Rikicin Jihar Nasarawa: Miyetti Allah ta bukaci zaman tattaunawa
kungiyar Fulani ta Miyetti Allah Kautal Hore reshen jihar Nassarawa, ta bukaci gwamnatin jihar da ta shirya taro a tsakanin jagororin kabilu da ke rigima a tsakaninsu a jihar, don shawo karshen tarzoma da ke faruwa a tsakanin kabilun, tare da kawo zaman lafiya mai ma’ana.Shugabar kungiyar na Jihar Nasarawa, Alhaji Gidado Idris ne ya […]
kungiyar Fulani ta Miyetti Allah Kautal Hore reshen jihar Nassarawa, ta bukaci gwamnatin jihar da ta shirya taro a tsakanin jagororin kabilu da ke rigima a tsakaninsu a jihar, don shawo karshen tarzoma da ke faruwa a tsakanin kabilun, tare da kawo zaman lafiya mai ma’ana.
Shugabar kungiyar na Jihar Nasarawa, Alhaji Gidado Idris ne ya bayyana hakan a yayin wata zantawa da wakilinmu a ofishinsa da ke Kasuwar Kara ta garin Masaka. Ya ce yadda adadin ’yan gudun hijira mafi yawa mata da kananan yara ke kwararowa zuwa cikin yankin karamar Hukumar Karu kadai, al’amarin na da ban tausayi, yadda al’amarin ya shafi sauran wasu karin kananan hukumomi daban.
Ya ce a baya an fuskanci rikicin da ya dara irin na Jihar Nassarawa muni a makwabciyarta Jihar Benuwai amma bayan an gudanar da taro a tsakanin kabilar Fulani da na Tibi tare da sasantawa da juna, ba a sake samun aukuwar wani tashin hankali ba a jihar tun daga wancan lokaci. Ya ce wuraren da ’yan gudun hijiran suka yi kaka-gida a karamar hukumar ta Karu su ne; Aso-B da Gurukun-kasa, sai kuma Unguwar Jaba.
Ya bayyana cewa muhimman abubuwan da ke damun Fulani a jihar sun hada da bayyana al’ummarsu a matsayin baki komin dadewansu a tarihin yanki, sai kuma daukar doka a hannu a kan ’ya’yansu a duk lokacin da aka samu kuskuren kutsen dabbobi cikin gona, a maimakon bukatar diyya kamar yadda aka saba yi a baya.