Rikicin Jihar Nasarawa abin kunya ne ga Musulmi da Kirista – Barista Ode Magaji
Barista Clement Ode Magaji shi ne Sakataren Hukumar Jin Dadin Kiristocin masu Ziyara ta Jihar Nasarawa. A tattaunawarsa da wakilinmu a Lafiya ya ce shugabannin Kiristocin jihar musamman CAN suna nuna halin ko-in-kula da harkokin hukumar. Ya kuma ce rikicin jihar ba shi da alaka da addini: Aminiya: Wadanne nasarori kuka samu bayan nada ka […]
Barista Clement Ode Magaji shi ne Sakataren Hukumar Jin Dadin Kiristocin masu Ziyara ta Jihar Nasarawa. A tattaunawarsa da wakilinmu a Lafiya ya ce shugabannin Kiristocin jihar musamman CAN suna nuna halin ko-in-kula da harkokin hukumar. Ya kuma ce rikicin jihar ba shi da alaka da addini:
Aminiya: Wadanne nasarori kuka samu bayan nada ka sakataren wannan hukumar?
Mun samu nasarori da dama, misali lokacin da na zo ban tarar da ko rediyo daya mai aiki ba. Amma yau ga na’urorin da muka sayo, wannan ofishi yau yana da talabijin na zamani. Muna da firiji a kowane ofishi. Haka masaukin bakinmu muna da wadannan kayayyaki. Kuma mun samu nasarar ziyarar da maniyyata Kiristoci daga jihar nan suka kai kasa Mai tsarki a bara, mun tafi kusan duk wuraren da masu ziyara ke tafiya. Da muka dawo gida irin shaidar da suka bayar ita ce a kan kyakkyawan shugabanci a wannan hukuma. Haka ya sa Gwamna Al-Makura ya yaba mana sosai a lokacin da shugaban kungiyar Kiristoci na Jihar Nasarawa Bishop Mila Maza ya jagoranci maziyartar. Gwamnan ya ce masa kafin shi da tawagarsa su dawo gida an gaya masa sun samu nasara. Kuma a lokacinmu ne maziyarta Kiristoci suka wallafa littafi suka kaddamar. Makasudin wallafa littafin ba don neman kudi ba ne. Mun yi ne don hada kan Kirista da Musulmi a samu zaman lafiya. Shi ya sa muka gayyaci Kiristoci domin nuna wa duniya cewa a wannan lokaci na rashin zaman lafiya a jihar da kasa baki daya idan da wani da ke da shawarar da zai bayar domin magance rigirgimun, ya zo ya bayar saboda tabbatar da zaman lafiya.
Aminiya: Wadanne matsaloli kuke fuskanta a hukumar?
A wannan hukuma muna fuskantar matsaloli da dama. Na farko shi ne yadda za mu jawo hankalin Kiristocin jihar nan da shugabanninsu son su zo mu hada kai mu yi aiki don sauke nauyin da ke kan hukumar. Na biyu shi ne yadda za su daina tunanin cewa tunda gwamnati tana biya musu bukatunsu, me suke nema a wurinmu kuma. Muna neman shawarwarinsu ne ba kudinsu ba. Kada ka zo lokacin da kake son tafiya Jerusalem kawai. Mu ne za mu yi maka hanyar tafiya Jerusalem. Wata matsalar ita ce ba mu da mutanen da za su rika daukar nauyin shiryes-shiryenmu a gidan rediyo ko jaridu da sauransu. Muna so mu rika sanar da mutane ta kafofin watsa labarai kan harkokin wannan hukuma da kuma muhimmancin zaman lafiya da juna a koyaushe, amma ba ma iya yin haka, don babu wani Kirista da ya zo ya ce ya dauki nauyin yi mana haka. Ka ga yadda Musulmi suke yi, mutum daya kan dauki nauyin irin wadannan shirye-shirye a gidan rediyo ko jarida musamman a lokacin Azumi. Amma mu Kiristoci ba mu yin haka, wannan babban kalubale ne. Wadannan su ne manyan matsaloli da hukumar ke fuskanta a yanzu.
