Rikicin kabilanci: kura ta lafa a yankin Gassol

Al’amura sun fara komawa daidai a garin Tella da ke karamar Hukumar Gassol a Jihar Taraba inda aka samu tashin hankalin da ke da alaka da addini da kabilanci. Rikicin wanda ya jawo mutuwar mutane da dama tare da asarar dukiya ta niliyoyin Naira ya biyo bayan sukar wasu matasa uku da wuka da wani […]

Rikicin kabilanci: kura ta lafa a yankin Gassol
Rikicin kabilanci: kura ta lafa a yankin Gassol

Al’amura sun fara komawa daidai a garin Tella da ke karamar Hukumar Gassol a Jihar Taraba inda aka samu tashin hankalin da ke da alaka da addini da kabilanci.

Rikicin wanda ya jawo mutuwar mutane da dama tare da asarar dukiya ta niliyoyin Naira ya biyo bayan sukar wasu matasa uku da wuka da wani dan kabilar Jukun ya yi a wurin shan tabar wiwi, kuma aka zargi jami’an tsaro da kin daukar wani mataki a kansa.
Wanda ake zargi da aikata wannan ta’asa mai suna Horror an ce da ma ya addabi jama’ar garin Tella kuma ya taba zama gidan yari fiye da sau uku saboda munanan laifuffukan da yake aikatawa.
An ce Horror ya yi kusan fin karfin hukuma kuma ana zargin iyayensa da ba shi karfin gwiwa ta hanyar hana hukuma kama shi duk lokacin da ya yi wata aika-aika.
Majiya Aminiya ta ce ganin hukuma ta ki daukar mataki a kan Horror ne sai ‘yan uwan wadanda ya soka da wuka wadanda daya daga cikinsu ya mutu suka nemi daukar fansa.
Majiyar ta ce bayan ‘yan uwan wadanda ya soka raunata sun kamo Horror domin daukar fansa ne, sai ‘yan uwan Horror suka fito da makamai suka fara kone- kone daga nan rikicin ya fadada zuwa kone-konen shaguna da gidajen jama’a tare da hallaka mutane.
Wani mazaunin garin Tella mai suna Ibrahim Tella ya ce ana zargin Horror da kasancewa babban dan ta’adda a garin tun dogon lokaci.
Malam Ibrahim ya ce ba wanda ya isa ya taba Horror da sauran abokan ta’addancinsa saboda suna takamar cewa su ‘yan kabilar Jukun ne.
Ya ce Horror ya sha fadi a bainar jama’a cewa zai yi sanadiyyar kawo fitina a garin Tella.
Binciken da wakilinmu ya gudanar ya gano cewa an baza jami’an tsaro da suka hada da ‘yan sanda da sojoji da ‘yan banga wadanda suka maido da zaman lafiya a ciki da kewayen garin Tella.
Kakakin Rundunar ‘Yan sandan Jihar Taraba, ASP Joseph Kwaji ya ce an tura jami’an tsaro yankin don tabbatar da zaman lafiya da kare rayuka da dukiyoyin jama’a.
Shugaban karamar Hukumar Gassol, Alhaji Tukura Bashiru ya nuna taikaci kan aukuwar lamarin. Ya ce iyaye a garin na Tella na da laifi kan aukuwar lamarin domin sun ki daukar mataki a kan ‘ya’yansu. Ya ce wanda ya tayar da fitinar mai suna Horror an dade ana zargin yana kawo fitina a garin Tellea da sauran wurare. Ya bayar da tabbacin cewa hukuma za ta kama shi a duk inda yake kuma za a hukunta shi gwargwadon laifinsa.
Alhaji Tukura Bashiru ya nuna damuwarsa kan yadda jama’ar garin ke ta ficewa da iyalansu zuwa wasu warare.
Jihar ta Taraba a ‘yan shekaru nan tana fama da fadace-fadacen da ke da alaka da kabilanci da addini, musamman a yankunan Kudancin jihar da ake zargin ‘yan kabilar Jukun da haddasawa.