Rikicin manoma da makiyaya ya jikkata mutum 12 a Kano

Manomi ya bugi saniyar da ta shiga gonarsa, sai mai ita ya rama ta hanyar dukan manomin. Daga nan ne rikici ya rincaɓe.

Rikicin manoma da makiyaya ya jikkata mutum 12 a Kano

Ana fargabar cewa aƙalla mutum 12 ne suka jikkata sakamakon wani rikici tsakanin manoma da makiyaya da ya auku a Ƙaramar Hukumar Warawa da ke Jihar Kano.

Lamarin ya faru ne a Gundumar Jigawa, inda ya rutsa da manoman ƙauyen Gadan Sarki da makiyaya daga ƙauyukan Majawa da Karade.

Wani mazaunin yankin, Malam Balarabe Ado, ya shaida cewa rikicin ya samo asali ne tsakanin mazauna ƙauyukan da abin ya shafa.

A cewarsa, rikicin ya fara ne bayan wata saniya ta shiga gonar wani manomi ta cinye amfanin gonarsa.

“Manomin ya bugi saniyar, lamarin da ya sa mai ita ya rama ta hanyar dukan manomin. Daga nan ne rikicin ya rikiɗe zuwa faɗa tsakanin ɓangarorin biyu, inda mutum 12 suka jikkata,” in ji shi.

Shi ma Shugaban Ƙaramar Hukumar Warawa, Alhaji Lamido Sunusi Ahmad, ya tabbatar da faruwar lamarin a cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai, Musleem Garindau, ya fitar.

Sanarwar ta ce shugaban ƙaramar hukumar ya ziyarci waɗanda suka jikkata a Babban Asibitin Wudil, inda ya bayar da umarnin gwamnati ta ɗauki nauyin duk kuɗaɗen jinyarsu har sai sun warke.

Ya yaba wa shugabannin al’umma da jami’an tsaro bisa gaggawar da suka yi wajen shawo kan rikicin tare da dawo da zaman lafiya a yankin.

Haka kuma, ya buƙaci al’umma su guji yaɗa jita-jita ko aikata duk wani abu da zai iya ƙara tayar da hankali, yana mai jaddada muhimmancin tattaunawa da sulhu domin tabbatar da zaman lafiya mai ɗorewa.

Ya kuma yi kira ga mazauna yankin da su rungumi zaman lafiya tare da amfani da hanyoyin sasanci domin kauce wa sake faruwar irin wannan rikici.

Da aka tuntuɓi kakakin Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kano, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce har zuwa lokacin ba su samu rahoton faruwar rikicin ba. Sai dai ya ce zai bincika domin tabbatar da abin da ya faru a yankin.