Aminiya: Kana nufin ba ku samun tallafi daga kungiyoyin Kiristoci na jihar ke nan?
A gaskiya Kiristocin jihar nan ba sa kula da mu yadda ya kamata. Ba sa ma ziyartar wannan hukuma. Na dade ina cewa muna nan ba don mun fi kowa ilimi ko wani abu ne ba. Su wane ne ya kamata su rika ba mu shawarwari? Ba shakka kungiyar CAN ya kamata a ce tana ganinmu a matsayin ’yan uwanta. Amma abin tambaya shi ne ko CAN tana yin haka? Ba wani cikin shugabannin kungiyar da ya taba cewa bari in kai wa wannan hukumar ziyara in ga me suke yi. Ko shawarwari ba su ba hukumar, ko bikin kaddamar da littafinmu da muka yi a kwanakin baya, shugaban CAN ne kawai ya halarci bikin. Ina sauran Kiristocin jihar nan suke? Ka duba yadda Musulmi da muka gayyato suka fito da yawansu suka halarci bikin. A gaskiya na ji kunya sosai game da haka, mun sanar da su, ban san dalilin da ya sa suka ki zuwa ba. Ko don ni ba na cikin kungiyarsu ne ban sani ba. Amma ina so in sanar da su cewa, wannan hukuma ta Kiristoci ne baki daya. Ko kana cocin ECWA ne ko na Goodnews ko ERCC ko Katolika, nan za ka bi ka tafi Jerusalem. Mun jima muna sanarwa a gidajen rediyo da jaridu cikin Ingilishi da Hausa cewa ba wai su zo, su ba da kudi ne ba. Ana so su zo mu hada kai mu sanar da Kiristoci harkokin wannan hukuma da sauransu. Idan ka zo a matsayinka na shugaban Kiristoci ka ba da shawara za ta taimaka sosai wajen daukaka hukumar. Gwamnati ne kawai take daukar nauyin wannan hukuma hakan abin kunya ne saboda muna da manyan Kiristoci a wannan jiha. Amma da yau za mu sanar cewa Gwamna ya ce gobe za a raba kujeru ga maziyarta Kiristoci za ka ga wannan wuri ya cika makil da shugabannin Kiristocin da ’yan siyasa kowa yana bukatar tafiya. Matsalar da muke fuskanta ke nan, ba mu samun hadin kai balle tallafi, kuma ina kalubalantarsu ne don su sauya tunani.
Aminiya: Jihar nan na cikin jihohin da ke son janye biya wa maniyyata kudin kujera, mene ne ra’ayinka game da haka?
Maganar ziyarar kasa Mai tsarki ya kamata maniyyata su rika ganinsa a matsayin wajibi ne a rayuwarsu. Idan ka karanta Littafi Mai tsarki za ka tarar akwai ayoyi da suka umurci mawadata kan tafiya kasa Mai tsarki don su yi addu’a. Haka na nufin tafiya Jerusalem ya kamata ya zama daya daga cikin aikin ibadar kowane Kirista mawadaci. Mun gode Allah gwamnati ta shigo lamarin don taimakawa. Amma kai Kirista dole ka yi iya kokarinka don ganin ka yi tanadi don ka tafi Jerusalem. Saboda haka ya kamata kowa ya biya wa kansa kudin tafiya kasa Mai tsarki ba ya jira gwamnati ta biya masa ba. Lokacin da na fara aiki a matsayin Sakataren wannan hukuma mutum takwas ne kacal suka biya wa kansu kudin tafiya a shekarar. Amma bayan wayar da kai da muka yi yau muna da mutum 28 da suka biya. Idan muka ci gaba da haka na tabbata nan gaba za mu samu karin masu biya wa kansu.
