Rikicin Masar: Abin da ya ci Doma bai barin Awai
Babu makawa dorewar kataniyar da yanzu haka ke wakana a kasar Masar ba za ta haifar wa nahiyar Afirka da ta Jaziratul-Al-Arabiya da mai ido ba, kuma wajibi ne al’ummomin kasar Masar su gaggauta sasanta dukkan bambance-bambancen da ke tsakaninsu. Ta ko ina aka lura da abin da ya faru a wannan kasa za a […]
Babu makawa dorewar kataniyar da yanzu haka ke wakana a kasar Masar ba za ta haifar wa nahiyar Afirka da ta Jaziratul-Al-Arabiya da mai ido ba, kuma wajibi ne al’ummomin kasar Masar su gaggauta sasanta dukkan bambance-bambancen da ke tsakaninsu. Ta ko ina aka lura da abin da ya faru a wannan kasa za a fahimci cewa Musulmi ne dai ba a son su kafa gwamnati, daidai da yadda aka dakile yunkurin kafa sabuwar gwamnatin Musulunci a kasar Aljeriya a ‘yan shekarun baya.
Babban abin da ya tabbatar da haka shi ne yadda sojojin kasar Masar, wadanda Amurka ta daure wa gindi don dakushe dukkan wata barazana da za ta samo asali daga kasar don cutar da kasar Isra’ila, suka bi shugabanni da ‘yan kungiyar Muslim Brotherhood suka kakkame, suka kuma takura masu don hana su yin zanga-zangar nuna kin amincewarsu da yadda aka kifar da gwamnatin da suka kafa cikin dan kankanen lokaci, bayan sun yi shekaru hamsin suna gwagwarmayar kaiwa ga wannan matsayin.
Sojojin da tun farko aka yi amfani da su don dakile nasarar da ake gani tsohon Shugaban kasar Masar, Mohammad Morsi zai samu, sun aikata abin da iyayen gidansu na Yammacin Turai da Isra’ila ke so, watau kawar da gwamnatin Musulunci da kuma jingine kundin tsarin mulkin kasar, suka kuma hambarar da majalisar dokokin kasar wacce ‘yan kungiyar Muslim Brotherhood ke da gagarumin rinjaye a ciki.
A yanzu sababbin shugabannin kasar, tare da hadin kan sojoji sun yi alkawarin gudanar da sabon zabe cikin dan kankanen lokaci, sun kuma nada abokin hamayyar tsohon shugaba Morsi a takarar shugabancin kasar a bara, wato Mohammed El-Baradai, wani fitaccen dan morin Amirka a matsayin Firayim Ministar kasar, sa’anan kuma za su sake tsara sabon kundin tsarin mulki. Masu lura da al’amuran yau da kullum na hasashen cewa hakan zai share fagen kafuwar sabuwar gwamnatin da za a dankawa El-Baradai don ya ji dadin dora kasar Masar bisa turbar da Yahudu da Nasara ke so don dacewa da manufofinsu na kare kasar Isra’ila daga ramuwar gayyar ketar da take yi wa Larabawa da kuma dakushe hasken addinin Musulunci a duniya. Idan kuma an tashi sake tsara sabon kundi za a karkade dukkan burbudin ra’ayi ko manufofin kungiyar Muslim Brotherhood daga cikinsa, a kuma haramtawa dukkan kungiyoyin da ake da alaka da addini, ciki har da Muslin Brotherhood, shiga cikin harkokinsiyasar kasar nan gaba.
Da yake nufinsu na danka wa ElBaradai bai ci nasara ba, sai suka sake wani kwararren ma’aikacin gwamanti, Hazem el-Biblawi. Shi kuwa ya himmatu wajen kafa gwamanti da kokarin shawo kan jam’iyyun kasar su amince da shi. Shi nma dai wannan an bai wa al’umma a dunkunkune.
