Rikicin Gaza: ’Yar majalisar Amurka ta bukaci a taka wa Isra’ila burki
Isra’ila ta katse layukan lantarki da ruwan sha da kuma abinci ga Falasdinawa a yankin Gaza
’Yar majalisar wakilan Amurka ’yar asalin Falasdinu, Rashida Tlaib, ta bukaci Amruka da sauran manyan kasashe su taka wa Isra’ila burki don kawo karshen cin zali da mamayar da take wa al’ummar Falasdinawa a yankin Gaza.
Rashida Tlaib wadda ita ce kadai Bafalasdiniya a majalisar ta bukaci Amurka ta kuma janye duk tallafin da take wa Isra’ila.
- Za a rataye dan sandan da ya kashe lauya mai juna biyu
- An cafke jami’in gidan yari kan zargin luwadi da ƙaramin yaro a Gombe
Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin Isra’ila ta katse layukan lantarki da na ruwan sha da ma hanyoyin safarar abinci zuwa yankin Zirin Gaza.
Gwamnatin Isra’ila ta bayyana cewa daga yanzu, kashi 1 bisa gona na ruwan da Gaza ke samu za ta rika saki, a matsayin matakin kuntata wa Falasdinawa saboda yakin da take da kungiyar Hamas.
’Yar majalisar ta yi kira da “a kawo karshen mamayar Isra’ila a yankin Falasdinawa, sannan ta janye katange su da ta yi, ta kuma bar nuna musu wariyar launi, shi ne kadai zai kawo karshen turjiyar su.
“Tashin hankalin da ke tattare da rayuwa a killace gami da wariya abu ne da babu mai kauna, don haka ya kamata kowa ya samu dama da ’yancin rayuwa cikin aminci,”
Tun bayan cin zabenta a 2018, Tlaib ta dage wajen yin kira da yanke hulda da kuma hukunta Isra’ila kan cin zalin da take wa Falasdinawa.
Sabon rikici
Hakan na zuwa ne bayan harin jiragen da Isra’ila ta hallaka Falasdinawa akalla mutane 550 a hare-haren jirage a yankin Gaza, inda ta shafe sama da shekaru 40 tana yin hakan da sunan kare kai.
Isra’ail mayaye wasu unguwannin Falasdinawa a Gaza, ta killace yankin tare da takaita shige da fice Falasdinawa, baya ga hare-harenta kan masu ibada a Masallacin Kudusu, wuri na uku mafi alfarma a Musulunci.
A tsawon shekaru, Majalisar Dinkin Duniya ta zargi Isra’ila da aikata laifukan yaki a yankin Falasdinawa ta hanyar kisa da kwace gidajen Falasdinawa.
Munafurcin kasashe —Jakadan Falasdinawa
Jakadan Falasdinu a Majalisar Dinkin Duniya Riyad Mansour ya zarign kasashe da kin cewa uffan kan cin zalin da Isra’ila ke wa Falasdinawa a Gaza, inda a ce, ba a jin duriyar “’yan siyasar sai idan yahudawa aka kashe”.
Ya yi wannan furucin ne gabanin taron gaggawa da kwamitin tsaron Majsalir ya kira ranar Lahadi domin tattaunawa kan sabon rikicin tsakanin Hamas da Isra’ila.
Riyad Mansour, wanda shi ne wakilin hukumar gudanarwar Falasdinu ya bukaci kwamitin da ya kawo karshin mamayar Isra’ila a yankin Larabawa, ba wai su rika magana kan abin da ya shafi Isra’ila kawai ba.
“Yanzu ne lokaci da za su gya wa Isra’ila ta riki turbar zaman lafiya ta yadda ba za a samu asarar rai a bangarenta ko bangaren Falasdinuawa ba.”
Wakilan Falasdinawa da Isra’ila ba sa cikin mahalarta zaman, amma Mansour ya bayyana datshe hanyoyi da kuma yawan hare-haren da Isra’ila ke kaiwa a Gaza bai cim ma manufar gurgunta karfin sojin Hamas ba, sai dai ma janyo asara ga fararen hulan a yankin Gaza.
A nata bangaren, Rasha ta bayyana cewa ba wa Falasdinawa da yankinsu ’yanci shi ne kadai mafita daga rikicin tsakaninsu da kasar Isra’ila.
A ranar Litinin Rasha ta sanar da cewa ba wa Falasdinawa kasarsu ami cikakkiyar ’yanci shi ne abin da zai kawo zaman lafiya, ba amfani da karfin soji ba.