Rikicin Kasuwar Magani: An gurfanar da mutum 65 a kotu
Akalla mutum 65 ne Gwamnatin Jihar Kaduna ta gurfanar a gaban kotu saboda zarginsu da hannu a rikicin Kasuwar Magani da ke karamar Hukumar Kajuru da ke jihar a makon jiya. Rikicin wanda ya yi sanadin rasuwar mutum 12 ya janyo hasarar dukiya mai yawa. Kakakin Gwamnan Jihar, Mista Samuel Aruwan ne ya sanar da […]
Akalla mutum 65 ne Gwamnatin Jihar Kaduna ta gurfanar a gaban kotu saboda zarginsu da hannu a rikicin Kasuwar Magani da ke karamar Hukumar Kajuru da ke jihar a makon jiya.
Rikicin wanda ya yi sanadin rasuwar mutum 12 ya janyo hasarar dukiya mai yawa. Kakakin Gwamnan Jihar, Mista Samuel Aruwan ne ya sanar da haka a ganawarsa da manema labarai, inda ya ce an gufarnar da mutanen ne a gaban kotun Majistare da ke Titin Daura, Kaduna a ranar Juma’a da ta gabata.
A cewarsa, ana zarginsu ne da ta da hargitsin da ya yi sanadin rasa rayuka da dukiyoyi da yin taro ba bisa ka’ida ba, tare da mallakar makamai. Ya ce gwamnatin jihar ba za ta kame hannu tana kallon wadansu tsirari suna ta da hankalin jama’a ba.
“Gwamnati za ta tabbatar da cewa doka ta yi aikinta a kan duk wanda aka samu da hannu wajen ta da rikicin. Kuma babu sani babu sabo a kan duk wanda aka kama. Dokar kasa ta bai wa kowa damar yin addinin da ya ga dama ba tare da tsangwama ba, saboda haka babu wanda ya isa ya tilasta wani yin addini ko imani da abin da bai yarda da shi ba.
“Wadannan mutum 65, za a tabbatar da doka ta yi aiki a kansu muddin kotu ta same su da hannu a wajen ta da wannan fitina saboda ya zama darasi ga sauran mutane,” inji shi.
Ya kuma yi kira ga al’ummar jihar su yi watsi da duk masu ingiza su domin su ta da rikicin addini ko na kabilanci. Ya kuma tabbatar wa al’umma cewa gwamnati tana iya kokarinta wajen ganin ta kare rayuka da dukiyoyinsu.
“Yanzu haka akwai jami’an tsaro a Kasuwar Magani da sauran garuruwan da ke kusa domin tabbatar da cewa babu wani rikici da ya sake tashi a yankin. Tuni kura ta lafa kuma jama’a na ci gaba da gudanar da harkokinsu,” inji shi.
Bayanai sun nuna cewa babban wanda ake zargi da haddasa rikicin mai suna Zidane, an ce ya gudu ba a san inda yake ba amma dai ana ci gaba da nemansa.