Rikicin matasa: An tsaurara tsaro a Jos jihar Filato
Rahotanni na bayyana cewa, an samu wani rikici da ya barke a yankin Dutse Uku, gadar Cele Bridge da unguwar Rikkos a karamar hukumar Jos ta Arewa da ke jihar Filato. Majiyarmu ta samu rahoton cewa, wasu matasan yankin sun yi ta kone gidajen jama’a, ya zuwa yanzu ba a tabbatar da dalilin wannan rikicin […]
Rahotanni na bayyana cewa, an samu wani rikici da ya barke a yankin Dutse Uku, gadar Cele Bridge da unguwar Rikkos a karamar hukumar Jos ta Arewa da ke jihar Filato.
Majiyarmu ta samu rahoton cewa, wasu matasan yankin sun yi ta kone gidajen jama’a, ya zuwa yanzu ba a tabbatar da dalilin wannan rikicin ba. Sai dai an samu rahoton ganin gawar wani matashi a Anguwan Damisa da ke Dutse Uku.
Wani mazaunin unguwar ya shaidawa majiyarmu cewa, a yau an girke jami’an tsaro yankin.