Rikicin Masarauta: Kotu ta yi watsi da ƙarar Aminu Bayero

Kotun ta ce an kori shari’ar da mai ƙara Aminu Ado Bayero ya gabatar saboda rashin cancanta.

Rikicin Masarauta: Kotu ta yi watsi da ƙarar Aminu Bayero

Dubban magoya bayan Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II sun fito sun yi dandazo suna murna da hukuncin da kotu ta yanke kan rikicin masarautar Kano.

An samu rahoton cewa kotun ɗaukaka ƙara da ke Abuja ta yi watsi da ƙarar Mai martaba Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero da ya shigar kan Sarkin Kano na 16, Malam Muhammadu Sanusi II, bisa rashin cancantarsa.

Kotun ta ce an kori shari’ar da mai ƙara na 1, Aminu Ado Bayero ya gabatar saboda rashin cancanta.

Kotun ɗaukaka ƙara ta yanke hukuncin cewa babbar kotun tarayya ba ta da wani hurumin kutsawa cikin lamarin da ya shafi dokar masarautar Kano.

Yayin da Sarkin ya fito a fadar Gidan Rumfa a ranar Juma’a, ya samu gagarumar tarba daga ɗimbin magoya bayansa suna rera waƙoƙin yabo da jinjina ga nasarar.