Rikicin limanci ya jawo dakatar da Sallar Juma’a a wani masallaci
Rikici a kan ikon mallakar masallaci a tsakanin kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’a Wa Ikamatis Sunnah (JIBWIS) ta karamar Hukumar Suleja a Jihar Neja da wani limamin masallaci a Kaduna Road, ya tilasta dakatar da Sallar Juma’a a masallacin. Lamarin ya faru ne a ranar Juma’ar da ta gabata, inda bayan zaman jira a karshe aka […]
Rikici a kan ikon mallakar masallaci a tsakanin kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’a Wa Ikamatis Sunnah (JIBWIS) ta karamar Hukumar Suleja a Jihar Neja da wani limamin masallaci a Kaduna Road, ya tilasta dakatar da Sallar Juma’a a masallacin.
Lamarin ya faru ne a ranar Juma’ar da ta gabata, inda bayan zaman jira a karshe aka bukaci mamu su tafi wasu masallatai su yi Sallah don kauce wa tashin fitina.
Da yake yi wa Aminiya bayani a kan lamarin, Limamin Masallacin Malam Usman Muhammad Rabi’u, ya ce masallacin wanda aka gina a 1998, kuma yake limancinsa tun lokacin, kungiyar Izala ce ta nemi ta dakatar da shi daga limanci tare da maye gurbinsa da wani sakamakon rashin halartar zama da sauran tarurrukansu da su ke gabatarwa.
Limamin ya ce akidarsa da ta sauran wadanda ke mara masa baya daya ce da ta Izala wajen yaki da bidi’a da kafa Sunnah, sai dai ya ce shi ba dan Izala ba ne kuma ba Izala ba ce ta gina masallacin, su ne a tsakaninsu suka yi kai-komo wajen gina masallacin, saboda haka kungiyar ba ta da ikon dakatar da shi daga limanci.
Sai dai shugaban kungiyar Izala a karamar Hukumar Suleja wanda kuma shi ne mataimakin shugabanta a Jihar Neja, Alhaji Inda Aliyu Abdullahi ya shaida wa wakilinmu cewa masallacin na Kaduna Road mallakin kungiyar ne kuma kungiyar ce ta nada liman tun a wani masallaci karami ida suka faro Sallah kafin a dawo masallacin na yanzu. Ya ce kungiyar Izala ce ta nemi wurin kuma ita aka danka wa wurin, sai dai ta bar al’amarin ginin a hanun limamin kasancewar shi ne wakilinta a yankin. “Jama’a da dama sun tuntube mu a kan niyyarsu ta taimakawa a lokacin aikin masallacin, kuma a duk lokacin da suka zo mukan tura su ne zuwa wurinsa,” inji shi.
Game da dalilin dakatar da limamin kuwa, Alhaji Inda Aliyu cewa ya yi, “Kusan shekara bakwai ke nan limamin ya janye daga halartar zama da sauran tarurrukan kungiyar, amma kasancewar ana tare da shi a akida guda an ci gaba da tafiya a hakan ba tare da an dakatar da shi ba. Sai dai matakan da ya fara dauka na raba jama’armu da wajen ciki har da korar ’yan agajinmu tare da kawo wasu daban, ya sa a wannan makon muka dakatar da shi tare da nada Malam Alhasan Babban-Tunga ya maye gurbinsa.”
Ya ce don magance aukuwar fitina ya sa suka sanar da babban ofishin ’yan sanda na yankin da ke garin Sabo-Wuse, kuma sakamakon haka an gayyace su ofishin don bin bahasin bangarorin biyu.
bangarorin biyu sun tabbatar wa Aminiya zuwansu ofishin ’yan sandan, sai dai a karshe DPO ya tura su ofishin Kwamandan ’Yan sandan yanki da ke Suleja, kasancewar maganar ta yi zafi.
Da wakilinmu ya tuntubi Kwamandan, ACP Abubakar Yahaya ya tabbatar da ganawar tasu, sai dai ya ce ya sanar da su cewa al’amura irin wadannan magance su zai fi dacewa ne a wurin malamai ko masarauta ba ofishinsu ba.
Daga baya bangarorin biyu sun dawo masallacin, kuma bangaren Izala na shirin gabatar da Sallah ne kamar yadda Aminiya ta samu labari, sai wasu dagatai biyu daga yankin suka ba da sanarwar cewa, Mai martaba Sarkin Suleja Malam Auwal Ibrahim ya bada umarnin kada a gabatar da Sallah a masallacin idan ba tsohon limamin ne zai jagoranta ba. Hakan ya sa aka bukaci jama’a da suke zamnan jira su tafi wasu masallatan.