Rikicin makiyaya da manoma: Hakkin gwamnati ne samar da wuraren kiwo ga Fulani – Sheikh dahiru Bauchi
Akwai wadansu gwamnoni da suka kafa dokar hana kiwo a jihohinsu hakan ya jawo an samu tashin hankali a jihohin Binuwai da Taraba, yaya Shehi ke kallon lamarin kuma ta yaya za a warware shi? Mulkin sama da kasa duka na Allah ne, Allah Ya ware wadansu mutane Ya ba su iko, wadansu su ne […]
Akwai wadansu gwamnoni da suka kafa dokar hana kiwo a jihohinsu hakan ya jawo an samu tashin hankali a jihohin Binuwai da Taraba, yaya Shehi ke kallon lamarin kuma ta yaya za a warware shi?
Mulkin sama da kasa duka na Allah ne, Allah Ya ware wadansu mutane Ya ba su iko, wadansu su ne shugabannin kasashe wadansu gwamnoni, wadansu shugabannin kananan hukumomi wadansu kuma masu gari. Amma duk da haka ba a son shugaba ko wani ya taka doka sai dai a yi adalci. Ni da nake maganar nan Bafulatani ne ta ko’ina amma ba ina magana a kan ni Bafulatani ba ne, ina magana ne a kan ilimin addini yadda ya ajiye rayuka. Kowa da yadda Allah Ya ajiye shi, saboda haka muke shawartar Gwamnatin Tarayya, ta yi wa masu dabbobin nan filayen kiwo wadanda ba za a taba ba ba za a sari wurin ba, a mai da shi gona ko a sari wurin a maida shi gida. A zamanin Sayyidina Umaru ya rushe gidaje ya kara Ka’aba saboda kara Ka’abar ya rushe gidaje, wadansu suka yi taurin kai suka ce ba za a rushe gidajensu a raba su da Harami ba. Sayyidina Umaru ya ce duk wanda ya yi taurin kai ku sayar da gidansa ku ba shi kudinsa ba Ka’aba ne ta je kofar gidansa ta zauna ba, shi ne ya zo filinta ya zauna. Kuma Sayyidina Usumanu a cikin cajin da mutane suka yi masa akwai cajin cewa ya kama muhallin mutane ya mai da shi wurin kiwo. Ya ce ba ni na fara ba wadanda suka riga ni ne suka fara, Sayyidina Umaru ne ya ware filaye ya ce na daji ne saboda kiwon dabbobin Zakka da sauran dabbobi, to saboda haka ni kuma a zamanina sai dabbobin suka yi yawa fiye da lokacin Sayyidina Umaru, to ya zama dole ke nan in kara filayen. Irin wadannan abubuwa duka ya kamata a dube su a yi adalci a yi gaskiya, a dubi kowa a ba shi hakkinsa gwargwado. Kada a rika take hakin mutane don nuna isa, kada a rika duba don bangare kaza ne ko don su kabila kaza ne ko addini kaza ne. Shi mai iko a kullum yana duban kasarsa da idon rahama ne gaba daya, kuma a rika lura a yi adalci. Wadansu mutane su dauki irin yunifom din wadansu mutane suna sawa su dauki makami suna kashe mutane a rika cewa Fulani ne, Fulani ne, wannan dole a duba a yi hukunci na gaskiya. Mun yi wannan bayani ne ko Gwamnatin Tarayya za ta samu yadda za ta warware wannan matsala. Kuma batun cewa wadansu ba za su ba da filayensu da suka gada iyaye da kannin ba wannan ba gaskiya ba ce, domin akwai lokacin da gwamnati take gina gidaje na siyasa wadansu suka ki kuma gwamnatin ta ce ko mutum ya ki za a gina gidan a filinsa. Saboda haka gwamnati ta nuna karfinta a kan adalci da bin kadin kowane mutum dan kasa. Su wadannan mutane ba za su zuba shanunsu a teku ba, kuma ba za su bar shanunsu ba kiwo ba, to yaya za a yi har a sa dokar kada a yi kiwo? Wannan ba zai yiwu ba, don haka muke jawo hankali cewa mu hada kai mu ’yan kasa kowa ya san hakkinsa, kada ya take hakkin wani, kuma kowa ya san inda doka ta ajiye shi kada ya dauki doka a hannu domin a samu zaman lafiya. Muna gaya wa Gwamnatin Tarayya ita ce take da hannu a kan kowane mutum a kowace jiha da karamar hukuma, kowane mai jama’a tana da hannu a kansa, cikin ikon da Allah Ya ba ta.
Wadansu na ganin wannan batu ya shafi bambancin addini, me za ka ce?
