Rikicin Kaduna: Sai an hukunta masu laifi – Buhari
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce, sai gwamnati ta hukunta wadanda aka samu da laifin rikicin jihar Kaduna wanda ya yi sanadiyyar rasa rayukan mutum 77. Shugaban ya bayyana hakan ne yayin ganawarsa da sarakunan da malamai shugabannin siyasa a dandalin wasannin na Umaru Musa Yar’Adua Kaduna. Buhari ya sake jaddadawa wajibi ne a dakatar […]
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce, sai gwamnati ta hukunta wadanda aka samu da laifin rikicin jihar Kaduna wanda ya yi sanadiyyar rasa rayukan mutum 77.
Shugaban ya bayyana hakan ne yayin ganawarsa da sarakunan da malamai shugabannin siyasa a dandalin wasannin na Umaru Musa Yar’Adua Kaduna. Buhari ya sake jaddadawa wajibi ne a dakatar da kisan gilla a jihar.