Rikicin Mil 12: Mutane uku suka mutu a kiri – kiri

Ya zuwa yanzu, an samu rahoton mutuwar mutum uku, cikin fiye da mutane 300 da Gwamnatin Legas ta kame a rikicin da ya gudana a kwanakin baya a unguwar Mil 12 da ke Legas. Kuma mafiya yawan mutanen da aka kame ’yan Arewa ne da ke gudanar da harkokinsu a kasuwar ta Mil 12, kana […]

Rikicin Mil 12: Mutane uku suka mutu a kiri – kiri
Rikicin Mil 12: Mutane uku suka mutu a kiri – kiri

Ya zuwa yanzu, an samu rahoton mutuwar mutum uku, cikin fiye da mutane 300 da Gwamnatin Legas ta kame a rikicin da ya gudana a kwanakin baya a unguwar Mil 12 da ke Legas. Kuma mafiya yawan mutanen da aka kame ’yan Arewa ne da ke gudanar da harkokinsu a kasuwar ta Mil 12, kana yawancinsu yara ne da matasa ’yan shekara 15 zuwa 30.
A cewar daya daga cikin shugabannin kasuwar Mil 12, Alhaji Dauda Tarai, kashi 85 na mutanen da aka kama yara kanana ne marasa galihu da ke kwadago a cikin kasuwar, wadanda jami’an tsaron suka je har cikin kasuwar ne suka kame su, alhali rikicin bai shafi kasuwar ba. “A lokacin da ’yan sandan suka zo kamen, akwai mutumin da ya so ya gudu, hakan ne ya sanya ’yan sandan suka harbe shi a ka kuma nan take ya mutu, suka tafi da gawar, ba kuma su ba ’yan uwansa sun yi mata sutura ba. Haka zalika, akwai wani Ba’are dan Jihar Kebbi da yake sana’ar yankan farce, wanda ya mutu a gidan kason, kimanin makwanni biyu ke nan, shi ma ba su ba da gawarsa an yi mata sutura ba kuma babu wani dan uwansa da aka sani a kasuwar.  Baya ga haka, akwai mutanen da su ma suka sami labarin dan uwansu ya mutu a kurkukun, su ma haka suka yi ta bibiya domin a ba su gawarsa su yi mata sutura. Haka aka yi ta wahalar da su, suka gaji da bibiya suka hakura.” Inji shi.
Ya kuma koka da tsauraran matakan beli da aka sanya, baya ga makudan kudi, abin da ya ce mafi yawan wadanda aka kame masu karamin karfi ne, da ba za su iya cika wadannan matakan ba.
Hajiya Halima, wacce kamen ya rutsa da dan uwanta mai suna Umaru, ta shaida wa Aminiya cewa sai da suka kashe sama da Naira dubu 150 kafin su sami belinsa a makon jiya kuma a halin yanzu yana nan kwance a asibiti ciki mawuyacin hali, sakamakon irin halin da ya samu kansa a kurkukun kiri-kiri na kuncin rayuwa da yunwa da kazanta. Domin a cewarta, wasu irin kuraje ne ke fesowa a jikin mutanen da aka tsare a wurin. “Akwai wani Bagobiri dan Nijar da shi ma ’yan uwasa suka yi belinsa bayan sun mayar da shi gida da kwana biyu shi ma ya mutu sakamakon irin bakar wahalar da ya sha. Babbar matsalar ita ce, daruruwan mutanen da ba su da gata, wadanda ba su san lokacin da za su fito daga irin wannan kangin ba.”  Inji ta.
A wata hira da dan Majalisar Tarayya daga Jihar Jigawa, Alhaji Muhammadu Sani Zoro ya yi a Radiyon Faransa, ya shaida cewa ya je Legas ne domin bibiyar hakkin mutanen da aka kame da kuma tattaunawa a kan yadda za a sako su, kasancewar akwai mutum 19 daga mazabunsa. Ya koka da yadda aka garkame su a gidan kasso na kiri-kiri tun ranar 3 ga watan Maris kuma a ce sai ranar 27 da 28 ga watan Mayu za a yi musu shari’a. “Mutum 306 ’yan Arewa aka kame. Tun a wancan lokacin na yi kokarin zantawa da Gwamnan Legas a kan wannan lamarin amma hakan bai yiwu ba. Don haka na taho na samu alkalan domin mu tattauna, a sassauta matakan belin.”
Ya kara da cewa, akwai jerin sunayen wadanda aka kame kuma duk wani gwamna da yake so ya yi bibiyar ’yan jihohinsa,  zai iya tuntubarsa.