Rikicin manoma da makiyaya a Binuwai: Sarkin Musulmi ya nemi a kafa hukumar bincike

Mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad ya bukaci Gwamnatin Jihar Binuwai ta kafa hukumar bincike don gano hakikanin abubuwan da suka haifar da rikici a tsakanin manoma Tibi da Fulani makiyaya.Sarkin Musulmin ya bayyana haka ne a ranar Talatar da ta gabata, lokacin da Aminiya ta tuntube shi kana bin da ke faruwa a […]

Rikicin manoma da makiyaya a Binuwai: Sarkin Musulmi ya nemi a kafa hukumar bincike

The supreme head of Muslim faithfuls in Nigeria and Sultan of Sokoto Mohammed Sa’ad Abubakar III speaks at the historic first Talakawa Summit in Nigeria in Dutse, Jigawa State on October 18, 2008. Top Jigawa State government officials in northern Nigeria led by Governor Sule Lamido and traditional rulers represented by the Sultan of Sokoto […]

Mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad ya bukaci Gwamnatin Jihar Binuwai ta kafa hukumar bincike don gano hakikanin abubuwan da suka haifar da rikici a tsakanin manoma Tibi da Fulani makiyaya.
Sarkin Musulmin ya bayyana haka ne a ranar Talatar da ta gabata, lokacin da Aminiya ta tuntube shi kana bin da ke faruwa a Jihar Binuwai da kuma yadda duk da sanya hannunsa ba a samu sakamakon a zo a gani ba.
Sarkin Musulmin, wanda ya dade na aiki tukuru don ganin an warware rikicin da ake yi a Jihar Binuwai, ya ce kafa wannan hukumar zai ba da dama ga bangarorin da ke rikicin su bayyana abubuwan da ke damunsu da kuma labarin abin da ya shafe su. Shi kuma Gwamna Gabriel Suswan sai ya yanke hukunci kan abin da ya dace ya yi don shawo kan matsalar.
Ya ce wani kwamitin da ke karkashin Sarkin Gombe wanda ya wakilce shi da kuma Tor Tibi da wasu fitattun shugabannin al’umma daga bangarorin ya ba da muhimman shawarwari kan yadda za a kawo karshen fadace-fadacen. An mika rahoton ga gwamnatocin jihohin Binuwai da Nasarawa wata uku da suka gabata, amma har yanzu bai sani ba ko an yi amfani da shawarwarin kwamaitin ya baya ba.
Sarkin Musulmin ya yi Allah wadai kan asarar rayuka da dukiyoyin da bangarorin masu rikicin suka yi, kuma ya nuna takaici kan yadda Fulani da Tibbi ke ta fada da juna, alhali sun dade suna zaune tare cikin lumana, har ma akwai wasan barkwanci da suke yi wa juna. Ya ce akwai bukatar lallai a gano dalilan da ke haifar da tashe-tashen hankulan na baya-bayan nan, bayan an samu zaman lafiya sakamakon tsoma bakin sarakuna.
Ya ce: “Duk labaran da kuke gani a jaridu suna nuna Fulani ne ke kai hari. Wannan ba shi ne hakikanin lamarin ba. Babu wanda ke bayyana irin satar shanun da ake yi a can. Tabbas manoma na darajanta amfanin gonarsu, tunda rayuwarsu ta dogara kacokan a kan abin da suke nomawa ne. Don haka za a samu maganin matsalar ne idan aka daina lalata amfanin gona, sannan aka daina satar shanu ko kashe su.”
Sarkin Musulmin ya soki lamirin rahotannin da ke nuna cewa rikici ne na addini, ya ce “Rikicin Binuwai ba shi da alaka da addini. Rikici ne na tattalin arziki kawai. Manoma za su fada da duk wanda ya lalata musu amfanin gona, ba tare da la’akari da addininsa ba, kamar yadda makiyaya za su yi fada da duk wanda ya kai wa shanunsu farmaki, ba tare da la’akari da addinin da yake bi ba. An sha yin rikicin manoma da makuiyaya a wasu jihohin, musamman wajen kokarin mamaye wuraren kiwo da mashayar ruwa, ba rikicin addini ba ne.”
Sarkin Musulmin ya ce: “Umartar Fulani su bar Jihar Binuwai ba zai warware matsalar ba. Domin babu wanda ya isa ya kori wani daga wani gari, tunda tsarin mulki ya ba kowane dan Najeriya damar zama a duk inda yake so, ya gudanar harkokin neman abincinsa. Idan muka fara korar juna daga wasu sassan Najeriya, to tamkar mun wargaza hadin kanmu ne da zaman lafiyarmu da tande-tanaden tsarin mulki. Idan wani sashi ya kaddamar da hare-haren daukar fansa, daya sashin ma haka zai sake kwatawa, sai a ce daukar fansa ce, ta yadda wutar rikici za ta yi ta ruruwa. Kamata ya yi a kafa hukumar bincike don ta gano dalilan da suka haifar da rikicin baya-bayan nan, ta yadda gwamnati za ta samu saukin shawo kan matsalar.”
Sarkin Musulmin, wanda ya ziyarci Jihar Binuwai har sau uku a wannan dan tsakani, don taimaka wa gwamnati wajen lalubo hanyar tabbatar da zaman lafiya, ya bukaci Gwamnatin Tarayya ta shigo cikin lamarin, ta yadda za ta taimaka wajen kawo karshen rikicin.