Rikicin Manoma: Karamar Hukumar Kwami Ta kafa Kwamitin Tsaro

An gargadi bangarorin kan shiga hakki ko yi wa juna barna

Rikicin Manoma: Karamar Hukumar Kwami Ta kafa Kwamitin Tsaro

A kokarinsa na kauce wa rikicin manoma da makiyaya da ke yawan faruwa a lokacin damuna, Shugaban Karamar Hukumar Kwami a Jihar Gombe, Dakta Ahmed Wali Doho, ya kafa kwamitin tsaro da sanya ido kan bangarorin.

Da yake zantawa da manema labarai a ofishinsa da ke garin Malam Sidi, shugaban karamar hukumar, ya bukaci manoma da su guji noma burtalolin shanu, wanda hakan ke haifar da rikici tsakaninsu da makiyaya, da ke haifar da asarar rayuka.

Su ma makiyayan ya gargade su da cewa su guji shiga gonakin manoma, saboda hakan ne ke jawo rikici idan suka cinye musu amfanin gona.

A cewarsa, lokacin girbi me aka fi samun rikicin manoma da makiyayan, saboda haka kwamitin zai ci gaba da sa ido daga yanzu har zuwa lokacin girbin don ganin ba a samu rikici ba.

Ya kara da cewa, kusancin garin Kwami da rafi ya sa ya zama wuri mai kyau don noman rani.

Don haka ya ja hankalin manoman yankin da su yi amfani da wannan damar wajen bunkasa tattalin arzikinsu.

Ya jaddada cewa noman rani na da matukar muhimmanci wajen magance matsalar karancin abinci a Najeriya.

Hakan ne ya sa suka hada kan matasan yankin don su fara noman rogo da zai taimaka wajen shawo kan matsalar karancin abinci da rage wa manoma tsadar takin zamani.