Rikicin kaka da jikanya: Kotu ta karbi takardun gida
Ranar Litinin da ta gabata ce Kotun Shari’ar Musulunci ta biyu da ke a Magajin Gari, tsakiyar birnin Kaduna ta sake dage sauraren kara tsakanin kaka da jikanyarta a kan takardun gadon gida. Yanzu haka mai Shari’a Aliyu Mukhtar bayan ya karbe takardun gidan da ake rigima a kansu kamar yadda ya umurta a kawo […]
Ranar Litinin da ta gabata ce Kotun Shari’ar Musulunci ta biyu da ke a Magajin Gari, tsakiyar birnin Kaduna ta sake dage sauraren kara tsakanin kaka da jikanyarta a kan takardun gadon gida.
Yanzu haka mai Shari’a Aliyu Mukhtar bayan ya karbe takardun gidan da ake rigima a kansu kamar yadda ya umurta a kawo masa su, sai ya dage ci gaba da sauraren shari’ar zuwa ranar 3 ga watan gobe.
Idan za a tuna, Aminiya ta ruwaito a makon da ya gabata cewa A’isha Ibrahim ta yi karar kakarta ta wajen uwa, Hajiya Maryam Sidi a kotu saboda wai ta hana ta takardun gidanta na gado.
Ita A’isha ta ce ta kai kara ne domin kotu ta taimaka mata wajen karbo mata takardun gadon gidanta da ke hannun kakar tata, shekaru bakwai da suka wuce.
Mai Shari’a Aliyu a waccen makon ya bukaci wacce ake kara da ta kawo wa kotu takardun gidan, inda ita kuma ta cika alkawari a wannan karon.
Saboda haka sai Alkali ya dage shari’ar, domin inda hali za a je a duba gidan, wanda ke kan titin Kinkino, GRA, Unguwar Rimi Kaduna.
Wacce ake kara Hajiya Sidi, jim kadan bayan an fito daga cikin kotu; ta shaida wa manema labarai cewa ta hana jikanyarta takardun gidan ne saboda tsoron kada ta lalata dukiyarta.
“Saboda haka na ji dadi tunda na mika takardun ga kotu kamar yadda kotu ta nema in yi. Domin ba ni da wani abu da nake boyewa dangane da hana ta takardun.
“Aisha da ’yar uwarta Khadija, duk ina kaunarsu kuma ba zan so ganinsu cikin damuwa ba; shi ya sa ma tun farko na hana ta tarkadun saboda gudun kar su lalata dukiyar.” Inji ta.
Game da ko za ta halarci bikin auren jikar tata, wanda za a yi a watan gobe, duk kuwa da cewa ta yi kararta a gaban kotu, sai kakar ta ce: “Ai da ni za a yi wannan aure in sha Allahu, ai angona ne. Ni da nake fara ita, A’isha ai baka ce. Ina kuma yi mata fatan Allah Ya ba su zama lafiya da angonta.” Inji ta cikin raha.