Rikicin Kaduna: El-Rufai ya tabbatar da rasuwar mutum 22

Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya ce, rikicin da ya faru a jihar ya yi sanadiyyar rasuwar akalla mutum 22 tare da raunata mutum 44 a sassan jihar ranar Lahadi. Gwamnan ya ce, an lalata kadarorin jama’a da dama a cikin birnin Kaduna. Gwamnatin jihar ta sassauta dokar hana fitan da aka sanya a jihar […]

Rikicin Kaduna: El-Rufai ya tabbatar da rasuwar mutum 22

Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya ce, rikicin da ya faru a jihar ya yi sanadiyyar rasuwar akalla mutum 22 tare da raunata mutum 44 a sassan jihar ranar Lahadi.

Gwamnan ya ce, an lalata kadarorin jama’a da dama a cikin birnin Kaduna.

Gwamnatin jihar ta sassauta dokar hana fitan da aka sanya a jihar daga sa’o’i 24 zuwa sa’o’i huxu don baiwa jama’a damar fita neman abinci da sauran bukatun su.