Rikicin Kwankwasiyya da Gandujiyya: An cafke ‘ya’yan kwamishina guda biyu

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kano, karkashin Kwamishina Rabiu Yusuf ta ce ta samu nasarar cafke wasu matasa uku bisa zargin su da  tayar da yamutsin da ya raunata mutane da dama. Matasan da ake zargi da tayar da tarzomar sun hada da ‘ya’yan Kwamishinan Ayyuka na Musamamn a jihar, Hon. Abdullahi Abbas Sanusi, wato Abbas […]

Rikicin Kwankwasiyya da Gandujiyya: An cafke ‘ya’yan kwamishina guda biyu

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kano, karkashin Kwamishina Rabiu Yusuf ta ce ta samu nasarar cafke wasu matasa uku bisa zargin su da  tayar da yamutsin da ya raunata mutane da dama. Matasan da ake zargi da tayar da tarzomar sun hada da ‘ya’yan Kwamishinan Ayyuka na Musamamn a jihar, Hon. Abdullahi Abbas Sanusi, wato Abbas Abdullahi Abbas da Sani Abdullahi Abbas, sai kuma dan aikin gidan kwamishinan, mai suna Shawuya.

Rahotanni sun bayyana cewa a ranar Lahadin da ta gabata ne aka samu yamutsi a tsakanin matasan Gandujiyya da Kwankwasiyya a yayin gudanar da wani daurin aure a unguwar Chiranci da ke karamar Hukumar Gwale.

Daga cikin wadanda suka samu raunukan har da ‘yan uwan kwamishinan ayyuka na musamamn din, Walid Abbas Sanusi wanda yake da alaka da Kwankwasiyya, inda ya samu rauni a kansa a lokacin wananan hargitsi, kuma ya yi wa Aminiya karin haske, yana mai cewa su dai ba su san hawa ba, ballantana sauka sai suka ji an rufe mu da sara da suka da kuma jifa. 

“Muna wurin daurin aure ba mu san abin da ke faruwa ba sai kawai ji muka yi an rufe mu da sara da suka ko ta ina, sanan ana yi mana ihu cewa ba sa yi. Da na duba sai na ga a cikinsu akwai ‘yan’uwana na jini wato ‘ya’yan yayana kwamishina Abdullahi Abbas”.

DSP Magaji Musa Majiya ya bayyaana cewa “kamar yadda jawabi ya zo mana ‘ya’ya ne suka kai wa kawunsu farmaki saboda bambancin siyasa, inda suka ji wa mutane uku ciwo. A lokacin da abin ya faru mun kai wadanan mutane uku asibiti, inda aka ba su kulawar gaggawa. A yanzu haka wadanda ake zargi suna hannunmu, kuma da zarar rundunar ta kamamla bincike za ta gurfanar da wadana ake zargi gaban kuliya.”

A wani ci gaban kuma, rundunar ta yi sammacin Kwamishinan Ayyuka na Musamman a jihar, Alhaji Abdullahi Abbas wanda ake zargi da yin kalaman tunzuri wadanda ake zargin su suka haifar da wancan yamutsin, domin yi wa rundunar bayani kan dalilansa na yin wadancan kalamai na tayar da zaune tsaye.

Aminiya ta samu ganin faifan bidiyon da Kwamishina Abdulalhi Abbas ya yi wadancan kalamai har ma ta rawaito shi yana cewa “ina son sanar wa ‘yan jam’iya cewa kararrawar siyasa ta busa a tsakaninmu da abokan adawarmu na cikin gida. Mun hadu da su a Minjibir ba su ji da dadi ba. Haka mun hadu da su a wajen fadar Sarkin Kano lokacin hawan;’ sallah, nan ma sun dandana kudarsu. Yanzu da shugabansu zai zo Kano za mu tare shi a Kwanar dangora ko Dakatsalle . 

“Kun san idan musulmi ya kare aikin Hajji abu na karshe shi ne jifan Shaidan, don haka ku jira wata rana da za a kira ku a umarce ku da ku jefe shaidanin siyasar Kano. Ba mu tsoron kowa, za mu iya bin shi da wannan yakin har dakinsa. A karshe ‘yan uwana za mu yi aiki sosai yadda za mu karya Kwankwaso kamar yadda kuka sani dama can tsoronmu yake yi.”

Haka kuma Aminiya ta rawaito cewa bayan kwamishinan ya amsa kiran rundunar ‘yan sanda tare da bayar da jawabi, rundunar ta bayar da belinsa, inda ta ce kafin ya tafi ta umarce shi da ya kawo hujjojinsa na kare kai. Har ila yau rundunar ta jaddada matsayinta na yi wa al’umma adalci ta hanyar zartar da hukunci akan kowa, ba tare da yin la’akari da matsayin mai laifi ba.