Rikicin Ojo-Oba bai shafi Hausawa ba – Sakatare Yakubu

Sakataren Kungiyar al’ummar Hausawa Mazauna Oja-Oba a Ibadan, Malam Yakubu Masoyi ya ce rikicin kwanan baya da aka yi kone-konen gidaje da kadarori a wasu unguwanni da ke kusa da su bai shafe su ba. Ya ce “Maimakon haka ma mun hanzarta daukar matakin yekuwar sanar da mutanenmu masu yawon tallar kaya a kan hanyoyi […]

Rikicin Ojo-Oba bai shafi Hausawa ba – Sakatare Yakubu
Rikicin Ojo-Oba bai shafi Hausawa ba – Sakatare Yakubu

Sakataren Kungiyar al’ummar Hausawa Mazauna Oja-Oba a Ibadan, Malam Yakubu Masoyi ya ce rikicin kwanan baya da aka yi kone-konen gidaje da kadarori a wasu unguwanni da ke kusa da su bai shafe su ba.

Ya ce “Maimakon haka ma mun hanzarta daukar matakin yekuwar sanar da mutanenmu masu yawon tallar kaya a kan hanyoyi su kaurace wa shiga unguwannin da rikicin ya rutsa da su.”

Ya fadi haka ne cikin zantawa da Aminiya, jim kadan bayan kammala taron da shugabannin al’ummar Hausawan Oja-Oba suka saba yi da jama’arsu a kowane mako, inda suke tattauna al’amuran da suka shafi zamantakewarsu da jama’ar gari. Ya ce, “Tun cikin dare da aka fara rikicin muka dauki matakin aikewa da sakonni ta wayar salula ga mutanenmu da kada su kuskura su shiga yawon talla a wadancan unguwanni har sai bayan rikicin ya lafa.”

“Dangane da zamantakewarmu da jama’ar gari kuwa muna godiya ga Allah muna zaune lafiya tare da su. Matsalar kawai da muke fuskanta ita ce rashin jin harshen juna a tsakanin al’ummar Yarabawa da mutanenmu masu yawon tallar kaya a cikin gari, inda a wasu lokuta ake samun wadansu batagari suna yin amfani da wannan dama wajen musguna wa mutanenmu. Sau da yawa idan irin haka ta auku, muna hanzarta kai rahoto ga jami’an tsaro domin maganin matsalar,” inji shi.

Sakataren Al’ummar Hausawan wanda shi ne Shugaban Kasuwar Tsofaffin Kaya ta Oja-Oba, ya ce, “Domin kauce wa barkewar rikici ne ya sa muke kira ga mutanenmu masu yawon talla da masu tura baro da leburori su girmama dokokin kasa tare da bin umarnin shugabannin gari (Yarbawa) wadanda a wasu lokuta suke gudanar da bukukuwan al’ada da ke hana shiga da fita wasu unguwanni.”

“Ba mu ce mutanenmu su shiga cikin bukukuwan al’ada da jama’ar gari ke yi ba, amma wajibi ne mu girmama irin dokokin da suke shimfidawa da ba sa so wani ya taka. Shi ya sa muke tunatar da mutanenmu a kowane lokaci, su girmama irin wadannan dokoki domin kyautata zamantakewa da zama lafiya tsakaninmu da su,” inji shi.