma duk da haka, sun kasa gano barazanar harin na Hamas, ko sun kasa dakilewa.
Hasali ma gwamnatin Isra’ila na da masu yi mata leken asiri a cikin kungiyoyin mayakan Falasdinawa da na Lebanon da Syria da ma wasu wuraren.
Sannan a shingen iyakarta Zirin Gaza, an sanya wayoyi masu kaya a sama, ga kyamarorin tsaro da na’urorin jin motsi, baya ga sojoji da ke sintiri a koyaushe.
Amma duk da haka, mayakan Hamas suka kutsa cikin yankin Isra’ila ta cikin katangar da kuma ta teku, sai bayan sun kaddamar da hari sun kashe na kashewa sun sace na sacewa, kafin hukumomin tsaron suka farga.
Gwamnatin Isra’ila ta ce gomman sojoji, fararen hula, kananan yara, tsofaffi da nakasassu na daga cikin wadanda Hamas ta yi garkuwa da su, amma kungiyar ta ce adadin ya ninninka hakan.
Isra’ila ta ce tana faragabar wasu daga cikin mutanen an riga an kashe su, inda shugaban kasar ya ce za su sa kafar wando da duk wanda ya cutar da mutanen.
Ina ne Falasdin, mene ne alakarsa da rikicin?
Gabar Yammacin Kogin Jordan da kuma Zirin Gaza wadanda yankunan Falasdinawa ne, da kuma Gabashin Birnin Kudus da Isra’ila, su ne yankin Falasdinu tun a zamanin Dular Rumawa.
A shekarar 1948 ne aka sanar da Isra’ila a matsayin kasa, amma har yanzu wadanda ba su amince da ita a matsayin halstacciyar kasa ba, na kiran yankin da sunan Falasdinu.
Hakazalika Falasdinawa na amfani da kalamar Falasdin a matsayin sunan yankin da ya hada Gabar Yammacin Kogin Jordan, Gaza da kuma Gabashin birnin Kudus.
Me ke iya faruwa nan gaba?
Kwamandan sojin Hamas, Mohammed Deif dai ya yi kira ga Falasdinawa da sauran Larabawa da su taimaka wa Hamas a yakinta na “fatattakar mamayar da Isra’ila ta yi”.
Abin jira a gani shi ne, yadda Falasdinawa da Larabawan da ke yankin Yammacin Kogin Jordan da Gabashin Birnin Kudus za su amsa kiran na Hamas.
Isra’ila dai na fuskantar barazanar yaki ta bangarori daban-daban, kuma tuni kungiyar mayakan Hezbollah ta kasar Lebanon ta amsa kiran na Hamas.
A halin da ake ciki Isra’ilar ta ba da umarnin girke karin sojoji da kuma tsananta sintiri a Gaza, a yayin da ta ce tana shirin kaddamar da aikin soji ta kasa a yankin.