Rikicin masarautar Ibadan: An maka Gwamnan Oyo da Olubadan a gaban kotu

Ana dai zarginsu ne da kokarin lalata sarautar Jihar

Rikicin masarautar Ibadan: An maka Gwamnan Oyo da Olubadan a gaban kotu

Gwamnan Oyo da Olubadan na Ibadan

Tsohon Gwamnan Jihar Oyo, kuma mai rike da sarauta a masarautar Ibadan, Sanata Rashidi Ladoja, ya maka Gwamnan Jihar, Seyi Makinde da Olubadan na Ibadan, Oba Lekan Balogun, a gaban babbar kotun Jihar Oyo da ke Ibadan.

Ladoja dai ya maka mutanen ne a kotu bisa zarginsu da yunkurin lalata sarauta da al’adar gargajiya a msarautar Ibadan mai dimbin tarihi.

Tsohon Gwamnan wanda ke rike da sarautar Otun (na hannun dama) kuma jiran gadon sarautar Olubadan dai na kalubalantar matakin Gwamna Makinde na daga darajar wasu Hakimai guda 10 zuwa Sarakuna a masarautar.

A ranar Juma’ar da ta gabata ce dai aka gudanar da bikin bayar da sandar mulki ga sabbin sarakunan su 10, wanda shi Ladojan yake cikinsu, amma ya ki halarta.

A cikin karar, tsohon Gwamnan ya ce ya gano wani shiri da Olubadan, yake yi na hana shi ci gaba da yin amfani da matsayinsa na Otun a masarautar da kokarin hana shi hayewa sarauta idan lokacinsa ya yi, saboda kin karbar sandar sarauta da aka mika wa sauran Hakiman su 10.

Ladoja ya ce shi ma a kafafen yada labarai ya ji labarin cewa za a mika masa sandar sarauta a ranar Juma’a 07/07/2023, alhali shi bai taba amincewa da sabon tsarin daukaka darajar Hakiman masu rike da manyan ba, inda ya ce hakan ya saba wa dokar al’adun gargajiya.

Binciken Aminiya ya gano cewa wannan takaddama ta faro ne a shekarar 2019 a lokacin da marigayi tsohon Gwamnan Jihar Oyo, Sanata Abiola Ajimobi na jam’iyyar APC da ke rike da ragamar mulki a wancan zamani ya daukaka darajar manyan masu rike da sarautu zuwa Sarakuna a masarautar Ibadan.

Sai dai a lokacin da Gwamna Seyi Makinde ya kama ragamar mulki a inuwar jam’iyyar PDP bai yi wata-wata ba wajen daukar matakin mayar da su matsayinsu na manyan Hakimai masu rike da sarautu a masarautar.

Wannan ya haifar da yawan ce-ce-ku-ce da yawan korafi da wasu masu fada aji da masana ’yan boko da lauyoyi suka rinka yi sukar lamirin Gwamna Seyi Makinde kan matakin.