Rikicin Masarautar Ibadan ya dauki sabon salo

Shugabannin zuriyar fitattun gidajen sarauta (Mogajis) a masarautar Ibadan sun nemi sababbin sarakuna 21 da Gwamnatin Jihar Oyo ta daukaka matsayinsu daga hakimai zuwa sarakuna da su bi umarnin Babbar Kotun Jihar, su daina kiran kansu sarakuna idan ba fitina suke neman tsokanowa ba. Sun ce tunda Babbar Kotun Jihar Oyo ta yanke hukuncin rashin […]

Rikicin Masarautar Ibadan ya dauki sabon salo

Shugabannin zuriyar fitattun gidajen sarauta (Mogajis) a masarautar Ibadan sun nemi sababbin sarakuna 21 da Gwamnatin Jihar Oyo ta daukaka matsayinsu daga hakimai zuwa sarakuna da su bi umarnin Babbar Kotun Jihar, su daina kiran kansu sarakuna idan ba fitina suke neman tsokanowa ba.

Sun ce tunda Babbar Kotun Jihar Oyo ta yanke hukuncin rashin amincewa da daukaka matsayinsu, to kamata ya yi a yanzu su daina sanya hular sarauta da rike sandar sarauta a hannayensu har zuwa lokacin da Kotun daukaka kara za ta yanke nata hukuncin a kan wannan al’amari.

“Muna kira ga Gwamna Abiola Ajimobi ya tsawata wa sababbin sarakunan su daina aikata abin da zai iya jefa Jihar Oyo cikin hargitsi ta fannin bijirewa umarnin kotu da suke yi da taka doka da oda, wanda ba mu bukatar su tura mutanenmu ga bango da zai kai ga yanke wa kansu hukunci,” inji shugabanni, a wajen wani taron gaggawa da suka yi a fadar Olubadan a ranar Juma’ar da ta gabata.

Mukamin Mogaji wato shugaban fitacciyar zuriya a masarautar Ibadan shi ne matakala ta farko da ake takawa wajen rike mukaman sarautu daban-daban har zuwa matakala ta karshe wato matsayin Olubadan.

Mai magana da yawun shugabannin zuriyar, Cif Wale Oladoja ya shaida wa ’yan jarida cewa, bayanin da sababbin sarakunan suka yi, cewa babu wanda ya isa ya hana su sanya hular sarauta bayani ne na raina kotu. Sun ce bai kamata su rika fakewa a karkashin lemar Gwamnan Jihar Oyo domin kokarin tura jama’a ga bango ba.

Tun da farko sai da sarakunan 21 suka yi taro da ’yan jarida a ranar Alhamis ta makon jiya, inda suka zargi tsohon Gwamnan Jihar Oyo Sanata Rasheed Ladoja cewa shi ne yake ruruta wutar fitina a kan wannan al’amari. Sun ce shi ne wanda yake rike da babbar sarauta ta Osi Olubadan, ba ya goyon bayan duk wani abin alheri da ci gaba da Gwamna Abiola Ajimobi yake yi saboda gabar siyasa da ke tsakaninsu.

Idan ba a manta ba takaddama tsakanin Gwamna Abiola Ajimobi da Olubadan na Ibadan Oba Saliu Adetunji ta faro ne a bara a lokacin da Gwamnan ya amince da daukaka darajar wasu hakimai zuwa sarakuna a masarautar Ibadan, wanda Olubadan ya ki amincewa da hakan.

Sababbin sarakunan 21 sun yi yunkurin tube Olubadan daga karaga a wancan lokaci, wanda hakan ya haifar da zafafan kalamai tsakanin bangarorin biyu a kan wannan al’amari da ya ki ci ya ki cinyewa.