Fadan da ake yi ba na Kirista da Musulmi ba ne, na mutane ne masu son zuciya, tsakanin mu Musulmi da Kirista muna zaman lafiya, addininmu na Musulunci addinin zaman lafiya ne addininsu addinin tausayi ne, yaya za a yi mai addinin tausayi ya yi fada da mai addinin zama lafiya? In ka ga an yi haka to wani ya bar layin addininsa saboda haka, abu mai muni a cikin addinin bayan tsafi ba kamar kisan dan Adam, su daura aure da ake yi su idda su kulle duka don a kiyaye ran dan Adam ne, to ba abin da ya fi muni kamar kashe jama’ar Musulmi ko dan Adam a bayan tsafi. Kowa yana kan addininsa muna zaune lafiya saboda haka nake nanatawa mu dai a bangarenmu Musulmi ba ma gaba da Kiristoci ai ma muna yabonsu ne fiye da sauran ’yan uwansu wadanda ba Musulmi ba kamar yadda Allah Ya yabe su a cikin Alkur’ani. Allah Ya ce “A cikin jama’ar mutanen da ba Musulmi ba, babu mafiya muni da kiyayya kamar mushrikai wato masu tsafi da Yahudawa, kuma in kana neman mutumin da ba Musulmi ba ne amma yana jin tausayin Musulmi yana son Musulmi, babu kamar Kirista domin mutanen Annabi Isa (AS) Allah Ya yi musu zuciya mai sanyi saboda sun gaji Yahudawa masu taurin zuciya, sai Allah Ya kawo su su kuma suka zamo masu sanyin rai masu tausayi masu tausayawa. Saboda haka nake jawo hankalin kowane dan uwana Musulmi ya zauna lafiya da makwabcinsa Kirista, Kiristoci su ma su zauna lafiya da makwabtansu mu Musulmi. Amma irin abubuwan da suka faru a baya, inda wadansu mutane masu kudi wadanda ba Musulmi ba, suka sayi motoci aka yi musu fenti irin na soja aka sayi yunifom irin na soja, aka bai wa samari aka ce musu wai su ne sojojin Yesu, su je su yi ta kashe Musulmi ana cewa Boko Haram ne, irin wannan duk ya kamata a duba a yi gaskiya. Amma a sallama wasu jihohin Najeriya a hannun wadansu mutane a ce sai yadda suka yi kamar ba gwamnati wannan ya kamata a janye. Duk mutumin da ba zai bari a yi kiwo a jiharsa ba, to ya bar kujerar Gwamna ya koma can cikin Sahara inda ba mutane ba dabbobi ya yi gwamnansa a can. Amma duk wanda zai zauna a garin da yake da jama’a, jama’ar kuma suna da dukiya dole ya ba kowa hakkinsa,
Akwai wasu majalisun dokokin jihohi da suke yunkurin kafa dokokin hana bara, me Malam zai ce?
Wannan zalunci ne dalili kuwa in dai bara ta gaskiya ce ba ta jabu ba, domin akwai mutanen da su ba karatu suke yi ba, suka mai da kansu masu bara suna bara tare da almajirai, wannan bara ce ta jabu, ba a son irin wannan zai lalata kasa ya hana mutane yin aikin raya kasa. Amma irin bara ta neman ilimin Alkur’ani wannan an gada ne tun zamanin Annabi (SAW), duk wanda ka ji yana bude baki yana cewa babu bara a Musulunci to bai san Musuluncin bane, tunda Annabi (SAW), bakin da suka je wajensa suka kaura suka koma Madina su ake kiransu Almuhajirin, to daga nan aka samu sunan almajiri. Su ma munafukan Madina manya sun yi taro suka ce ya kamata a hana musu abinci domin su bar musu garinsu, saboda haka almajirai baki ne na Allah. Mutum ya haifi ’ya’yansa dole ya kai su suyi karatun addini, dole ya kai su su yi karatun duniya, dole ya bar wadansu su taimaka masa, in shi kansa ba zai iya bin ’ya’yansa da ya kai su makarantar nan ya kula da abincinsu da wajen kwanansu ba, kuma shi ma mutumin da aka kai masa almajirai ba ya da iko ya ciyar da ’ya’yansa ma balle ya ciyar da almajirai, sai aka bar abin a kan gayya na masu aikata aikin alheri. Su ba su abinci da daddare su ba su abinci duk lokacin da suke bukata, su kuwa su saurari lada wajen Allah. To amma Nasara shi da bai damu da Lahira ba ko abincinsa ya saura shi ba zai bai wa wani ba. Nasara in ya yi bako ba zai saukar da shi a gidansa ba sai ya saukar da shi a otel ya biya otel din, har da abinci amma ba dai ya saukar da shi a gidansa ya ci abinci a gidansa ba. To amma mu a wajenmu abin da ka rage ka bai wa almajiri ya ci ya fi wanda kai ka ci a cikinka balle wanda ka mutu ka bari aka gada. To almajiran Nasara suke da iko a duk duniya a yau, duk wanda ka gani da iko yau in ka bincika almajirin Nasara ne ko Nasaran Ingilishi ko na Faransa ko na Jamus ko Nasaran ko’ina. Su ke da mulki su ke da murya sai su daga murya, ka ga almajiran boko wadansu suna Amurka wadansu Ingila wadansu Jamus ba wanda ya ce komai sai dai wadanda ke zuwa tsakanin gari da gari a cikin kasa a ce ana yawo da almajirai. Akwai wata gwamnati da aka yi wani lokaci ba ka da iko ka shiga mota da allo sai a kama ka a ce kai dan Tatsine ne, sai da muka tashi tsaye muka ce duk wanda ya sake kiran mu masu karatun Alkura’ni da cewa mu ’yan Tatsine ne, to za mu yi kararsa. Shi Tatsine ko duk wani abu da ya zo na ta da hankali ra’ayi ne wanda aka watsa direbobi kuma suka dauka, kuma almajiran ma wadansu sun dauka suke yi.
Amma hana bara zalunci ne, almajiran ma ba za ka gan su sun je gidan Minista ko Gwamna ko Sakataren Gwamnati ko Shugaban karamar Hukuma suna bara ba, su wadanda ake bara a gidajensu ba su damu su yi kara ba, to me ya dame ka? Ka bari mana bawan Allah ya ci abinci a hannun bayin Allah!