Rikicin manoma da makiyaya ya ci rayuka 2 a Neja 

An kashe mutane biyu a wani rikicin Fulani makiyaya da manoma kabilar Gbagyi a kauyen Kadna da ke Karamar Hukumar Shiroro ta Jihar Neja.

Rikicin manoma da makiyaya ya ci rayuka 2 a Neja 

Mutane biyu, makiyayi daya da wani manomi dan kabilar Gbagyi sun rasu a wani rikici da ya barke tsakanin wasu da ake zargin Fulani makiyaya ne da manoma kabilar Gbagyi a kauyen Kadna da ke Karamar Hukumar Shiroro ta Jihar Neja.

Majiyoyi sun shaida wa wakilinmu cewa, an kuma kona gidaje da dama da dabbobin gidaje da kayan abinci da sauransu na manoman Gbagyi a rikicin na ranar Alhamis.

Hakazalika manoma da dama a kauyen Kadna sun bar gidajensu zuwa Gwada da kauyukan da ke makwabtaka da su saboda fargabar ramuwar gayya daga makiyaya.

Wata majiya da ta nemi a sakaya sunanta ta ce rikicin ya fara ne da safiyar ranar Alhamis inda wani da ake zargin Fulani makiyayi ne ya kutsa cikin wata gona, lamarin da ya haddasa arangamar.

Wakilimu ya kasa samun kakakin ’yan sandan jihar Neja, SP Wasiu Abiodun, ta wayar tarho har zuwa lokacin hada wannan rahoto. Har yanzu kuma bai amsa sakon da aka aika a wayarsa ba.