Wannan al’amari ya yi daidai da manufar Yahudawa na tsara wata sabuwar akida ta mulkan duniya da suke kira New World Order, wacce za a gina ta don tabbatar da kafuwar gwamnati guda a duniya, mai tsarin tattalin arziki bai daya da kuma halayyar zamantakewa wacce ba ruwanta da addini ko bautar Ubangiji (SWT), sai yi wa Dujal hidima. Shi ya sa a yanzu a kasashen Musulmi zalla da kuma dukkan wuraren da Musulmi suka yi katutu ake ta samun tashe-tashen hankula, babu zaman lafiya sai zubar da jini da dauki-ba-dadi walau bisa al’amuran da suka jibanci kabilanci ko rarrabuwan kawunan Musulmi, wanda Yahudu da Nasara suka dade da yin amfani da su don hana Larabawa da sauran Musukmin duniya zaman lumana da kwanciyar hankali.
Tuni kasashen nahiyar Arewacin Ifrikiyya suka shiga tasku, ba domin komai ba sai don addinin Musuluncin da suka runguma hannu bibbiyu, da kuma kokarin da Yahudu da Nasara ke yi na ganin sun farraka kawunan al’ummomin nahiyar don su ji dadin ci gaba da karkata akalarsu inda suke bukata. Haka nan kuma a nahiyar Yammacin Ifrikiyya, kasashe kaman su Nijar da Najeriya da Mali sun fada cikin tarkon Yahudu, sun kuma rasa ‘yanci da mutuncinsu, sun kama hanyar yin ban-kwana da addininsu. A wadannan kasashe Yahudu da Nasara sun yi amfani addini don haddasa yamutsi da kata-kata, hakan kuma ya rarraba kawunan mabiya daban-daban don a ji dadin mamaye su, a tatsi arzikinsu da karfi da yaji. A sakamakon haka babu hadin kai ysakanin al’ummomin don tunkarar bala’o’in da Turawa ke haifarwa, ko kuma dagewa don magance illolin da suke haddasawa don amfaninsu, bayan sun cutar da jama’a.
A nahiyar Gabas ta Tsakiya kuwa, inda manyan addinan duniya guda biyu suka samo asali, babu wata kasa mai zaman lafiya da lumana sai Isra’ila. kasashe kaman su Masar da Palasdinu da Lebanon da Syria da kuma Turkiya duk sun gamu da sharrin makwabciyarsu Isra’ila, bala’o’i da masifu sun sassauko masu, kuma nunkufurcin Turawa da munakisar Yahudawa na neman kai su kasa. Sun kasa gane cewa an yi amfani da bambance-bambancen manufofin addinsu na Islama don nesanta su da juna ta yadda ba za su iya hada kawunansu don yakar ta ba. A takaice dai Yahudawa, tare da taimakon Nasara, sun fatattaka Larabawan gabashin Bahar Rum, sun kuma yi taushi tamkar atafa, ba wata a cikinsu mai tabukawa don ramuwar gayya.
Yanzu tun da an kai Masar kasa, a matsayinta na babba a cikin kasashen Larabawa mai mutane fiye da miliyan casa’in, to wacce ce kuma za ta iya kokartawa, har ta karyawa Yahudu da Nasara tsinken tsire a ido? kasashen Tsibirin Arabiya, kaman su katar da Oman da Bahrain da Omman da Kuwait da Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) duk sun zame ‘yan koren Yahudu –kamar babbar yayarsu, Saudi Arabia — wadanda Nasara ke karkata akalarsu ga nuna kiyayya ga addinin Islama da kuma kyayawan dabi’unsu na Larabawa. Abin takaici game da haka ma shi ne wai kasar Saudiya ce ta fara aikewa da sakon taya murna ga gwamnatin zalunci da sojoji ‘yan barandar Amerika suka kafa a Masar. Kai! Allah wadan naka ya lalace, wai rakumin dawa ya ga na gida. To idan ba su yi hankali ba sai abin da ya samu Masar ya ishe su, domin kuwa abin da ya ci Doma bai barin Awai.