Rikicin ma’aurata: Darasi daga su Maryam Sanda da mijinta

Hukuncin kisa ta hanyar rataya da kotu ta yi wa Maryam Sanda, sakamakon samunta da laifin kashe mijinta Bilyaminu Bello a shekara biyu da suka gabata, abin ya daga min hankali. A lokuta da dama, a kan yi auren soyayya, a sha biki, a kashe kudi, sannan jim kadan bayan aure sai a bige da […]

Rikicin ma’aurata: Darasi daga su Maryam Sanda da mijinta

Hukuncin kisa ta hanyar rataya da kotu ta yi wa Maryam Sanda, sakamakon samunta da laifin kashe mijinta Bilyaminu Bello a shekara biyu da suka gabata, abin ya daga min hankali.

A lokuta da dama, a kan yi auren soyayya, a sha biki, a kashe kudi, sannan jim kadan bayan aure sai a bige da rikici a gidajen auren.

Wani lokacin nakan rasa yadda lamarin yake. Nakan tambayi kaina, shin wannan ko ba auren soyayya suka yi ba? Ko dai an tilasta su ne? Ko kuma dai na ciki na ciki ne, amma suka nuna wa duniya soyayya?

Kullum zaman aure dole sai da hakuri, domin Hausawa na cewa hakori da harshe suna samun matsala. Amma yadda ake ci gaba da samun rikici a tsakanin ma’aurata, abin akwai takaici.

Na san wata da suka yi auren soyayya da mijinta, soyayyar gani a fada. Muka sha biki abin ba a cewa komai. Kowa na murna, daga iyaye, abokai da ’yan uwa da abokan arziki zuwa mu kawaye. Amma cikin wata biyar auren ya mutu. Mece ce matsalar? Suna rikici a gidansu, mijin na cewa laifin matar ce, matar na cewa laifin mijin ne. Laifin me yake miki? Amsar a kullum bai wuce kananan abubuwa da ba su kai sun kawo ba. Laifin me take maka, ya kai miji? Shi ma kullum babu gamsasshiyar amsa. Amma kullum cikin rigima. Har ta kai iyaye sun fara shiga, yana zagin iyayenta, tana zagin nasa iyayen. Haka dai aka raba auren, sannan bayan wani dan lokaci sai suka fara bibiyar juna, wai tana son mijnta, shi ma yana son matarsa; abin kamar ka yi dariya, amma ba dama.

Don haka ne nake so a dauki darasi daga biki da zaman aure da kisan Bilyaminu da hukuncin kotu a kan Maryam.

Akwai bidiyo a manhajar Youtube da ke nuna bikin Maryam Sanda da mijinta, marigayi Bilyaminu, inda aka gwangwaje, aka sha biki cikin murna da jin dadi. Kowa na sam barka. Daga kallon fuskokinsu a bidiyon, babu alamar takura, ko tilastawa. A fuskokinsu babu komai sai murna da nishadi.

Amma kuma me ya sa rikici har ya kai ga kisa? Akwai kananan bayanai da suka fito daga bangarorin biyu, kowa na zargin kowa, duk da cewa Allah ne kadai Ya san asalin abin da ya faru, amma duk maganganun da bangarorin biyu suka yi, a nawa tunanin bai kai ga fada ba, balle har ya kai ga kisa.

Babban darasin shi ne, yanzu an yanke wa Maryam hukuncin kisa ta hanyar rataya. Ana sa ran za ta daukaka kara har zuwa Kotun Koli, wanda ba mamaki a dauki shekara 1 zuwa 2. Abi mamaki shi ne yadda wadansu daga cikin maza suke murna, kamar an rama musu, wadansu daga cikin mata kuma suna bakin ciki.

Me ya sa aka samu sabani? Domin duniyar aka sa gaba kawai. Ko ma me ya faru, Kotun Koli ce za ta tabbatar da hukuncin ko akasin haka, sannan kuma yanzu haka akwai fiye da mutum 2000 da aka yanke wa hukuncin kisa, amma ba a kashe su ba.

Amma lallai ya kamata iyaye su dauki darasi mai yawa; dole a tabbatar an yi bincike kafin a daura aure, ta hanyar tabbatar da tarbiyya da tarihin gidan da za a ba aure (ko za a aura). Sannan iyaye su lura da kawaye da abokan ma’auratan.

Dole a koya wa mutane cewa aure ibada ne, dole za a ji dadi, kuma za a ji zafi. Idan an samu dadi a yi murna a gode Allah, idan an samu zafi a yi hakuri, shi ma a gode wa Allah.

Idan aka sanya Allah a gaba, komai zai yi sauki kuma za a samu nasara.

Allah Ya amintar da mu a gidajenmu.

Daga Nusaiba S. Muhammed

Barikin NDA, Kaduna 07038964363