Rikicin Gwamna da Minista ya hana ’yan gudun hijira samun tallafi a Taraba
Ministar Harkokin Mata, Sanata Jummai Alhassan ta zargi gwamnatin Jihar Taraba da kin ba ta kayan abincin da Gwamnatin Tarayya ta tura jihar don raba wa ’yan gudun hijira a matsayin taimako.Minista Jummai Alhassan ta yi zargin ne a lokacin da take yi wa dubban ’yan gudun hijirar da ke Sakandaren Kimiyya ta Tarayya da […]
Ministar Harkokin Mata, Sanata Jummai Alhassan ta zargi gwamnatin Jihar Taraba da kin ba ta kayan abincin da Gwamnatin Tarayya ta tura jihar don raba wa ’yan gudun hijira a matsayin taimako.
Minista Jummai Alhassan ta yi zargin ne a lokacin da take yi wa dubban ’yan gudun hijirar da ke Sakandaren Kimiyya ta Tarayya da ke garin Jalingo, inda ta shaida wa ’yan gudun hijirar da suka fito daga jihohin Adamawa da Borno da wadanda rikicin addini da kabilanci ya raba su da gidajensu a garuruwan Wukari da Ibbi da ke jihar cewa su yi hakuri domin gwamnatin jihar ta ki ba ta kayan abincin da Gwamnatin Tarayya ta ce ta raba musu. Ta ce Gwamnatin Tarayya ta bayar da tan dubu 10 na masara don a raba wa ’yan gudun hijirar amma gwamnatin Taraba ta ki yarda ta ba ta kayan.
Wannan bayani ya bai wa ’yan gudun hijira da sauran jama’ar jihar mamaki ganin yadda ’yan gudun hijirar ke fama da wahala. Wadansu ’yan gudun hijirar da suka tattauna da wakilinmu sun yi Allah wadai da yadda gwamantin Taraba ta sa siyasa a cikin lamarin raba kayan taimakon.
Mista James Dama wanda ’yan Boko Haram suka tilasta wa gudun hijira daga karamar Hukumar Madagali a Jihar Adamawa ya nuna bacin rai game da lamarin. Ya ce kin bayar da taimakon da gwamnatin Taraba ta yi ya nuna rashin tausayi da imani. Mista Dama ya ce gwamnatin Taraba ba ta ba su wani taimako ba, amma ta hana wanda ta Tarayya ta tanada a ba su.
Wata ’yar gudun hijira mai suna Malama Rabi wadda aka kashe mijinta da ’ya’yanta a rikicin addini na garin Wukari ta ce dama gwamnatin Taraba ba ta damu da matsalolin ’yan gudun hijirar Wukari da Ibbi ba, domin ba ta taba ba su taimako ko na sisin kwabo ba, sai kuma ga shi Shugaban kasa ya aiko da kayan abinci a ba su amma gwamnatin jihar ta ki yarda a ba su.
Malama Rabi ta nemi Shugaba Buhari ya tsawatar wa Gwamnan Jihar kan wannan batu.
Ta ce su ’yan gudun hijira daga Ibbi da Wukari na sane da wariyar addini da gwamnatin jihar ke nuna musu, inda ta yi zargin cewa gwamnatinTaraba tana bai wa ’yan gudun hijira daga jihohin Adamawa da Borno taimako a boye saboda maganar addini.
Da take jawabi ga manema labarai Minista Jummai ta ce gwamnatin jihar tana ikirarin cewa wai ba ta je ta duka wa Gwamnan Jihar ba ne shi ya sa jihar ta ki bayar da kayyayakin. Ta ce a dokar kasa ba dole ne ta je ta gaida Gwamna ba kuma Shugaban kasa ne ya ba ta umarnin ta zo jihar ta raba wa ’yan gudun hijira kayan taimako ba wai ta je ta gaida Gwamnan ba.
Da yake kare dalilan da suka sa gwamnatin jihar ta ki bai wa Ministar kayayyakin don raba wa ’yan gudun hijirar, Shugaban Ma’aikatan Gidan Gwamnatin Jihar, Mista Rebo Usman ya ce Ministar ba ta shaida wa gwamnatin jihar za ta shigo jihar ba kuma tana raina Gwamnan Jihar da gwamnatinsa.
Mista Rebo Usman ya ce bai kamata a ce mutum mai matsayin Minista ya shigo jihar ba tare da sanar wa Gwamna ba. Ya ce wadansu ministoci su biyu sun kawo ziyara a jihar kuma kafin su zo sun shaida wa gwamnati, kuma jami’an gwamnati sun tarbe su amma ita ta ki yin haka.