Rikicin kula da cunkoson hanya ya kunno kai tsakanin Gwamnatin Legas da ta tarayya

Ga dukkan alamu rikicin da ya kunno kai tsakanin jami’an lura da cunkoson ababen hawa a Jihar Legas da sabon kwamitin da gwamnatin tarraya ta kafa don lura da cunkoson hanyoyin mota a jihar ya dauki sabon salo, inda gwamnan Jihar Legas Babatunde Raji Fashola, ya bukaci masu abubuwan hawa a jihar su bijire wa […]

Rikicin kula da cunkoson hanya ya kunno kai tsakanin Gwamnatin Legas da ta tarayya
Rikicin kula da cunkoson hanya ya kunno kai tsakanin Gwamnatin Legas da ta tarayya

Ga dukkan alamu rikicin da ya kunno kai tsakanin jami’an lura da cunkoson ababen hawa a Jihar Legas da sabon kwamitin da gwamnatin tarraya ta kafa don lura da cunkoson hanyoyin mota a jihar ya dauki sabon salo, inda gwamnan Jihar Legas Babatunde Raji Fashola, ya bukaci masu abubuwan hawa a jihar su bijire wa jami’an da gwamnatin tarraya ta baza a kan hanyoyin jihar.

Gwamnan ya yi furucin ne a lokacin da yake jawabi a bikin kungiyar masu sanya kayan sarki a kwalejin ’yan sanda da ke Ikeja a makon da muke ciki.
Furucin na Fashola ya zo bayan da jami’an kwamitin lura da hanyoyi da gwamnatin tarraya ta kafa da jami’an kula da cubkoson ababen hawa na jihar suka ba hammata iska a ranar Litinin din da ta gabata a kan babbar hanyan Legas zuwa Ibadan inda wasu da dama suka jikkata daga bangarorin biyu.
Fashola ya bayyana cewa kwamitin da gwamnatin tarayya ta kafa wadanda jami’an hukumar tattala farashin mai fetur ne na SURE-P ba su da ’yancin lura da cunkoson hanyoyin jihar.
Ya bayyana cewa gwamnatin tarrayya ta kafa kwamitin ba bisa ka’ida ba watannin kadan da suka gabata don ta yi amfani da su wajen zaben shekarar 2015 a jihar.
A cewarsa kamata ya yi kudin da aka samu daga rarar man fetur aka sanya su cikin hukumar SURE-P a gyara hanyoyin da suka lalace a jihar musamman hanyar Oshodi-Appa. Shi kuwa kwadinetan kwamitin na gwamnatin tarrayya da ke lura da cunkoson hanyoyi a jihar Legas, Alhaji Abdulrazak Rafiu ya yi watsi da zarge-zargen da gwamna Fashola ya yi.
Ya ce jami’an kwamitin suna da ’yancin su yi aiki a kan hanyoyin gwamnatin tarayya da ke jihar.
Sai dai ya zargi gwamnatin jihar da sanya siyasa a cikin lamarin a maimakon ta fuskanci kalubalen da ke gabanta a jihar.