Rikicin Masarautar Kano: Tsagin Aminu Ado Bayero zai ɗaukaka ƙara
Tsagin Sarkin ya ce zai jira sai kotun ƙoli ta yi hukunci sannan zai haƙura.
Tsagin Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero, ya bayyana cewa za su ɗaukaka ƙara zuwa kotun ƙoli game da hukuncin da kotun ɗaukaka ƙara ta yanke kan batun soke masarautun Kano.
A ranar Juma’a, kotun ɗaukaka ƙara ta bayyana cewa babbar kotun tarayya ba ta da hurumin sauraron ƙarar da ta shafi soke masarautun jihar, wanda ta haifar da ruɗani.
Wannan hukuncin ya jingine hukuncin da babbar kotun tarayya ta yanke a baya, wanda ya dakatar da gwamnatin Kano daga soke masarautun.
A yayin taron manema labarai da aka gudanar ranar Asabar, Aminu Babba Dangundi, wanda ya shigar da ƙarar a madadin masarautun da aka rushe, inda ya ce ba za su karɓi hukuncin ba tare da ƙalubalantarsa a kotun ƙoli ba.
Ya ce, “Gwamnatin Kano da majalisar dokoki ba su bi ƙa’ida ba wajen soke masarautun ba.
“Bai kamata a cire sarki ba tare da ba shi damar kare kansa daga zarge-zargen da ake masa ba.”
Dangundi ya ƙara da cewa sun riga sun nemi takardun hukuncin kotun ɗaukaka ƙara domin sauƙaƙa ƙarar zuwa kotun ƙoli a ranar Litinin.
A gefe guda, gwamnatin Kano ta nemi tsagin Aminu Ado Bayero su yi biyayya ga hukuncin kotun ɗaukaka ƙara.
Sai dai Dangundi, ya ce har sai kotun ƙoli ta yanke hukunci ne kawai za a samu mafita ta ƙarshe.
“Idan aka ɗaukaka ƙara, doka ta tanadi cewa komai ya tsaya yadda yake kafin a kammala shari’ar a kotun ƙoli. Ita kotun ƙoli ce ƙarshen mataki a shari’ar,” in ji shi.
Wannan rikicin dai ya samo asali ne tun daga 2019 lokacin da gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje, ta kafa sabbin masarautu huɗu, lamarin da ya tayar da ƙura a harkokin masarautar jihar.
Yanzu haka, idanu sun koma kan matakin da kotun ƙoli za ta ɗauka game da wannan rikici mai cike da tarihi.