Rikicin kabilanci ya ci mutum 33 a Kaduna
Rahotanni daga karamar Hukumar Kajuru da ke Kudancin Kaduna sun ce akalla mutum 33 ne suka rasu a rikici da ya auku a tsakanin Fulani da ’yan kabilar Kadara a ranar Litinin zuwa Talata a kauyukan Unguwar Aku da Kufana. Bayanai daga yankin sun ce rikicin ya samo asali ne lokacin da wata mata ’yar […]

Rahotanni daga karamar Hukumar Kajuru da ke Kudancin Kaduna sun ce akalla mutum 33 ne suka rasu a rikici da ya auku a tsakanin Fulani da ’yan kabilar Kadara a ranar Litinin zuwa Talata a kauyukan Unguwar Aku da Kufana.
Bayanai daga yankin sun ce rikicin ya samo asali ne lokacin da wata mata ’yar kabilar Kadara da ke noma ta shaida wa ’ya’yanta cewa wadansu ’ya’yan Fulani da ke kiwo sun yi kokarin yi mata fyade.
Su kuma ’ya’yan matar da suka je ba su tarar da makiyayan a gonar ba da suka hango wani da ke kiwo a can gefe sai suka far masa da duka har ya rasu.
Wani labarin ya ce lamarin ya taso ne saboda a kwanakin baya an kashe wani Bafulatani bisa zargin dan fashi ne da ya addabi mutanen yankin.
Ardon Ardodin Kachiya kuma Shugaban kungiyar Miyetti Allah a Arewa maso Yamma, Alhaji Ahmadu Ardo ya bayyana wa Aminiya ta wayar tarho cewa a yanzu haka akwai mutane sama da dari da ke gudun hijira a gidansa. “Yanzu haka da muke hira da kai inda rikicin nan ya faru babu kyau. Amma yanzu mun riga mun yi jana’izar wadanda suka rasu. Abin da kawai muke so daga wajen gwamnati musamman jami’an tsaro shi ne su taimaka su yi mana rakiya zuwa cikin dazuzzuka domin tsinto gawarwarkin sauran ’yan uwanmu da rikicin ya shafa. Muna iya zuwa da kanmu amma muna gudun kada sauran kabilun su dauka za mu je ramuwar gayya ne. Shi ya sa muke son mu je tare da jami’an tsaro,” inji shi.
Alhaji Adamu ya yaba wa shugaban ’yan sandan yankin, saboda kokarin da ya yi wajen magance matsalar.
daya daga cikin matasan Kadara a yankin ya tabbatar da kisan inda ya ce Bafulatanin da aka fara kashewa sanannen dan fashi ne a yankin. “Sarkinmu na Kadara har ya kira Fulani ya yi masu bayani a kan abin da ya faru saboda matasansu sun sha alwashin daukar fansar kisan da aka yi wa Bafulatanin amma duk da haka sai da suka hallaka matasan Kadara biyar da suke zargi da hannu wajen kisan dan uwansu. Wannan ne ya bata wa matasanmu na Kadara rai, su ma suka kai harin ramuwar gayya a kansu a Kauru,” inji shi.
Mukaddashin Kakakin ’Yan sandan Jihar, ASP Yakubu Sabo ya tabbatar da aukuwar rikicin amma ya ki ya ambaci yawan mutanen da suka rasu. “Rikici ne a tsakanin kabilu biyu kuma tuni mun aika da ’yan sanda da sojoji domin kwantar da rikicin. Yanzu dai hankula sun kwanta a wuraren da abin ya faru, sai dai ba zan iya tabbatar da yawan mutanen da suka rasu ba,” inji shi.