Rikicin kabilanci ya ci mutum daya a Binuwai

Hukumar ’yan sanda a Jihar Biniwai ta bayyana cewa mutum daya ne ya rasa ransa a fadan kabilanci da ya faru a yankin Mbayion na karamar Hukumar Gboko. Kakakin rundunar ’yan sanda a jihar, Moses Joel Yanu ya ce an samu nasarar kama wasu mutane da ake zargin suna da hannu wajen faruwar rikicin. Sai […]

Rikicin kabilanci ya ci mutum daya a Binuwai

Hukumar ’yan sanda a Jihar Biniwai ta bayyana cewa mutum daya ne ya rasa ransa a fadan kabilanci da ya faru a yankin Mbayion na karamar Hukumar Gboko.

Kakakin rundunar ’yan sanda a jihar, Moses Joel Yanu ya ce an samu nasarar kama wasu mutane da ake zargin suna da hannu wajen faruwar rikicin.

Sai dai wasu mazauna kauyen sun bayyana wa wakilinmu cewa mutanen da suka mutu sun wuce daya, a yayin rikicin, wanda aka fara tun daga ranar Lahadin da ta gabata kuma ya ci gaba zuwa kwanaki biyu. An kona gidaje a yayin wannan hargitsi na kabilanci. Haka kuma an samu tabbacin cewa almarin ya yi kamari, inda wasu daga masu rikicin suka yi ta hako gawarwakin mutane daga makabarta a yankin, kamar kuma yadda aka yi ta barnata amfanin gona a gonakin mutane.

A yayin rubuta rahoton nan, an samu bayanin da ke tabbatar da cewa mazauna yankin suna ta yin kaura, a yayin da iyalan masarautun Ormo na Mbajob da na Mbasakera da na Igyura na masarautar Mbaasaya da ke yankunan Mbayion a karamar Hukumar Gboko, duk al’amarin ya shafe su, inda suka samu rashi na dukiya da sauransu, a sakamkon rikicin.