Rikicin manoma da makiyaya ya ci rai 3 a Nasarawa

Aƙalla mutane uku ne suka rasu a wani sabon rikicin manoma da makiyaya a yankin Dogon Duste da ke Jihar Nasarawa

Rikicin manoma da makiyaya ya ci rai 3 a Nasarawa

Aƙalla mutane uku ne suka rasu a wani sabon rikicin manoma da makiyaya a yankin Dogon Duste da ke tsakanin ƙananan hukumomin Nasarawa da Toto a Jihar Nasarawa.

Kwamishinan ’yan sandan jihar, Umar Nadada ya ce tabbatar da aukuwar na ranar Litinin 18 ga watan Nuwamba da misalin ƙarfe 4:30 na yamma.

Jami’in ’yan sandan shiyya (DPO) ya ruwaito cewa, da isar su wurin, an gano gawarwakin mutum biyu a gonar, wasu hudu kuma sun jikkata.

An kai waɗanda suka jikkata zuwa cibiyar kula da lafiya a matakin farko domin yi musu magani.

A wani bincike da ’yan sandan suka gudanar, sun gano wata gawa a cikin daji, wanda ya kawo adadin waɗanda suka mutu zuwa uku.

Kwamishinan ya tabbatar da cewa an daidaita al’amura a yankin, kuma ’yan sanda na gudanar da cikakken bincike domin gano musabbabin rikicin.

Ya kuma jaddada mahimmancin haɗin kan al’umma wajen tabbatar da tsaro, sannan ya buƙaci mazauna yankin da su ba jami’an tsaro haɗin kai domin hana afkuwar irin haka a nan gaba.

Nadada ya bayyana irin kokarin da rundunar ’yan sandan ke yi na hada kai da al’umma domin kamo wadanda ke da hannu a rikicin da kuma tabbatar da sun fuskanci shari’a.

Ya jaddada cewa kare rayuka da dukiyoyi wani nauyi ne na haɗin gwiwa, ya kuma yi kira ga mazauna yankin da su baiwa ’yan sanda goyon baya wajen tunkarar ƙalubalen tsaro.