Rikicin ma’aurata: Yadda rayuka ke salwanta kan karamin sabani
A ranar Litinin da ta gaba ce wata Babbar Kotun Birnin Tarayya, Abuja ta yanke wa Maryam Sanda hukuncin kisa ta hanyar rataya bisa samunta da laifin kashe mijinta, marigayi Bilyaminu Bello. Shekara biyu ke nan da aukuwar lamarin, inda aka samu mabambanta bayanai kan musabbabin rikicin nasu da ya yi sanadiyar ta fusata ta kashe […]
A ranar Litinin da ta gaba ce wata Babbar Kotun Birnin Tarayya, Abuja ta yanke wa Maryam Sanda hukuncin kisa ta hanyar rataya bisa samunta da laifin kashe mijinta, marigayi Bilyaminu Bello.
Shekara biyu ke nan da aukuwar lamarin, inda aka samu mabambanta bayanai kan musabbabin rikicin nasu da ya yi sanadiyar ta fusata ta kashe shi, kuma kotun ta yanke mata wannan hukunci bayan dogon lokaci.
Yayin yanke hukunci kan shari’ar Alkalin Kotun Mai shari’a Yusuf Halilu, ya ce hukuncin wanda ya yi kisa shi ne shi ma a kashe shi, wanda hakan ya sa ya yanke wa Maryam Sanda wannan hukunci.
Yanzu haka Maryam Sanda na gidan gyaran hali na Suleja inda wasta majiya ta ce za ta daukaka kara zuwa kotun gaba.
A lokacin da aka yanke hukuncin, wakilin Aminiya ya jiyo Maryam Sanda tana cewa, “Inna lillahi wa inna Ilaihir raji’una, Ya Allah…” inda take ta addu’o’i tare da kiran sunan Allah.
Ana cikin wannan jimamin ne kuma, kwatsam sai aka samu labarin wata mata mai shekara 19 ta kashe mijinta a Malumfashi a Jihar Katsina.
Kashe-kashe a gidajen ma’aurata na ta’azzara
Bayan yanke hukunci ga Maryam Sanda, an sake samun irin wannan lamari guda biyu, daya a Jihar Katsina, inda wata mata ta kashe mijinta, daya kuma a Jihar Abiya, inda wani magidanci ya kashe matarsa, jama’a kuma suka kone shi. Wannan ne ya sa Aminiya ta tattaro bayanan yadda lamarin kisa a tsakanin ma’aurata ke ta’azzara.
A binciken da Aminiya ta gudanar, ta gano cewa baya ga kisan mijinta Bilyaminu da Maryam Sanda ta yi a shekarar 2017, akalla zuwa yanzu mutum 56 ne suka aka hallaka a rikicin ma’aurata, inda aka kashe mata 39 da maza 17.
Daga cikin mutum 56 da suka rasu, lamarin ya fi aukuwa ne a Kudancin Najeriya, inda aka kashe mutum 36, sai 20 a Arewa.
Haka kuma Aminiya ta gano cewa Jihar Legas ce ta fi yawan hallaka abokan zama a tsakanin ma’aurata da mutum 12, sai Jihar Neja da ke kan gaba a Arewa da mutu 6.
Jihohin Anambra da Neja ne suke biye da Jihar Legas da mutum shida-shida, sai Jihar Ogun mai mutum 5, sai Kano da aka kashe mutum 4 da kuma Katsina da Ribas da aka kashe mutum uku-uku.
Aminiya ta kuma gano cewa a shekarar 2017 da lamarin Maryam Sanda ya faru, an sake samun aukuwar lamarin sau biyu, a jihohin Katsina, inda wata mata mai suna Dausiyya Abdulmumini mai shekara 15 ta kashe mijinta mai suna Saminu Usman mai shekara 27 a kauyen Danmayaki a Jihar Katsina a ranar 17 ga watan Disamban 2017 saboda mijin ya yi hadari ya ji rauni sosai wanda hakan ya sa ta kashe shi. Sai wani mai suna Ebiretus da ya kashe matarsa mai suna Fidelia a watan Disamban 2017 a kauyen Uli da ke Ihiala a Jihar Anambra saboda ba ta dafa masa abincin Kirsimeti ba.
Sannan a shekarar 2018, an samu aukuwar lamarin sau 20, a shekarar 2019 aka samu aukuwar haka sau 30, sai bana, inda zuwa yanzu aka samu sau 4.
Haka kuma binciken Aminiya, ya gano cewa yawancin rikicin yakan faro ne daga abu karami, kamar kin dafa abinci da kin yi wanki da musayar yawu. Sa a wasu lokuta da zargi ke shiga, wanda kan yi sanadiyar fara rikici.
Akwai ma wanda ya kashe matar saboda ba ta shayar da jaririn da ta haifa masa ba da sauransu.
Akwai wani mai suna Caleb Danjuma da ya kashe matarsa Precious a kauyen Washo da ke Jihar Nasarawa saboda ta ki wanke masa kayan sawa.
