Rikicin Gaza: Ya kamata Isra’ila ta bari a kai kayan agaji —WHO
WHO ta bukaci a ba da damar shigar da kayan a gaji ga yankin Gaza
Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta bukaci Isra’ila ta da damar shigar da abinci da kayan agaji Zirin Gaza inda jiragen Isra’ila suka shafe kwana uku suna luguden wuta.
Hakan na zuwa ne a yayin da adadin mutanen da aka kashe a sabon rikicin Isra’ila da kungiyar Falasdinawa ta Hamas ya haura 1,500.
A safiyar Talata jiragen Isra’ila suka kashe Falasdinawa ’yan jarida uku a sakamakon makamamin da ta harba kan wani gini a Gaza, yankin da Isra’ila ta lalata gidajen mutane 187,500 baya ga kashe mutane akalla 700 tare da jikkata wasu dubbai.
- Isra’ila sun rushe gidade 187,500 a Gaza cikin kwana 2 —MDD
- Ranar Juma’a za a daura auren zawarawan Kano
- Rikicin Gaza: Muhimman abubuwan da ya kamata ku sani
Ma’aikatar Lafiyar Gaza ta ce Falasdinawa 704 ne suka rasu a Gaza da Yammacin Kogin Jordan, wasu 3,726 suka jikkata.
A daya bangaren kuma, Hamas ta kashe Isra’ilawa 800 ta jikkata wasu dubbai, ta yi garkuwa da wasu 150; sannan Isra’ila ta kashe mayaka hudu na kungiyar Hezbollah a kasar Lebanon.
A ranar Litinin Isra’ila ta hana shigar da abinci da kuma zirga-zirga a Gaza, gami da yanke wa yankin wutar lantarki da ruwan sha.
Amma WHO ta hannun Tarik Jasarevic ta bukace ta da ta ba da damar shigar da kayan abinci da magunguna da sauran kayan agaji ga daruruwan mutane da ke bukatar agaji da kayan jinkai.
Majalisar Dinkin Duniya ta sanar cewa haramun ne kawanyar da Isra’ila ta yi wa yankin Gaza.
Manzon MDD kan kare hakkin bil Adama, Volker Turk, ya ce dokar duniya ta haramta, “tare mutane a yanayin da rayuwar farar hula ke cikin hadari, ta hanyar hana su samun abinci da suran bukatun rayuwa.”
Volker Turk ya ce wajibi ne a mutunta dan Adam da rayuwarsa, inda ya yi kira ga bangarorin da ke yaki da juna su kai zuciya nesa.
Ya ce, datse Gaza da Isra’ila ta yi ya kara jefa Falasdinawan cikin halin ha’ula’i musamman wajen samun agaji da motocin daukar marasa lafiya, a daidai lokacin da ake samun karuwarn mutanen da hare-haren Isra’ila suka shafa.
“Sanarwar ta ci gabad a cewa duk matakin hana zirga-zirgar jama’a da kayayyaki, laifi ne da zai iya jawo horo mai tsanani, idan babu lalurar yin hakan.
Hamas ta ya barazanar ce bayan a ranar Litinin Isra’ila ta katse hanyoyin kai abinci da ma wutar lantarki da ruwan sha, ta kuma hana shiga ko fita daga yankin Gaza.
Matakin na Isra’ila, wadda ta kai hare-hare sama da 500 a a Gaza, ya haifar da karin fargaba game da matsin rayuwar da al’ummar za su shiga a daidai lokacin da suke bukatar agaji.