Rikicin Isra’ila da Hamas a Gaza

Ana tsakiyar rikici tsakanin kasar Isra’ila da kungiyar Falasdina ta Hamas da ke iko a zirin Gaza ne, Shugaban kasar Amurka Barack Obama da Babban Sakataren Majalisar dinkin Duniya Ban Ki-moon suka bukaci a tsaigaita wuta amma ba tare da samun nasara ba. Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya sha alwashin cewa ba zai tsagaita kai […]

Rikicin Isra’ila da Hamas a Gaza
Rikicin Isra’ila da Hamas a Gaza

Ana tsakiyar rikici tsakanin kasar Isra’ila da kungiyar Falasdina ta Hamas da ke iko a zirin Gaza ne, Shugaban kasar Amurka Barack Obama da Babban Sakataren Majalisar dinkin Duniya Ban Ki-moon suka bukaci a tsaigaita wuta amma ba tare da samun nasara ba. Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya sha alwashin cewa ba zai tsagaita kai hare-hare a zirin Gaza ba, har sai bayan kungiyar Hamas ta dakatar da harba rokoki zuwa cikin kasar Isra’ila.
Rikicin ya samo asali ne bayan Isra’ila ta gano  gawawwakin wasu samari Yahudawa su uku a Gabar Yammacin Kogin Jordan wanda kuma ake zargin membobin kungiyar Hamas da hannu wajen kashesu. Yahudawa sun dauki fansa da kisan wani saurayi Bafalasdine.
Tun bayan wannan ne rikici ya barke tsakanin bangarorin biyu, wanda bisa ga yadda alkaluman yawan mutanen da suka rasu ya bayyana Falasdinawa ne suka fi asara. Har zuwa shekaranjiya Laraba, Bayahude daya ne kawai ya rasa ransa akalla kuma kusan Falasdinawa 200 ne suka mutu sakamakon rikicin wanda aka kwashe kwanaki ana yi. Wannan na faruwa ne saboda Isra’ila na kakkabo dukkannin rokokin da aka harbo daga Gaza wanda hakan kan kare al’ummarta  daga hare-haren mayakan Hamas.
Yawancin wadanda suka rasa rayukansu fararen hula ne da ba su ji ba, ba su gani ba. Kodayake, Isra’ila na ikirarin  cewa tana kai hare-harenta ne kan ’yan ta’adda. Yana da wuya a ce za a iya ware tsaki da tsakuwa a lokacin kai hari a karamin yanki kamar yankin zirin Gaza.
A lokuta da dama ’yan jam’iyyar Likud wadda ke mulkin kasar Isra’ila sun sha yin kira da a dauki tsauraran matakai kan kungiyar Hamas ciki har da harin da ake kaddamarwa a yanzu. Akwai kuma wasu rahotonni da ke cewa wasu dakarun musamman na Isra’ila suna shirye-shiryen kai hari ta kasa a kan iyakarta da Gaza. Wannan matakin idan ya tabbata wani yunkuri ne na kara mamaye yankin da Isra’ila ta janye tun shekarar 2005. An dai kwashe lokaci mai tsawo ana takaddama kan yadda Isra’ila take ci gaba da mamaye yankunan Falasdinawa wanda kuma hakan ke kawo cikas ga samuwar zaman lafiya mai dorewa a yankin.
Mista Netanyahu ya bayyana rashin jin dadinsa ga sulhun da ya gudana tsakanin kungiyar Fatah da Hamas bayan sun kwashe lokaci suna zaman doya da manja. kungiyar Falasdinawa ta Fatah wadda Mahmoud Abbas ke jagoranta, tana da iko ne da Gabar Yammacin Kogin Jordan. Inda zirin Gaza kuma yake karkashin ikon kungiyar Hamas. Saboda dimbin dalilai kamar sauyin siyasar da ke faruwa a yankin Gabas-ta-Tsakiya ciki har da yadda aka mayar da kasar Iran saniyar ware, wadda ita ce babbar mai taimakawa Hamas, Gaza yankin ne da ke matukar bukatar taimako daga kasashe kawayenta. Isra’ila ta ki amincewa da tattauna da Fatah saboda laifin sasantawa da Hamas wadda ita take mata kallon kungiya ce ta ’yan ta’adda.
Hamas kungiya ce mai tsatsauran ra’ayi kuma ta dage kan adawarta da kafa kasar Yahudawa ta Isra’ila. A daya bangaren kungiyar Fatah mai sassaucin ra’ayi ce da take neman biyan bukatunta ta hanyar laluma. Rikicin Falasdinawa da Yahudawa rikici ne da ya ki ci, ya ki cinyewa. Kodayake tun bayan yarjejeniyar tsakanin kasashen Masar da Isra’ila da aka wa lakabi da yarjejeniyar Camp Dabid wadda kasar Amurka ta jagoranta a lokacin, ba a taba samun wata yarjejeniya mai dorewa ba tsakanin Isra’ila da Falasdinawa, mutanen da suna ji suna gani aka karbe masu kasarsu a shekarar 1948 lokacin da ake kokarin kafa kasar Yahudawa. An kwashe dimbin shekaru ana kokarin samar da dauwamamman zaman lafiya a yankin, inda Majalisar dinkin Duniya da Tarayyar Turai da kasashe kamarsu: Amurka da Rasha da Birtaniya duka sun yi kokari amma hakarsu ba ta cimma ruwa ba. Kuma ana danganta rashin nasarar hakan ne da yadda Isra’ila ta ki amincewa da bukatar mika wasu yankuna na Falasdinawa da ta mamaye.
Jama’ar Falasdinawa sun gaji da ga fara sa ba su ga kaho ba kan batun alkawarin kafa masu kasar kansu. Hakazalika, suna ganin kasar Amurka ta fi karkata bangaren Isra’ila maimakon tsayawa tsaka-tsaki. Ya dace Amurka ta sake tunani kuma ta gargadi Isra’ila kan musgunawa Falasdinawa da take.
Akwai bukatar tsagaita wuta don kawo karshen kashe-kashen da ke faruwa a yankin. Ya zama wajibi ga kasashen duniya su tilasta wa kasar Isra’ila da ta yi wannan saboda ita take aikata hakan. Har ila yau, a ci gaba da fatan samun zaman lafiya mai dorewa, ya dace a baiwa Falasdinawa ’yancin kafa kasarsu.