Rikicin makiyaya da manoma babban kalubale ne

Hakika rikicin da ake jinginawa ga Fulani makiyaya da manoma da ke faruwa a wasu sassan kasar nan, musamman Arewa ta Tsakiya da Arewa maso Yamma babban kalubale ne ga kasar nan da jama’arta. Abu ne sananne cewa bisa dabi’ar dan Adam za a rika samun sabani a tsakanin makiyaya da manoma, tunda masu iya […]

Rikicin makiyaya da manoma babban kalubale ne

Hakika rikicin da ake jinginawa ga Fulani makiyaya da manoma da ke faruwa a wasu sassan kasar nan, musamman Arewa ta Tsakiya da Arewa maso Yamma babban kalubale ne ga kasar nan da jama’arta.

Abu ne sananne cewa bisa dabi’ar dan Adam za a rika samun sabani a tsakanin makiyaya da manoma, tunda masu iya magana sun ce, harshe da akori ma suna sabawa.

To amma babban abin takaicin shi ne yadda ake kokarin cusa siyasa ga lamarin. Bai kamata a sanya siyasa a abin da ya shafi rayuwa da zaman lafiyar jama’a ba, wannan yana iya kawo cikas da zama barazana a kokarin da duk wani ko wadansu rukunin jama’a za su yi domin magance matsalar.

Duk mai lura da yadda ake tafiyar da rikicin makiyaya da manoma a jihohin Benuwai da Taraba zai fahimci cewa an koma siyasa da kamfe ne kawai da batun maimakon nemo hanyar magance shi.

Ya kamata gwamnonin wadannan jihohi su tuno da abin da tsohon Shugaban kasa Janar Yakubu Gowon ya taba fad a shekara 2014 cewa ba Fulani makiyaya ne suke kai hare-haren da ake zargi ba, a’a wadansu ’yan ta’adda ne da aka horar da su suke yin wannan aika-aika. a duba Janar Gowon ya taba fadi a garin Abakaliki cewa ya kamata ’yan Najeriya su zargi wadansu miyagu da suke shigar Fulani suna kisa da barnata dukiya. Abin takaici ne a nan Arewa a samun wadansu shugabanni na siyasa ko na addini su rika bayyana wannan ta’asa da rikicin Fulani makiyaya da manoma ko rikici na addini. Su lura wadannan ’yan ta’adda suna yin irin wannan aika-aika a jihohin Kaduna da Zamfara da wasu sassa na jihohin Katsina da Bauchi da Kano su kuma wadanda suke aikata wannan danyen aiki ba ruwansu da Bahaushe ko Bafulatani, Musulmi ko wanda ba Musulmi ba, kowa suna kashe shi ko su kwace masa dukiya.

Don haka matukar ’yan siyasa ba su daina amfani da wannan rikici da miyagu suke shiryawa suka tsaya tsakani da Allah suka fuskanci matsalar, to za a ci gaba da samun kashe-kashe da tashe-tashen hankula a wadannan jhohi da sauran sassan kasar nan.

Lokaci ya yi da za a daina amfani da wannan rikici don yi wa wannan gwamnati zagon kasa, a daidai lokacin da take kokarin ganin bayan kungiyar Boko Haram, wadda ta mayar da kasar nan tamkar mayanka a shekarun baya.

Ga gwamnonin jihohin Benuwai da Taraba, ya kamata su yi nazari cewa dokarsu ta hana kiwo da wadansu makiya jihohinsu da Arewa da kasar nan suka sanya suka kafa, da gangan aka cusa musu wannan ra’ayi domin a ba makiya jihohinsu da kasar nan damar da za su aiwatar da kashe-kashe a jihohin.

Kuma ya kamata Gwamnan Jihar Benuwai ya tuno da bayanan da hukumomin tsaro ciki har da Hukumar Tsaron kasa ta farin kaya (DSS) ta bayar inda ta zargi tsohon Gwamnan Jihar Gabriel Suswam da daukar nauyin wani dan ta’adda da ya addabi jihar a baya, ya ci gaba da ta’addanci a jihar domin ya hana Gwamnan na yanzu sakat.

A karshe muna yaba wa Gwamnan Jihar Filato Barista Simon Lalong kan yadda ya ki yarda a sake jefa jiharsa wannan matsala bayan ta yi fama da rikice-rikicen kabilanci na tsawon shekaru.

Muna fata gwamnonin jihohin Benuwai da Taraba, Samuel Ortom da Darius Ishaku  za su hanzarta janye wannan doka, ta nuna kiyayya ga Fulani makiyaya ta yadda za a samu zaman lafiya tare da kunyata masu fakewa da dokar suna kashe jama’ar da ba su san hawa ba, balle sauka a jihohinsu ba.

Su kuma mutanen da ake yi musu kallon dattawa irin su Janar T.Y.danjuma ya kamata su lura cewa zaman lafiya ya fi zama dan sarki, don haka su daina bari gubar kabilanci da kiyayya suna rudarsu suna ingiza jama’a a duk wani abu da zai kawo tashin hankali a tsakanin kabilu da mabiya addinai daban-daban na kasar nan.

Mun gaji da irin jinin da ake zubarwa a Arewa, a bar mu mu yi fama da talauci da kuncin rayuwar da suke addabarmu ba sai an kirkiro wani abu da zai dada jefa mu ga zubar da jinin juna ba.

Alhaji Gambo Abdullahi Bababa

Shi ne Shugaban kungiyar Masu Harhada Magungunan Gargajiya ta Jihar Bauchi, za a iya samunsa ta tarho: 08023622651 da 07032096837