Aminiya: Mene ne gaskiyar batun cwea wasu Musulmi a nan jihar suna biya wa Kiristoci kudin zuwa Jerusalem?
kwarai wanna gaskiya ne. Kamar yadda na bayyana maka a baya daya daga cikin manufofinmu na gayyato Musulmi a lokacin kaddamar da littafinmu shi ne mu nuna godiyarmu ga shugabannin Musulmi da Alhazai da ’yan siyasa da sarakunan gargajiya da sauransu da suke biya wa maniyyatanmu kudin zuwa Jerusalem. Misali a bara, wani dan majalisar jihar Musulmi ya biya kudin kujera hudu ga maniyyata Kiristoci. Shi Musulmi ne amma ya ga ya dace ya biya wa Kiristocin mazabarsa kudin tafiya Jerusalem. Kuma ina kira ga Kiristoci ’yan siyasa, su yi koyi da abin da wannan Musulmi ya yi ga Kiristoci ta hanyar biya wa Musulmi kudin zuwa aikin Hajji. Idan suka yi haka zumuncin da ke tsakanin mabiya addinan biyu zai inganta. Dukkanku shugabannin mutane ne baki daya ba na addini daya kawai ba.
Aminiya: Jihar nan a ’yan kwanakin nan tana fama da tashin hankali, ana kashe-kashe da asarar dukiya a kudancin jihar. Wasu na alakanta hakan da addini, me za ka ce?
Tashin-tashinan da yake aukuwa a nan jihar, idan aka ce yana da alaka da addini, to, sai mu tambayi wadanda ke fadan ko ba Musulmi da Kiristoci a cikinsu. Idan akwai Musulmi da Kiristoci a bangarorin biyu masu fada, to, yaya za a ce fadan addini ne? Idan shugabanninmu sun ki yin magana, mu ya ku bayi ya kamata mu natsu mu tambayi kanmu yaya muke fada? Yaya muka iya zama da juna a lokaci mai tsawo ba tare da tashin hankali ba, sai a wannan lokaci? Abin kunya ne kuma rashin mutunci ne gare mu baki daya Musulmi da Kirista da dukkan kabilu, mu rika kashe juna, domin idan kafin wannan lokaci akwai kyakkyawar dangantaka a tsakaninmu hakan na nufin akwai wani abu da ke faruwa ba daidai ba a yanzu. Ba ma so mu ambaci suna, amma yanzu idan ka fita waje misali rikicin yankunan Bassa me ya sa aka dauki lokaci mai tsawo ana fada da ya kai ga wannan asarar rayuka da dukiya? Ba Musulmi da Kiristoci a wannan yanki ne? Idan suna nan, me suka yi don magance wannan lamari? Idan suka kasa yin haka, to, laifinsu ne. Ba sarakunan gargajiya da gwamnati ta san su a yankin ne? Me suka yi don shawo kan lamarin? Ba wakilan wadannan mutane ne a gwamnati? Me suka yi lokacin da aka soma rigirgimun? Muna da shugabannin matasa a wadannan yankuna, me suka yi? Abin bakin ciki shi ne yadda matasa suka bari ana amfani da su don aikata miyagun ayyuka maimakon na ci gaba a yankunansu. Misali, idan ka tafi kauyena za ka ga cewa zumuncin da ke tsakanin mutumin Eggon da Gwandara ya yi karfi sosai ta yadda idan ka ce wa Eggon ya dauki bulala ya zane Gwandara zai ce ba zai iya ba. Haka idan ka ce da Gwandara ya dauki tsintsiya ya bugi Eggon zai ce ba zai iya ba. Kuma idan Eggon yana magana cikin harshen Gwandara, za ka yi mamaki. Amma abin mamaki yau an wayigari muna neman kan junanmu mu gille, hakan na nufin wani abu yana faruwa ba daidai ba, kuma shugabanninmu sun sani. Sai dai sun ki yin magana ne.
Don haka ina ba jama’ar Jihar Nasarawa shawara su guje wa fitina, domin su ba gwamnati damar ci gaba da gudanar da kyakkyawan shugabancin da take yi.