Rikicin Pakistan: An kama kusoshin jam’iyyar Imran Khan

Gwamnati ta tura sojoji don murkushe tarzomar da ta barke sakamakon kama Khan kwanaki uku da suka gabata

Rikicin Pakistan: An kama kusoshin jam’iyyar Imran Khan

Gwamnatin Pakistan sun kama wani babban jigo na jam’iyyar tsohon Firayim Minista Imran Khan a ranar Alhamis, a yayin da gwamnati ta tura sojoji don murkushe tarzomar da ta barke sakamakon kama Khan kwanaki uku da suka gabata.

A cikin dare ne dai jami’an tsaron suka kama Shah Mahmood Qureshi, wanda ya kasance Ministan Harkokin Waje na shekara hudu a lokacin da Imran Khan ke firayim minista.

An kuma kama wasu manyan jiga-jigai biyu na jam’iyyar PTI ta Mista Khan —  Asad Umar da Fawad Chaudhry a ranar Laraba.

Kawo yanzu an kashe akalla mutum biyar bayan da tarzomar da ta biyo bayan kama Mista Khan da hukumar yaki da rashawa ta kasar ta yi a ranar Talata ta kara munana.

Wannan na faruwa ne a daidai lokacin da Pakistan ke a kasar mai mutane miliyan 220 ke fama da matsananciyar matsalar tattalin arziki da kuma jinkirin samun dauki daga Asusun ba da Lamuni na Duniya (IMF) tun watan Nuwamba.

Masu zanga-zangar sun kutsa kai cikin gine-ginen sojoji tare da kai farmaki gidan wani babban hafsan soji a birnin Lahore da ke gabashin kasar; sun kuma kai hari tare da kona wasu gine-gine da kadarorin gwamnati.

A ranar Laraba gwamnatin kasar ta amince da bukatar gwamnatin birnin Islamadan da kuma biyu daga cikin larduna hudu na kasar — Punjab da Khyber Pakhtunkhwa, wadanda kowacce daga cikinsu tungar Khan ce, — na tura sojoji domin dawo da zaman lafiya.

Rundunar ’yan sandan Islamabad ta fada a safiyar ranar Alhamis cewa sojoji sun isa babban birnin kasar.

’Yan sanda dai sun kama masu zanga-zanga sama da 1,300 a lardin Khan na Punjab saboda tashin hankali.

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno

DAGA LARABA: Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya