Rikicin iyali ya janyo mutuwar direban ’yar Mutallab
Rikicin iyali ya yi sanadiyar mutuwar direban ’yar fitaccen dan kasuwar nan Alhaji Umaru Mutallab. Marigayin mai suna Abubakar Abdullahi mai shekara 40, ya baro Abuja ne domin sulhunta wasu daga cikin iyalansu da suka dade suna rikici da juna.Mahaifiyar marigayin mai suna Zaliha Aliyu ta fadi cikin kuka cewa: “Wannan rikicin ya kai shekara […]
Rikicin iyali ya yi sanadiyar mutuwar direban ’yar fitaccen dan kasuwar nan Alhaji Umaru Mutallab. Marigayin mai suna Abubakar Abdullahi mai shekara 40, ya baro Abuja ne domin sulhunta wasu daga cikin iyalansu da suka dade suna rikici da juna.
Mahaifiyar marigayin mai suna Zaliha Aliyu ta fadi cikin kuka cewa: “Wannan rikicin ya kai shekara kusan uku, kuma dukkansu ’yan uwan juna ne da shi marigayin da wadanda suka yi kisan.Wannan matsala da yake ta gida ce na sanar da dattawa sau hudu kuma duk ya yi ne domin daukar mataki saboda wanda ya yi kisan mai suna Usman tare da dan uwansa Garba duk suna zaune ne a gidan mijin ’yata Maimuna, inda a koyaushe suke yawan fada. Shi kuma Usman yana yawan furta cewa zai kashe ta duk lokacin da suke rikici. Mijinta wanda kawu yake a wurinsu don haka duk abin da yake yi ba ya sa baki, gudun wai kada ya saba da ’yar uwarsa. Hakan ya sa mijinta mai suna Musa Muhammad ya ki tankawa har lamarin ya baci, shi ne marigayin ya ce bari ya zo ya ji matsalar ashe su suna da wata manufa a boye. Jin cewa marigayi zai ziyarci gidan domin sulhuntawa da jawo hankalinsu sai Usman ya gayyaci ’ya daba abokansa, lokacin da marigayin ya shiga gidan sai Usman da Garba suka taso masa da fada-fada, shi kuma ganin yana babba gare su sai ya mari Usman, sai kawai suka kama shi da dambe gida ya cika, jama’a suka kama marigayi suka fito da shi waje suka ba shi hakuri suka ce ya koma gida.”
Ta ce a kan hanyar zuwa gida ne sai Usman ya buga masa rodi a kai, wadanda ya gayyato suka haushi da duka a wurin ajali ya yi halinsa.
Maimunatu wadda a kan sulhunta ta da abokan zama ne aka kashe yayanta ta ce rigima ce tsakaninta da matar Usman ke yawan shiga tsakninsu, “Sai shi Usman ya rika taya matarsa har ta kai yana cewa sai ya kashe ni ko ya ce sai ya kashe ’ya’yana. A kan haka ne marigayin ya zo domin ya sulhunta mu, amma sai Usman ya fara zaginsa yana ci masa mutunci. Bayan an raba su ya fita sai suka bi shi tare da abokansa suka kashe shi da rana tsaka.”
Ta ce lokacin da abin ya faru ta kira mijinta wanda shi ma direban mota ne amma har bayana kwana biyu da rasuwar maigidanta bai zo gidansu ballantana ya ga halin da suke ciki ko ya tausaya wa mahaifiyarsu kan abin da ’ya’yan yarsa suka aikata. “Sai ma aikowa suke da bakaken maganganu ganin cewa an kama Usman da ya jagoranci kisan, suna barazanar kashe ni ko kashe ’ya’yana kan kama dan uwansu,” inji ta.
Aminiya ta yi kokarin jin ta bakin mijin Maimuna mai suna Muhammad inda wakilinmu ya ziyarci gidansa har sau uku a Sarkakiya Unguwar Zariya amma bai samu nasara ba, sai dai da wakilinmu ya neme shi ta wayar hannu ya ce a kyale shi ya ji da abin da ke damunsa.
daya daga cikin wadanda ake zargi da kashe marigayi Abubakar mai suna Abubakar ya musanta sa hannunsa a kisan, ya ce “Gaskiyar magana dukkanmu ’yan uwa ne, rikice ne na dangi kuma a kan gidan da aka yi hada-ka wajen gina shi ne ake rikincin jiran gado a kansa alhali wadanda suka gina shi duk suna raye.”
Ya ce, “marigayin yayana ne shi kuma wanda ake zargi da kisan kanena ne uwa daya uba daya, mijin wanda ake fada a kanta kawuna ne domin auren zumunta aka yi musu. Mahaifianmu uwansu daya ubansu daya dukkanmu abu daya ne. Kuma wannan rikici bai kai shekara uku kamar yadda ake ta fada ba, ina son ka zaga makwabta ka yi binciken halin kowane daya daga cikinmu.
Ya musanta zargin da ake yi cewa ya ce zai kashe kudi domin a canja sakamakon binciken da likita zai yi don a nuna ba da rodi aka kashe marigayin ba. Sannan ya musanta zargin cewa ya ba wanda ake zargin kudi ya gudu, inda ya ce wanda ake zargin ne ya kai kansa ga ’yan sanda. “Abubuwan suna da yawa da ban so in yi magana a kan lamarin da ’yan jarida ba amma hakan ya zama dole domin jama’a su fahimci gaskiyar lamarin. Wanda ake zargi da sanadiyyar mutuwar marigayi haka Allah Ya kaddaro masa, domin marigayin ai ya fi karfin wanda suka yi rikicin tare kuma da za ka zo ka dubi jikinsa za ka ga raunukan da shi marigayin ya ji masa, kuma a yadda bayanai suka zo mana an ce marigayin ya dauki abokin fadan nasa da nufin jefa shi a cikin rijiya amma jama’a suka kwato shi,” inji shi.
Wakilinmu ya tuntubi babban ofishin ’yan sanda na kofar Fada, Zariya, inda Mataimaki Babban Jami’in ’Yan sandan yankin DSP Yakubu B. Abbas ya tabbatar da faruwar lamarin. Ya ce bayan kama wadanda ake zargi da hannu a lamarin sun tura su hedkwatarsu da ke Kaduna domin ci gaba da bincike.