Rikicin manoma da makiyaya: Sau uku muna ganawa da Obasanjo – Bayari
Shugaban Kungiyar Ci Gaban Al’ummar Fulani ta Gan-Allah, Alhaji Sale Bayari ya ce sun zauna da tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo har sau uku bayan ya gayyace su kan matsalolin tsaro da halin da al’ummar Fulani suke ciki., inda ya ce bayan ganawar ce sai Obasanjo ya hada su da manyan sarakunan Yarbawa da wadansu […]
Alhaji Sale Bayari a tsakiya tare da wadansu shugabannin Kungiyar Gan Allah a Kudu maso Yamma
Shugaban Kungiyar Ci Gaban Al’ummar Fulani ta Gan-Allah, Alhaji Sale Bayari ya ce sun zauna da tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo har sau uku bayan ya gayyace su kan matsalolin tsaro da halin da al’ummar Fulani suke ciki., inda ya ce bayan ganawar ce sai Obasanjo ya hada su da manyan sarakunan Yarbawa da wadansu gwamnoni da ke Kudu maso Yamma domin tattauna yadda za a shawo kan wannan al’amari na rikicin manoma da makiyaya da kashe-kashe da fashi da makami da satar mutane ana garkuwa da su domin neman kudin fansa.
Alhaji Sale Bayari wanda yake tare da Sakataren Labarai na Kungiyar Yarbawa ta Afenifere Mista Yinka Odunmakin ya fadi haka ne a zantawarsa da Aminiya a Ibadan bayan da ya jagoranci ayarinsa zuwa fadar Alaafin na Oyo Oba Lamidi Adeyemi don kai masa ziyarar ban girma tare da tattaunawa kan lamarin tsaron kasa.
Ya ce Obasanjo ya gayyace shi a watan Yuni da ya gabata a inda ya yi masa tambayoyi da ya gamsu da amsoshin da ya ba shi ne, sai ya sake gayyatarsu a karo na biyu kuma suka yi ganawa ta 3 a ranar 3 ga Augusta inda shugabannin kungiyar daga jihohin Yamma da jihohin Kwara da Kogi suka halarta. “Hakan ne ya sa Obasanjo ya yanke shawarar hada mu da manyan sarakunan Yarbawa da suka hada da Alaafin na Oyo da Ooni na Ife da wasu gwamnoni muka gana da su a lokuta daban-daban kan yadda za a yi maganin matsalolin tsaro a kasa,” inji sh.
Shugaban ya ce “Ganawar da muka yi da wadannan shugabannin ta yi tasiri sosai domin daga lokacin da muka fara tattaunawar zuwa yanzu an samu saukin kalaman batanci a kan Fulani da ke fitowa daga bakin wadansu shugabannin Yarbawa da kungiyoyinsu ke yin barazanar korar Fulani daga yankin.”
Game da sakamakon ganawarsu da Alaafin na Oyo ya ce “Daya daga cikin muhimman abubuwan da Alaafin na Oyo Oba Lamidi Adeyemi ya tabbatar mana shi ne cewa bai goyi bayan korar fulani daga Kudu maso Yamma ba domin dukkanmu ’yan Najeriya ne da dokar kasa ta amince da zamanmu a ko’ina cikin kasa. Sai dai Sarkin ya nuna bacin rai a kan yawan fadace fadacen manoma da makiyaya da yawan samun Fulani a cikin miyagun ayyuka na satar mutane da garkuwa da su da fashi da makami inda ya ce ba zai taba zuba ido yana kallon haka na aukuwa a masarautarsa ba.”
A wajen taron da ya yi da ’yan jarida a Ibadan, Alhaji Sale Bayari cewa ya yi shekaru da yawa da suka wuce al’ummar Fulani suke zaune a wannan sashe kuma ana samun auratayya tsakaninsu da Yarbawa inda da yawa daga cikinsu ba sa jin harshen Fulatanci ko Hausa sai Yarbanci. Saboda haka ya yi kira ga dukkan jami’an tsaron kasar nan su ba da hadin kai ga Kungiyar Gan-Allah domin dakile miyagun ayyukan da ake zargin Fulani ko wasu abilu suna aikataw tare da kama masu aikatawa da tabbatar da an yi musu hukunci domin ya zama darasi ga masu shirin aikata irin haka a nan gaba.