Rikicin Ombatse a Nasarawa: An takaita hawa babura a kananan hukumomi bakwai
Gwamnatin Jihar Nasarawa ta haramta zirga-zirgar babura daga karfe 7:00 na yamma zuwa karfe 6:00 na safe a wasu garuruwa da kananan hukumomi bakwai na jihar da rikicin kabilanci ya ki ci, ya ki cinyewa. Gwamnan Jihar Umaru Tanko Al-Makura ne ya sanar da haka a wani jawabi da ya yi ga al’ummar jihar ta […]

Gwamnatin Jihar Nasarawa ta haramta zirga-zirgar babura daga karfe 7:00 na yamma zuwa karfe 6:00 na safe a wasu garuruwa da kananan hukumomi bakwai na jihar da rikicin kabilanci ya ki ci, ya ki cinyewa.
Gwamnan Jihar Umaru Tanko Al-Makura ne ya sanar da haka a wani jawabi da ya yi ga al’ummar jihar ta kafofin watsa labarai, da dare a ranar Juma’ar da ta gabata.
Gwamna Al-Makura ya ce garuruwan da aka hana zirga-zirga da babura sun hada da garin Awe da Doma da Keana da Lafiya da Akwanga da Obi da Nasarawa Eggon. Kuma ya yi kira kan a samu fahimtar juna a tsakanin al’ummomin jihar inda ya bayyana cewa ba an dauki matakin don cin zarafin kowa ba.
A cewarsa gwamnati ta yi haka ne don ta kawo karshen tashin-tashina a wadannan garuruwa da jihar baki daya. Ya yi kira ga jami’an tsaro su tabbatar cewa dokar da aka kafa tana aiki yadda ya kamata. Gwamnan ya kara da cewa ya zame masa wajibi ya yi wa al’ummar jihar jawabi dangane da abin da ke faruwa a wasu sassan jihar musamman na kwana kwanan nan inda a cewarsa ya kai ziyarar gani da ido zuwa wuraran da rikicin ya shafa kuma nan ba da jimawa ba gwamnati za ta tallafa wa wadanda suka yi asara.
Idan ba a manta ba a ’yan kwanakin nan ne rikicin kabilanci ya sake aukuwa a tsakanin ’yan kungiyar Ombatse da mutanen Alago a garuruwan Obi da Assakio inda aka sake kashe mutane aka kuma kone gidaje da dama.
A makon jiya ma ’yan kungiyar Ombatse sama da 200 sun kai wa sojoji da ke binciken ababen hawa a hanyar Akwanga zuwa Keffi hari, inda sojojin suka kame wasu ’yan kungiyar Ombatse da dama ciki har da wani dan sandan kwantar da tarzoma mai suna Kofor Ekipi Male da ke aiki da Hedkwatar Mopol ta 45 da ke Abuja, wanda ake zargin ya jagoranci ’yan Ombatse da suka kai musu harin tare da raunana wasu daga cikinsu.