Rikicin kabilanci ya ci dalibai 20 a Nasarawa
Sama da dalibai 20 da ke karatu a Kwalejin Ilimi ta Ipere da ke Agyaragu a karamar Hukumar Obi a Jihar Nasarawa suka rasa rayukansu sakamakon rikicin kabilanci a tsakanin ’yan kabilar Eggon da na Migilli da ya auku kwanakin baya. Shugaban makarantar Mista Agwale Ayuba ne ya bayyana haka a jawabinsa a lokacin da […]
Sama da dalibai 20 da ke karatu a Kwalejin Ilimi ta Ipere da ke Agyaragu a karamar Hukumar Obi a Jihar Nasarawa suka rasa rayukansu sakamakon rikicin kabilanci a tsakanin ’yan kabilar Eggon da na Migilli da ya auku kwanakin baya.
Shugaban makarantar Mista Agwale Ayuba ne ya bayyana haka a jawabinsa a lokacin da mambobin kungiyar ’Yan jarida ta kasa (NUJ) reshen jihar suka ziyarci kwalejin. Shugaban ya ce kwalejin wadda mai zaman kanta wasu masu kishin kasa ’yan kabilar Migilli ne suka kafa ta kimanin shekara bakwai da suka gabata da manufar taimaka wa kokarin gwamnatin jihar wajen samar wa al’ummarta ingantaccen ilimi. Ya ce kwalejin ta samu ci gaba sosai tunda aka kafa ta da suka hada da samun amincewar Hukumar Kula da Kwalejojin ilimi ta kasa (NCCE), inda ta amince kwalejin ta ci gaba da gudanar da wasu kwasa-kwasai 10 daga cikin 20, kuma suna sa rai hukumar za ta amince da sauran 10 nan ba da dadewa ba.
Ya kara da cewa a halin yanzu makarantar ta samu shiga jerin manyan makarantun kasar nan da ke cikin tsarin JAMB yayin da dalibai da dama da kwalejin ta yaye suka samu damar ci gaba da karatu a jami’o’in kasar nan.
Ya alakanta dimbin nasarori da kwalejin ta cimma ga sadaukarwa da aiki tukuru da malaman makarantan ke yi.
Mista Ayuba Agwale ya ce kalubale da kwalejin ke fuskanta a yanzu shi ne na koma baya sakamakon rigirgimun kabilanci da yankin ke fuskanta a kai-a kai musamman wanda ya auku kwanakin baya inda makarantan ta rasa dalibanta sama da 20, kuma malamanta da dama lamarin ya shafe su. Ya nuna takaici kan yadda a duk lokaci da ake fada a yankin wadansu ke amfani da haka suna lalatawa tare da sace kayayyakin makarantar lamari da ya ce yana gurgurta ci gaban kwalejin.
Ya bukaci gwamnatoci a dukkan matakai musamman na tarayya ta samar da cikakken tsaro ga kwalejin ta kuma taimaka musu da tallafin nan da take bai wa manyan makarantu a karkashin asusun TETFUND don ba su damar farfadowa daga asarar da suka yi a lokutan fadace-fadacen.
Tun farko a jawabin shugaban kungiyar NUJ na jihar Kwamared Dan Yakubu ya gode wa mahukuntan kwalejin bisa kyakkyawar tarbar da suka yi musu inda ya ce sun kai ziyarar ce domin su duba yanayin ci gaban kwalejin. Ya jinjina wa hangan nesa da ’ya’yan Migilli suka yi na kafa makarantar inda ya ce ba girman makaranta ba ne ilimi, amma samun kwararrun malamai shi ne ilimi. Daga nan ya bukaci malaman makarantar su ci gaba da koyar da kyakkyawar tarbiyya ga daliban don samun shugabannin gobe nagari.