Rikicin kwacen waya ya lakume rayuka uku

Mutum uku sun rasu wasu da dama sun jikkata a rikici kan kwacen waya.

Rikicin kwacen waya ya lakume rayuka uku

Mutum uku sun sheka lahira wasu da dama sun samu rauni bayan rikici ya barke kan kwacen waya, a cewar shaidu.

Mazauna sun shiga halin dar-dar a garin Falele na Karamar Hukumar Lokoja ta Jihar Kogi, bayan rikicin da ya biyo bayan kwacen wayan ya kai ga kashe-kashe.

Ganau sun ce lamarin ya faru ne bayan wasu da suka kwace wayar hannun wani mutun sun tsere zuwa wani kanti domin su boye.

Mutanen da suka biyo su sun yi zaton mai kantin na daga cikin barayin, sai suka kama shi da duka har suka kashe shi, alhali masu kwacen sun riga sun tsere.

Bayan haka ne ’yan uwan mai kantin suka gano daya daga cikin masu hannu a kisan, su ma suka far masa da duka, har suka kashe shi, suka kuma kona gawarsa.

Mutane da dama da suka samu rauni a yamutsin kuma an garzaya da su zuwa asibiti.

Kakakin ’yan sanda a Jihar Kogi, DSP Williams Aya, ya tabbatar da faruwar lamarin, amma ya ce gawarwaki biyu suka samu.

Ya bayyana cewa bayan daya daga cikin mutanen ya daba wa mai kantin wuka ya mutu, sai dangin mamacin suka dauki fansa ta hanyar kashe wancan din.

DSP Aya ya kara da cewa an kama wasu mutum biyu bisa zargin ’yan kungiyar asiri ta Aro Barger ne da kuma hannu a kisan.

Ya ce an fara bincike kafin a gurfanar da su a kotu kan lamarin da ya faru ranar Litinin da safe.

Amurka za ta dawo wa Najeriya N80bn da ta ƙwato daga Diezani

Yadda gwamnati ta yi sulhu da ’yan bindigar Kaduna

‘Da kuɗin yankan farce na je Hajji’

Zambar Intanet: EFCC ta kama ’yan China 4 da wasu 101 a Abuja