Haka kuma akwai wani mai suna Ibasiki da ya kashe matarsa a garin Oshodi da ke Jihar Legas saboda ba ta dafa masa abinci ba.
Kashe Bilyaminu zuwa yanke hukunci
Kimanin wata 26 bayan kashe mijinta, a ranar Litinin da ta gabata kotu ta yanke wa Maryam Sanda hukuncin kisa ta hanyar rataya.
A ranar 24 ga watan Nuwamba ne ’yan sanda suka kai kararta bisa zargin hannu a mutuwar mijinta Bilyaminu Bello, da ga tsohon Shugaban Jam’iyyar PDP ta Kasa, Alhaji Bello Halliru Muhammad.
Sannan daga baya aka sake tuhumarta tare da mahaifiyarta, Maimuna Aliyu da dan uwanta Aliyu Sanda da ma’aikaciyar gidansu, Sadiya Umar da laifin taimaka mata wajen wanke jinin da ya zuba da batar da abubuwan da za su iya zama shaida a gaban kotu.
Daga baya kotu ta sallami mutum ukun tare da wanke su, sai ta bar Maryam ita kadai.
A ranar 24 ga Nuwamba, shekarar 2014 ce kotu ta tura Maryam kurkuku, bayan ta ki amincewa da bukatar belinta. Sai a watan Maris na 2018 ta samu beli bisa la’akari da batun lafiyarta.
A 19 ga Afrilun 2018, wani shaida ya bayyana yadda Maryam yi ta kokarin daba wa mijinta Bilyaminu wuka, inda suka shiga tsakani, sannan daga baya suka ji ya rasu.
A 27 ga Fabrailun 2019, kotu ta sanya ranar sauraron bayanai na karshe.
A 26 ga Maris na 2019, kotu ta sanya ranar sauraron bukatar wanda ake zargi wato Maryam cewa ba ta da laifi.
A ranar 4 ga Afrilun 2019, kotu ta ce Maryam na da lafin da za ta kare kanta a kai.
A ranar 8 ga watan Oktoba, Maryam ta fara gabatar da bayanai da shaidun kare kanta. Sai a ranar 16 ga Disamban bara kotu ta sanya ranar yanke hukunci, kuma a ranar 27 ga Janairun bana, kotun ta yanke mata hukuncin kisa ta ranyar rataya.
Yadda aka yanke hukunci ga Maryam Sanda
Da yake yanke hukunci a ranar Litinin, Mai shari’a Yusuf Halilu ya ce maganar cewa marigayin ya mutu ne bayan ya fadi a kan kwalbar Shisha rufa-rufa ce kawai, inda ya ce tunda ta tabbatar da cewa ita ce ta gan shi na karshe kafin rasuwarsa, “Kawai an fasa kwalbar Shishar ce domin a yi rufa-rufa. Wannan ba zai dauki tunani ba. An fasa kwabar ce bayan rasuwarsa. Na gamsu cewa wanda ake zargin ta daba wa marigayin wuka ne. Akwai takaici a lamarin ganin cewa wanda aka kashe din mijin wadda ake kara haihuwa ta shiga tsakaninsu. Wannan ba abin takaici ba ne kawai, har da zalunci,” inji shi.
Ya kara da cewa, “Duk da cewa ina tausaya wa wadda ake zargi a matsayinta na uwa mai kananan yara biyu, wanda ta kashe ubansu, ba zan iya taimakon wanda ake zargin ba wajen guje wa shari’a. Na gamsu sosai cewa Maryam Sanda ce ta aikata laifin kashe mijinta Bilyaminu, don haka kotu ta tabbatar miki da laifin kisa.”
Abin da ya faru a kotun
Bayan alkalin ya tabbatar da laifin, kafin yanke hukuncin sai Maryam ta fice a guje daga wajen da ake tsare wadanda ake tuhuma, inda wadansu daga cikin ’yan uwanta suka yi kokari suka mayar da ita.
Nan ta fara kuka tana cewa, “Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un. Ya Allah na ta yin azumi da salloli. Me ya sa?”
Haka ta ci gaba da addu’o’i, sannan wadansu matan suka rika kuka, har daya daga cikinsu ta nufi inda Maryan take tana kuka, kafin jami’an tsaro su mayar da ita.
Da yake yanke hukuncin, Mai shari’a Yusuf ya ce yi wa Bilyaminu da kasa adalci ya fi komai, Maryam Sanda za ta girbi abin ta shuka ne; wato jini da jini.
“Kuma yadda mata ke kashe mazansu ko yadda mazan ke kashe mata abin na kara ta’azzar yanzu a cikin al’umma. Don haka na yanke wa Maryam Sanda hukuncin kisa ta hanyar ratayewa har sai ta mutu. Na yi haka ne domin in tabbatar da cewa lallai ya kamata a yi adalci a wannan shari’a da kuma tabbacin cewa ruhin marigayin na nan yana neman adalci, kuma ina tsammanin ruhin na zuwa kotun nan domin jin yadda za ta kaya, wanda hakan nake tunanin zai sa ya koma kabarinsa ya kwanta cikin aminci,” inji shi.