Yadda rikicin limanci tsakanin Izala da Darika ya jikkata mutum 8
Rikicin limanci a Babban Masalacin Juma’a na garin Okene a tsakanin ‘ya’yan kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah wa Ikamatis Sunnah da na mabiya darikar Tijjaniya ya jikkata mutum takwas a jihar Kogi. Wata majiya ta shaida wa Aminiya cewa tun bayan rasuwar babban Limamin masallacin, Shaikh Musa Galadima, a shakarar 2019 ake samun tashin tashina a […]
Rikicin limanci a Babban Masalacin Juma’a na garin Okene a tsakanin ‘ya’yan kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah wa Ikamatis Sunnah da na mabiya darikar Tijjaniya ya jikkata mutum takwas a jihar Kogi.
Wata majiya ta shaida wa Aminiya cewa tun bayan rasuwar babban Limamin masallacin, Shaikh Musa Galadima, a shakarar 2019 ake samun tashin tashina a tsakanin bangarorin biyu a kan wanda zai gaji marigayin.
Wasu da suka shaida faruwar lamarin sun fada wa Aminiya cewa rikicin, wanda ya faru ranar Juma’a, ba shi ne irinsa na farko ba a masallacin, domin a baya ma an taba kwata irin hakan, inda ko wanne bangare ke fatan jan ragamar shugabanci a masallacin.
- Dakatar da tarukan addini: ‘Da malamai muka yi shawara’
- Ramadan: Malamai sun bukaci a tallafawa mabukata
Suka ce lamarin ya auku ne a daidai lokacin da ake shirin tayar da sallar Juma’a, bayan da Ustaz Bello Hussaini na kungiyar Izala ya ambaci limamin da ke jan salla a masallacin da sunan liman mai rikon kwarya.
Takaddama ta barke
Wannan kalma da Ustaz Bello Husaini ya siffanta Shaikh Salihu Abere da ita ba ta yi wa ‘yan darikar Tijjaniya a masallacin dadi ba, inda suka bukaci da ya nemi afuwa.
Wannan takaddama ce dai ta kai ga aka bai wa hammata iska a tsakanin mabiya kungiyoyin biyu, aka raunata mutum takwas.
Majiyar ta ce jama’ar da suka taru a masallacin domin yin sallar juma’a sun yi ta kan su.
Wani mazaunin yankin mai suna Abdusalam Muhammad da ya yi wa ‘yan jarida karin haske, ya bayyana lamarin da abin takaici.
Abin da ya faru
“A kan idona rikicin ya faru, a lokacin da babban limamin masallacin ya shigo domin ya jagoranci sallar juma’a.
“Abin da ya bai wa jama’a da dama a masallacin mamaki shi ne, ganin yadda Ustaz Bello Hussaini, wanda a lokacin yake gabatar da jawabi kafin isowar limamin, bayan ya dakata da jawabin da yake yi sai ya sanar da cewa limamin rikon kwarya ya iso a maimakon ya kira shi da babban limamin masallacin.
“Wannan shi ne musabbabin rikicin wanda aka shafe awa guda ana gwabzawa kafin daga bisani ‘yan sanda su shiga tsakani”, inji shi.
‘Ban yi kuskure ba…’
A nasa bangaren, Ustaz Bello Hussaini, wanda ya furta kalaman da suka janyo rikicin, ya ce babu wani aibu a cikin abin da ya fada na kiran Shaikh Salihu Abere da sunan mai rikon kwarya, domin ba a kai ga nada limami ratibi a masallacin ba.
Ya ce bayan rasuwar babban limamin masallacin, Shaikh Salihu Abere, wanda shi ne Na’ibin Liman, ya ci gaba da jagorantar sallar Juma’a kamar yadda gwamnan jihar Yahaya Bello ya ba shi umarni a matsayin mai rikon kwarya.
Ya kara da cewa Momoh Jimoh ne ya tunkare shi bayan da ya ambaci Shaikh Abere a matsayin mai rikon kwarya.
Gwamna ya sa baki
“Da ya tunkare ni sai rikicin ya barke; sun yi wa ‘yan kungiyarmu su hudu mummunan rauni, an kuma yi wawaso a rumfunan su na kasuwa.
“Ba laifi ba ne ambatar da na yi wa Shaikh Abere da mai rikon kwarya, domin an ba shi umarnin yin limanci ne a matsayin mai rikon kwarya, saboda ba a kai ga nada limami ratibi a masallacin ba”, inji shi.
Gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello ya gayyaci manyan sarakunan gargajiyar yankin zuwa Lokoja, babban birnin jihar, domin samar da matsaya tare da warware matsalar.